[5:40pm, 1/6/2017] Hamagee: 🍁🌿🍁🌿 *MAFARKIN HAMAGEE 2* 🌿🍁🌿🍁 ®WISDOM OFFICIAL WRITERS *_In devotion to Sis Feedy_*❤ Page 021 Several years ltr,, Zeedat da Jaheed na hango a gindin wani rafi kan dutse sunata wasa da dariya,sun girma sun qara kyau abunsu,Zeedat nada kimanin shekaru 21 yanxu haka,shikuma Jaheed 19years kenan.Daka gansu kaga y'an gida d'aya saboda yanayin jikinsu iri d'aya,dogaye neh kuma basuda jiki gasu farare tass ga kyau,saedae ita Zeedat kamannin mamarta tayo shi kuma Jaheed da babansu yake kama sarki kenan,wani in ya gansu ma zaece y'an biyu neh saboda kansu d'aya.Babban matsalarsu a yanxu itace rashin jituwar iyayensu dan ko had'uwar da sukeyi a waje ma bada sanin iyayen bane,saedae sum sha alwashin sae sun daedaeta tsakaninsu koba dad'e koba jima tunda yanxu sune masu tasowa iyayen kuwa gangarawa sukeyi. Suna cikin haka sae Jaheed yace "zaki wuce yanxu neh dan nikam na gaji gida zani yanxu",Zeedat tace "yanxun harka gaji,yaushe ma muka fito",Jaheed yace "ae idan baki manta ba mun riga ku fitowa ba anan kka sameni ba?",tace "haka ne kam amma ae lokacin kace baka jima kaima da fitiwa ba",yace "iyi,bakji yunwar da nake ji bane",Zeedat tayi dariya tace "yanxu naji magana,dama kwae kace mun yunwar kke ji mana",shima dariyar yyi sannan yace "kinga tafiyata sae kin dawo",Zeedat tace "toh saena zo dan nikam ba yanxu ba gaskiya",Jaheed ya miqe Fadawansa suka rufa masa baya sukayi gida.. ©Hama G Muh'd [5:40pm, 1/6/2017] Hamagee: 🍁🌿🍁🌿 *MAFARKIN HAMAGEE 2* 🌿🍁🌿🍁 ®WISDOM OFFICIAL WRITERS *_In devotion to Sis Feedy_*❤ Page 022 Zeedat kuwa cigaba tayi da wasanta da ruwa,acikin hadimanta akwae wata wacce ta yadda da ita me suna *SUNAM*,Sunam yarinya ceh me mutunci da daraja babba,tasan hakkin dan Adam sosae kuma batada hayaniya,gata da gaskiya da rik'on amana wanda hakan yasa Zeedat ta yarda da ita. "Sanam",Zeedat ta kira sunanta,"naam"ta ansa da wata iriyar murna me shegen dad'in ji,Zeedat tace da ita "zoki gani,kamar mutum a can",sae tayi mata nuni da wani waje inda mutum yake tafiya shi kadae da gani kuma hunter neh,Sanam tace "kwarae kuwa naga mutum gashi can kamar ma maharbi neh",Zeedat tace "kaman dae kam",can da suka qure mishi kallo sae sukaga ashe inda suke yake nufowa,Sanam tace "gimbiya Zeedat mu bar wajen nan dan ko tabbas mu yake tunkarowa wataqil ma ganinmu yasa shi zuwa nan",cikeda rashin kulawa Zeedat tace "toh laifin me mukayi mishi da zamuji tsoron shi mu har wajen",Sanam tace "ba haka bane ranki shi dad'e ina jin tsoron mutane neh dan bamu sani ba ko mugu neh",Zeedat tace "ae koma miye shi bbu yadda ya iya damu tunda bamu shiga mishi hidima ba toh haka nan shima be isa ya shiga namu ba,ki dena tsoro bbu abunda zae faru"Sanam dae kwae tana jinta neh amma duk ta tsorata da