🌸🦋🌸🦋🌸🦋🌸🦋🌸
*ALHAKI NEH!*
🌸🦋🌸🦋🌸🦋🌸🦋🌸🦋
® *_REAL PURE MOMENT OF LIFE WRITERS_*
_ɯɛ ɖơŋ'ŧ ơŋٳყ ɛŋŧɛřŧąıŋ ŋɖ ɛɖųĆąŧɛ, ცųŧ ɯɛ ąٳŞơ ŧơųĆɧ ŧɧɛ ɧɛąřŧ ơʄ řɛąɖɛřŞ_
By the applomb writer: *Hamagee*
Feb,2018.
# WWW.PMLWRITERS@GMAIL.COM
# IG PML WRITERS
# https://www.facebook.com/PML_-Writers-FANS-459256761123035
# http://maryamsbello.blogspot.com
Wattpad @Hama_gee
Page 11
°
Tun Zainab na makaranta Allah ya d'ora mata jarabar son Aminu,sau da dama takan fad'a ma Ummanta amma a kowane lokaci sai Umman nata ta kwantar mata da hankali kan cewa ta bari ya kammala karatun shi dan ba aure zaiyi ba yanzun. Ta bari in ya kammala zatayi wa Zuwaira magana sai asuka san yadda za'ayi not knowing that Aminu zai samu mata tun kafin ya kammala karatun. Ba zata suka ji auren Aminu ya taso,babu yadda iya sai haquri amma Umman tasha fad'a mata cewa idanma bata samu shiga ata farko ba ai namiji mijin mace hud'u neh tunda tana sonshi.
Zuwaira ceh ta d'an tab'a Adda Hansatu kafin tace "keh k'awata muna kan magana,Aminu dai ko zuwa dubamu bayayi tunda yayi auren nan". Adda Hansatu cikin zabura kamar an mintsineta tsabagen gulma tace "karki fad'a mun,yanzu rashin mutuncin matar shin harya kai ga hakan?". Zuwaira ta d'anyi guntun tsaki kafin tace "keh dai bari kawai,shiyasa ma nazo wajenki dan nasan baki rasa mafita wa mutum,dan nikam da harna fara tunanin zuwa gurin malami dan inaganin asirce min harnashi tayi". Da sauri Adda Hansatu ta tareta "a'a haba Zuwaira ,gara da kika taho wajen nawa neman shawarar ma".
Baki kawai Zuwaira ta sake tana kallon Adda Hansatu,Adda Hansatun ce ta cigaba "akwai mafita ai,mafitar kuwa itace kisa shi ya sake aure". Waro ido Zuwaira tayi tareda fad'in "aure dai!". Adda Hansatu tace "aure fa,inba hakan ba ta yaya zakiyi ki janyo kan d'an naki gareki,ai yanzu kina sa shi ya aure wacce kike so to an gama dan gabad'aya sai yadda kika ce za'ayi".
Shiru Zuwaira tayi kamar me yin nazari sai kuma ta dawo da kallonta ga Adda Hansatu,tace "amma maganarki da k'amshin gaskiya k'awata",Adda Hansatu tayi murmushi kafin tace "kina wasa dani kenan". Zuwaira tace "ai daman sanin kine yasa nace bari na kawo kuka na gunki". Adda Hansatu tace "hakane sannan".
Zuwaira ce tace "amma ba wannan ba,babban matsalar itace ina zanga idon Aminun ballentana har in taso mishi da wannan maganar? Kuma kin san ba ganin girmana yakeyi ba ballantana tunda inda yana ganin girman nawa da bazai rink'a yin abinda yake yin nan ba. Sannan wa nake da ita da zan had'ata da Aminun inma ya yardan?".
Wani irin dariya Adda Hansatu ta sake wanda yasa har Zuwaira ta fara tsarguwa. Can dai tace "wannan duk ba wata matsala bace ai,kin ga anan zan iya ceh miki fad'uwa tazo daidai da zama dan Zainab ba k'aramin k'aunar Aminu takeyi ba,baki ga yadda ta sauya ba gabad'aya jin na ambaci sunan shi?". Zuwaira tace "tabbas kuwa,gashi Zainab kam 'yace ma sai abinda muka ceh". Adda Hansatu tace "kw'arai kuwa,maganar samun shi kuwa zuwa zakiyi har Bauchin ki gamu dashi,ki nuna mishi da gaske kikeyi tunda d'ankine zaibi abinda kike so koda dan gudun fushin ubangijin shi".
Zuwaira tace "kema fa kince wani abun,dan kam gaskiya bazan zauna ina uwarshi ace kuma wata tana juya minshi ba,wannan ba zai yiwu ba wallahi",haka Adda Hadiza tayita zugata ita kuma kanta na huruwa harta yanke shawarar nanda sati guda zata je Bauchin. Bayan sun gama shawarwarinsu sai Adda Hansatu ta rakata sannan ta dawo gida.
www.hghausanovelseries.blogspot.com