This site offers you with different novels series from one writer, I hope this will educate and as well as entertain you..

ALHAKI NEH! (Page 5)

🌸🦋🌸🦋🌸🦋🌸🦋🌸

*ALHAKI NEH!*

🌸🦋🌸🦋🌸🦋🌸🦋🌸🦋

® *_REAL PURE MOMENT OF LIFE WRITERS_*

_ɯɛ ɖơŋ'ŧ ơŋٳყ ɛŋŧɛřŧąıŋ ŋɖ ɛɖųĆąŧɛ, ცųŧ ɯɛ ąٳŞơ ŧơųĆɧ ŧɧɛ ɧɛąřŧ ơʄ řɛąɖɛřŞ_

By the applomb writer: *Hamagee*

Jan,2018

# WWW.PMLWRITERS@GMAIL.COM
# IG PML WRITERS
# https://www.facebook.com/PML_-Writers-FANS-459256761123035
# http://maryamsbello.blogspot.com

Wattpad @Hama_gee

Ina me k'ara bawa masoya da ma'abota karanta littattafai na a duk inda kuke hak'uri kan jina da kukayi shiru kwana biyu,naga sak'onninku kuma nagode Allah ya bar zumunci da k'auna. Na samu hutun makaranta so insha Allahu zamu cigaba daga inda muka tsaya... Daga k'arshe ina muku fatan alkhairi,Happy new year...

Page 05

°
Wajen k'arfe bakwai na safiyar yau Zuwaira ta gama d'umama sauran tuwon da suka ci jiya akan zasu karya dashi yanzun. Ta raba ta sama kowa nashi sannan ta kira Aminu yazo ya d'auka ma Babanshi nashi ya kai,ita kuma ta d'au na Umma ta nufa d'akinta dan kai mata. Ganin har yanzu tana bacci yasa ta tab'e bakinta tareda fad'in "sabon salo,inba lalaci ba me zaisa har yanzu ace mutum bai tashi daga barci ba",tana kaiwa nan ta juya ba tareda tashinta ba.

D'aukan nata tayi sannan ta nufa k'ofar d'akinta inda ta zauna ta fara cin tuwon.Bayan sun gama sai Mahdi ya shirya ya tafi kasuwa,Aminu kuma makaranta ya tafi saiya rage saura Zuwaira ita kad'ai a cikin gidan. Itama bayan ta gyara gida tayi wanke wanke saita kwanta bacci,ba ita ta tashi ba sai wajen sha biyun rana.

Ta fito waje tareda neman kujera ta zauna kafin ta ware a baccin tasan me zata dafa musu na rana. Kukan akuya ta jiyo a d'akin Umma shine ya juyo da hankalinta wajen,ganin bata ji Umma ta koro akuyar ba yasa ta tashi taje dan ganin ko Umman bata ciki neh.

Tana shiga kuma taganta a cikin d'akin kwance a kan shimfid'ar ta kamar yadda tazo d'azu ta ganta. Abin ya d'aure ma Zuwaira kai sosai,nan ta shiga tashin ta amma ina shiru kake ji. Ta d'aga hanunta taji baya motsi kuma bata numfashi,nan ta tabbatarwa kanta cewa Umma ta mutu. Abinka da zuciya kuma ta musulunci dole ta d'anji wani abu ganin gawar Umma,saidai bai wani dameta sosai ba.

Tashi tayi ta nufa k'ofar gida wurjajan kamar an korota,tayi kiran wani yaron makw'aftan su sannan ta aikeshi yaje ya kira mata Mahdi a kasuwa,da gudu yaron yaje aikan kasancewar yadda tajaa mishi kunne kan yayi saurin.

Bayan kaman 15mins da aiken yaron saiga Mahdi ya dawo gida dake akwai y'ar tafiya daga kasuwar zuwa gida kuma ba abin hawa gareshi ba. Yana shigowa Zuwaira ta ruga inda yake da gudu tana kuka tana nuna mishi d'akin Umma,a zatonshi ma wani abun Umman tayi mata,tambayarta ya shiga yi "lafiyarki,meya faru?". Zuwaira dai yau babu bakin amsawa sai janshi da tayi har izuwa d'akin. Suna shiga ta zube a k'asa gaban Umma tana zuba kuka.

Anan neh hankalin Mahdi ya soma tashi dan tunanin da yazo mishi a rai sanda ya ganta,shima tsugunawar yayi kisada ita yana kiran sunanta "Umma! Umma lafiya kuwa,meya sameki?",kuka ya shiga yi kamar mace. Sai lokacin Zuwaira ta dubeshi dan taga kamar be fahimci halinda Umman ke ciki bane,tace "Mahdi saidai hak'uri fa dan Umma ta riga mugidan gaskiya",ta wani jaa numfashi bayan ta fad'i hakan.

Wani dummm Mahdi yaji,kanshi ya d'au zafi saidai babu yadda zaiyi tunda dama mutuwar dolece kuma kowa ma zaman jiranta yakeyi. Nan ya tashi ya fita yayi kiran mak'ota akazo ana k'ok'arin yi mata wanka. Kafin nan saiya tafi gidan Kawu Bello dan sanarda shi rasuwar,yaci sa'ar samun shi a gida kuwa saidai daga farko korarsa yayi da cewa karya yadda ya shigo mishi gida kuma karya yadda ya sake zuwa koda ta layin gidanshi neh.

Saidai jin maganar dake tafe da Mahdi yasa shi jin sanyin jiki,gabad'aya ya rasa samun nutsuwa. Tare suka koma gidan inda suka tarar har anyi mata wanka,nan aka sanar a masallaci tareda yi mata sallah a masallacin juma'a. Bayan an kammala komai sai aka d'auketa aka kaita kabari. _*Allahu akbar,Allah kasa muyi mutuwar shahada,kasa muyi dace da samun rahamarka dan darajar al'arshi,ameen*_.

Bayan an kaita anyi mata addu'o'i sai kowa ya dawo gida,aka bar y'an uwa da koke koke. Nan aka shiga dafe-dafen abincin bak'i y'an gaisuwa. Haka ranar ta kasance musu babu dad'i.

Washegari ma an karb'a bak'i sosae,masu zaman makoki da kuma masu zuwa ta'aziyya su fita duk dai gasunan. Haka aka jera kwana uku anayi. Abu kamar ba zai wuce ba,yau kimanin sati guda kenan da rasuwar..

    hghausanovelseries.blogspot.com

Share:

No comments:

Post a Comment

Popular Posts

Translate

Archive

featured post

UNIVERSITY GIRL Final episode(Chapter thirty)

Powered by Blogger.

Contact Form

Name

Email *

Message *

Blog Archive