zuwan mutumin nan.. ©Hama G Muh'd [5:40pm, 1/6/2017] Hamagee: 🍁🌿🍁🌿 *MAFARKIN HAMAGEE 2* 🌿🍁🌿🍁 ®WISDOM OFFICIAL WRITERS *_In devotion to Sis Feedy_*❤ Page 023 Mutumin nan na qarasowa inda suke ya tsaya a daedae inda Zeedat take zaune,wucewa yazo yi amma ganinta ya sanya shi tsayawa.Bata ceh dashi komai ba iyakaci tasan ya mugun burgeta dan ba kad'an ba yyi kamada jarumi gashi fari kyakyawa kamar balarabe,infact shigarsa ma ta larabawa yyi,da kamar zae wuce sae kuma ya tsaya dan sosae Zeedat ta burge shi dukda cewa shi baya kula mata amna yau ya d'au aniyar kulawa,yace da ita "assalamu alaiki baiwar Allah",Zeedat ta shiga tunani aranta take tambayar kanta 'tooo menene kuma wannan daya fad'i,na biyun kuma Allah! Toh menene hakan yake nufi',Bawan Allahn ya fahimci rud'un data shiga dan haka yace da ita "ko baki jin yaren dana keyi neh?",Zeedat tace "naji wannan amma ban gane me kace daga farko ba kuma naji kace Allah,shin meyake nufi? Kuma ni y'ar Sarki ceh ba baiwa ba dan naji d'azu ka ambaci baiwa",cikeda mamaki yake kallonta,yaya za'ayi ace mutum besan Allah ba afterall shine mahaliccinmu kuma mamallakin mu gabaki d'aya,ya daure ya b'oye mamakin sa yace mata "amma keh ba musulma bace koh?",da wani sabon mamakin ta kalleshi tace "musulma!menene shi din?",wani irin mamakinta neh ya kamashi a ranshi yake fad'in 'lallae wannan jahilci yyi mata yawa,dama ashe akwae irin way'annan har yanzu a duniya,toh ae ko kafirai sunsan musulunci kwae dae aeki dashi neh bazasu yi ba,toh insha Allahu saena warkar da wannan baiwar Allahn daga wannan duhun jahilcin da take ciki,Allah ka bani iko da damar yin hakan'... ©Hama G Muh'd [5:41pm, 1/6/2017] Hamagee: 🍁🌿🍁🌿 *MAFARKIN HAMAGEE 2* 🌿🍁🌿🍁 ®WISDOM OFFICIAL WRITERS *_In devotion to Sis Feedy_*❤ Page 024 Ya kalli Zeedat yace "ni sunana Abdulmud'allib amma ana kirana da Mud'allib",Zeedat tace "suna me dad'i,ni kuma sunana Zeedat",ya maimaita sunan "Zeedat",saeya kalleta yace "suna me dd'i,da zaki bani dama dana koyar dake addinin musulunci,addinin daya fi dacewa dake da kowa ma.Lallae had'uwar mu alkhairi ceh garemu baki d'aya",Zeedat tayi shiru tana sauraren shi,ita dae wannan baqo na burge ta matuqa dan haka take so ta bashi had'in kai don koyar da ita yanayin rayuwar shi ko zae taimaka mata itama,Mud'allib ya kalleta yace "toh malama Zeedat ni zan wuce garinmu,a nan kusada kuu muke dan haka gobe insha Allahu ina so mu had'u anan kuma keh kad'ae karki sanar da kowa zuwanki nan saboda bazan cutar dake ba dan mu addininmu yyi mana hani da mu cutar da d'an uwanmu",cikeda zumud'i Zeedat tace "amma zanso insan addinin nan naku da baya son wani ya zalunci wani dan babban abunda keh damuna kenan da mutanen garin nan akwae zalunci,kuma naji ka ambaci wani abu yanxunnan wae insha Aallhu,koh zaka sanarda ni abunda hakan keh nufi",Mud'allib ya kalleta yace "tabbas zan sanarda keh kuma zan koyar dake dukkanin abunda ya shafi addinin mu amma sae gobe in mun had'u kamar yadda nace kada ki sanarda kowa zuwanki nan ke kad'ae kuma zaki zo",Zeedat ta d'anyi jim na wani lokaci sae kuma ta fara magana kamar dae wacce ta tuno wani abun "abunda yafi yanxu shine karmu had'u anan,dan idan muka had'u qanina zae iya biyoni dan ya saba idan be ganni ba toh nan yake zuwa dan nice ma na sabar mishi da zuwa nan hutawa dan haka barin maka kwatancen wani wajen daban",Mud'allin yaji dad'in hakan dan haka tayi mishi kwatancen inda zasu had'u da kuma lokacin da zasu had'un.. ©Hama G Muh'd [5:41pm, 1/6/2017] Hamagee: 🍁🌿🍁🌿 *MAFARKIN HAMAGEE 2* 🌿🍁🌿🍁 ®WISDOM OFFICIAL WRITERS *_In devotion to Sis Feedy_*❤ Page 025 Godiya Mud'allib yyi mata sannan sukayi sallama ya tafi,saeda Zeedat ta daena ganinsa kafinnan ta juyo ta kira Sanam tace da ita su tafi,suna tafe suna d'an hiransu kamar qawaye saedae duk yadda Sanam taso jin hirarsu Zeedat da baqonnan Zeedat taqi fad'a mata komai illa sunanshi data gaya mata,a haka har suka iso gida. Koda Mud'allib ya koma gida yau ba'a gane mishi dukda cewa ba mai magana bane dama amma yau ya fita daban,sannan be samu yyi bacci ba da dare yyi,tunanin Zeedat neh ya hanashi baccin,alla alla yake gobe tayi dan su sake had'uwa dan shi ya matsu yaga Zeedat ta zama musulma auren ta kuma yake sonyi dan tunda yake be tab'a ganin mace kamarta ba,gata kyakykyawa me kaifin basira dan daga gani qwaqwalwarta zata d'au abu da wuri,gata y'ar sarauta amma bata ji da kanta,wani abunda ya qara burgeshi da ita shine lokacinda tace mishi zata yadda ta abunda addinin shi yace saboda su garinsu bisa zalunci yake tafiya ita kuma bata son hakan.Saeda aka kira sallahr asuba Mud'allib be runtsa ba dan haka ya tashi yyi alwala yazo ya gabatar da nafilfilu sannan yaje massalaci yyi asubar shi a jam'i,saeda gari ya waye kafinnan ya idar da karatun kurani da yakeyi wanda hakan dabi'ar ceh tukunna ya dawo gida,sae a lokacin ya samu yyi bacci da niyyar qarfe goma zae tashi ya shirya dan zuwa inda sukayi da Zeedat zasu had'u dama 12 sukayi zasu had'un. A wajen Zeedat ma batayi baccin kirki ba sae tunanin Mud'allib takeyi,bata samu tayi bacci ba sae wajen qarfe 3 dan haka ba ita ta tashi ba sae qarfe 10:30,tana tashi tayi wanka ta shirya saeta fito ta gaida mamanta da Haima dake zaune kusada maman suna tattaunawa,bayan ta gaida sune saeta zauna tayi karin kummalon ta a wajen.. ©Hama G Muh'd [5:41pm, 1/6/2017] Hamagee: 🍁🌿🍁🌿 *MAFARKIN HAMAGEE 2* 🌿🍁🌿🍁 ®WISDOM OFFICIAL WRITERS *_In devotion to Sis Feedy_*❤ Page 026 Kamar yadda Mud'allib ya tsara zae tashi qarfe 10,toh hakan ya tashi,bbu b'ata lokaci ya tashi yazo ya shirya yyi karin kummalo sannan ya fito yazo ya gaida Ummee dan haka yake kiran maman shi,babanshi kuma tun a masallaci suka gaisa dan haka be tsaya wata wata ba ya fita dan zuwa garinsu Zeedat,qarfe 10:30am ya fito bashi ya isaba sae 11:50am. Bayan Zeedat ta kammala karin lokacin 11:00am daedae dan haka bata motsa daga inda take ba ta zauna sukayi ta hira dasu mamanta sae 11:40am dot,ta lallab'a ta bar wajen,d'aki ta koma inda ta wata qofa ta fita lokacin 11:500am daedae,bbu nisa sosae da gurin da sukayi zasu had'un dan haka 11:58am ta isa. A daedae wajen ta sameshi yana jiranta,suka gaisa sannan suka nemi gurin zama sannan suka fara maganarsu kamar yadda yyi alqawarin koyarda ita musulunci haka yyi iyaka bakin qoqarinsa da fahimtarsa ya sanarda ita komai,kama daga yadda ake sallah,azumi da duk wani abun da ya shafi addinin islam,sannan ya bata tarihin annabawa da mutanen daa sosae,Zeedat kuwa tayi kuka harta gode Allah,a yanxu halinda ake ciki Zeedat ta musulunta,dan haka tare ma sukayi sallahr azahar da niyywr idan taje gida zatayi kamar yadda ya gwada mata (bayan tayi wankan tsarki kenan),yanxu sun yanke shawarar kullum zasu ringa had'uwa a wajen yana koyar da ita karatun alqur'ani me girma da wasu littafan musulunci.. ©Hama G Muh'd [5:42pm, 1/6/2017] Hamagee: 🍁🌿🍁🌿 *MAFARKIN HAMAGEE 2* 🌿🍁🌿🍁 ®WISDOM OFFICIAL WRITERS *_In devotion to Sis Feedy_*❤ Page 027 Yau tun da safe Jaheed ke neman Zeedat,koda ya tambayi Sanam saeta ceh mishi itama bata ganshi ba da kamar zata sanarda shi cewa sun had'u da wani jiya amma saeta fasa,Jaheed ya damu matuqa gashi baya son shiga sashensu dan mamansu tace idan ya sake ya shiga sashen saeta yi fushi dashi,dan haka ya wuce zae fita,a qofar fita ya tambayi masu gadi ko sunga fitar Zeedat,d'aya daga cikinsu yace qwarae yaga sanda ta fita d'azun nan,Jaheed ya tambaye shi ko ya san ta inda tabi sae megadin yace gaskiya be sani,kai tsaye Jaheed ya bar gidan inda ya nufa wajen da suke had'uwa da Zeedat neh wato gindin wannan rafin. Yana tafe guards d'insa na biye dashi har suka iso wajen,ganinta yasa yaji relief ya qarasa inda take zaune tana jifan duwatsu cikin ruwan ya zauna,tana ganin shi ita kuma ta sakar mishi murmushi tace "sae yanxu ka fito",yace "iyi bayan nayi ta neman ki tun d'azu ban samu ba,meyasa kka fito keh kadae ga can Sanam a gida itama tana cikiyar ki?",Zeedat tace "kwae yau banjin ayi mun rakiya neh,kuma nasan kaima idan ka fito nan zaka zo",saeta sakar mishi wani murmushi,shima murmushin yyi mata.Basu wani jima sosae a gurin ba suka tashi suka koma gida,tun a mashigar gidan suka rabu karma wani ya gansu yaje ya fad'a ma Wahiyya.. ©Hama G Muh'd [5:42pm, 1/6/2017] Hamagee: 🍁🌿🍁🌿 *MAFARKIN HAMAGEE 2* 🌿🍁🌿🍁 ®WISDOM OFFICIAL WRITERS *_In devotion to Sis Feedy_*❤ Page 028 Zeedat na shiga taje ta gaida mamanta da Haima dake zaune da ita sannan ta koma d'aki inda ta gabatar da sallah tareda bitan karatun da Mud'allib ya qara mata yau,wani sauyin yanayi take ji a rayuwarta kamar wacce aka cire ta cikin wani qangi,ko dayake qangin neh! Koda yaushe Zeedat ta tuno Mud'allib son shine yake qaruwa mata a rai,yana burgeta matuqa dan bata qi ace su kasance tare a koda yaushe ba.Shima Mud'allib haka yake a wajen shi yana son Zeedat matuqa saedae be fad'a mata ba,ya d'au alwashin gobe idan suka had'u zae sanarda ita abunda ke ranshi saedae besan ko zata amince ba. Washegari kamar yadda suka tsara zasu had'u hakan sukayi,bayan ya gama koya mata karatun neh ya sanarda ita abunda ke cikin ranshi na cewa yana sonta,itama ta amince mishi,godiya yyi mata kafin suka rabu bayan sunyi sallahn azahar tare.Ya d'an mata rakiya kafin ya juya ya tafi gida shima a ranshi yana mugun jin dad'i.. ©Hama G Muh'd [5:43pm, 1/6/2017] Hamagee: 🍁🌿🍁🌿 *MAFARKIN HAMAGEE 2* 🌿🍁🌿🍁 ®WISDOM OFFICIAL WRITERS *_In devotion to Sis Feedy_*❤ Page 029 Yaukam Zeedat bata da niyyar zama a wannan wajen da suka saba had'uwa da Jaheed dan tasan lokacin la'asar ya kusa shiyasa kwae ta wuce abunda kai tsaye tayi gida. Sarki yanzu ya fara tsufa saboda haka ya rage biyewa Wahiyya kan wasu abubuwan da takeyi dan haka yanxu ta tsaneshi bata sonshi dan harta fara tura ma d'ansa qwalli d'aya wato Jaheed tsanarshi,ta sanarda Jaheed wasu abubuwa da uban yyi wanda duk wani me hankali zaiji ya fita a ranshi wanda kuma dukda had'in kanta akayi wasu kanma ita ta sashi yyi su,amma yanxu tana ware kanta. Saedae duk abubuwan nan bata nunawa sarki a idonshi cewa bata qaunarshi,a halinda ake ciki ma neman hanyar da mulki zae bar hannun shi ya koma na d'anta takeyi dan a ganinta a yanxu Sarki baida wani amfani a gurinta.Wahiyya kenan butulu!! Yaayi kuwa na nan hankalinsu kwance da y'arta Zeedat,basuda wata damuwa yanxu,dama damuwar kenan ta rashin kulawa daga Sarki wanda yanxu kam ma ya zame musu jiki dan ko kwata kwata ya daena damun su.Barinma Zeedat da daman tun haihuwar ta bata san miye gata da jin dad'in uba ba,a yanxu maganar sauya rayuwar dukkanin y'an garin neh a ranta zuwaga tafarki mafi gaskiya mafi b'ullewa wanda tana jiran lokacin da Mud'allib zai bata izini neh kwae.. ©Hama G Muh'd [5:43pm, 1/6/2017] Hamagee: 🍁🌿🍁🌿 *MAFARKIN HAMAGEE 2* 🌿🍁🌿🍁 ®WISDOM OFFICIAL WRITERS *_In devotion to Sis Feedy_*❤ Page 030 Yanzu ya zame wa Zeedat da Mud'allib jiki,kullum sae sun had'u a wannan wajen yyi ta koyarda ita abubuwa masu tarin yawa gameda addinin musulunci wanda ita kuma take ta qara zurfafa a cikinsa,dad'in shi da ita kuwa komai ya koya mata bata mantawa yana nan a zaune,a halinda ake ciki yanxu ma harta kai izu 25 na qur'ani,kuma hadda ceh me kyau a kanta ba wae ko irin na muna hadda ba. Kullum maganar Jaheed a yanxu ita ce ina Zeedat ke zuwa kullum saeta tafi wani waje ta barshi,ita kuma saeta ceh mishi ae inta fito kafin yazo neh saeta d'an fara zagawa. Sarki na kwance a d'akin Wahiyya duk damuwa ta isheshi,tunanin Yaayi da y'arshi kawae yake yi da irin zaluntar su da yyi tayi a baya akan Wahiyya,motsin da yaji neh ya dawo dashi daga tunanin da yake yi,Wahiyya ceh riqeda kwarya da barasa a cikinta,tana wani kwarkwasa kamar yadda ta saba mishi sae tace "meke damun sarki neh?",Sarki ya dubeta yace "bbu komai sae tsufa",tayi murmushi irin nata na shaid'anun matan nan sae tace "ga me kore damuwa nan,abunda kafi son sha dan d'ebe kewa wato barasa,gata da sanyi",a take Sarki ya miqe ya zauna dan da gaske yana son shan barasa koda ba a cikin damuwa yake ba,Wahiyya ta miqa mishi ya qarb'a yasha,bayan ya gama sha ya kwanta a wurin duk ya bugu.. ©Hama G Muh'd [5:43pm, 1/6/2017] Hamagee: 🍁🌿🍁🌿 *MAFARKIN HAMAGEE 2* 🌿🍁🌿🍁 ®WISDOM OFFICIAL WRITERS *_In devotion to Sis Feedy_*❤ Page 031 Aina da Wahiyya na zaune suna tattaunawa kan abunda suka aikata,dan Aina ceh ta kawo ma Wahiyya maganin data Saka ma Sarki wae dan ya nakasa a d'aura d'anta Jaheed a kan karagar mulki,Wahiyya na sanarda Aina cewa Sarki yasha barasar kuma yanzu haka yyi barci daga ji idan ya tashi aikinsu yyi,Aina ta kwashe da dariyar mugunta tace "lallae me jiran kujera ya zamo me ita zuwa gobe nasan Sarki zae tashi a nakashe kuma nanda wasu y'an kwanaki idan aka ga Sarki ba zae iya komai ba nasan za'a d'aura me girma Jaheed a kan kujerar Sarki",cikeda zumud'i Wahiyya tace "haka neh zancen ki". Bayan d'an wani lokaci,Wahiyya ceh ke magana da wasu fadwa da tasa aka yo mata kiransu,kome tace musu?oho! Nidae naga ta basu y'an silalla a jikin wata y'ar qaramar jaka,su kuma suna ta murna,su biyu neh fadawan,bayan ta basu sae suka fice suka koma bakin aikinsu. •••••••••••••••••••••••••••••••• Later at night,, Aina na kwance tana sharar bacci a d'akinta dan dama ba'a d'akin Wahiyya take kwana ba,wasu mutane neh suka shigo a hankali fiskokin su duk a rufe,sun saka baqaqen kaya kowannen su kuwa takobi neh a hannunshi,basu tsaya wata wata ba d'ayansu ya tashi Aina sae d'ayan yyi saurin sa mata tsumma ya toshe mata baki.. ©Hama G Muh'd [5:47pm, 1/6/2017] Hamagee: 🍁🌿🍁🌿 *MAFARKIN HAMAGEE 2* 🌿🍁🌿🍁 ®WISDOM OFFICIAL WRITERS *_In devotion to Sis Feedy_*❤ Page 032 D'ayan na toshe bakinta sae wanda ya tashe tan yace mata "kin san *shi ramin qarya qurarre neh*,kuma hausawa sukan ce *idan zaka gina raminka na mugunta,toh ka gina shi daedae da kai dan tabbas wata ran kaine zaka afka cikinshi* saboda haka kin toni wanda yafi ki kuma bbu makawa haka zaki afku cikin shi,batare da wani b'ata lokaci ba gimbiya ceh ta aiko mu kashe ki wato uwargidan ki matar sarki Jaisus kuma biyanmu zatayi da abu mafi soyuwa a zuqatan y'an Adam,saboda haka yanxu zamu cika aikinmu",idanun Aina duk sun firfito waje da jin wanga batu,jikinta kuwa sae rawa yake yi,tuni ta tsulo fitsari a gurin,bafaden nan da ya toshe mata baki neh yyi maza ya fille kanta agurin bbu ko tausayi,ta kai kusan mintuna 20 kafin jikinta ya daina motsi,su kuma shegun tuni suka watse suka bar d'akin. Washegari da safe magana ya bazu a fada cewa anyi kisan gilla ma Aina,Sarauniya Wahiyya kuwa murna taji kamar meh dan a ganinta yanxu asirinta bazae tonu ba,saedae a gaban jama'a nuna tayi rashin Aina takeyi,koda aka tambayi sarki kuwa saeta ceh tun safe take tashin sa amma yaqi tashi sae surutai da yake tayi shi kad'ae,koda Jaheed yaji haka hankalinshi be wani tashi ba Wahiyya ceh tasa aka yo mata kiran likita tazo ta duba sarki. Bayan ta duba shi saeta tabbatar wa mutane cewa Sarki ya nakasa dan ko tashi da kanshi ba zae sake iyawa ba,murna wajen Wahiyya ba'a magana,sae dae cikin mutane tana nuna damuwarta.. ©Hama G Muh'd [5:48pm, 1/6/2017] Hamagee: 🍁🌿🍁🌿 *MAFARKIN HAMAGEE 2* 🌿🍁🌿🍁 ®WISDOM OFFICIAL WRITERS *_In devotion to Sis Feedy_*❤ Page 033 Jaheed ya d'an tausaya ma sarki da yaji abunda ya sameshi qwarai,saedae idan ya tuno da abubuwan da yyi sae yaji kwae ya tsane shi.Labari ko da ya iske Yaayi da Zeedat basuji dad'i ba musanman Zeedat wacce tasha alwashin musuluntar dashi kafin ya koma ga Allah. Koda Zeedat da Mud'allib suka had'u yau,ya fahimci akwae abunda yake damun Zeedat dan haka ya tambayeta,ita ko bata b'oye mishi ba ta sanar mishi komai ta kuma fad'a mishi cewar tana son ta sa baban ta ya karb'i muaulunci,Mud'allib be musa mata ba yanxu kam dan a halinda ake ciki ya yarda da Zeedat kuma ya san ba kad'an ba yanxu tayi nisa cikin musulunci kuma imaninta ba zae bari wani ko wata su rinjaye ta zuwa ga kafirci ba.Ba tareda sun jima ba yace taje tasan duk yadda zatayi taga babanta dan musuluntar dashi kafin ace ya mutu,koda sukayi sallama bata tsaya ko ina ba dan yau Jaheed yace mata bazae fita ba dama,sae gida. Hamdala tayi data samu an mayarda baban can side d'inshi yanxu ya bar sashen Wahiyya kenan,koda ta shiga sae sarki ya fara koke koke yana neman yafiyarta,itama kukan ta shiga yi tana ce mishi ba komai ta yafe ae shi babanta neh kuma ta d'au mishi alqawarin nema mishi gafarar mamanta ma. Ko kad'an zeedat bata sha wuya wajen musuluntar dashi ba,nan ya sanarda ita *mafarkin* da yayi kwanan nan wanda shiyasa shi ya dawo sonta kamar rae,wae yyi *mafarkin* y'an garin nan suna cikin duhu wanda ko ganin d'an uwanka baka iyawa tsabagen duhun da suke fuskanta,wae sae tazo ta kawo musu haske wanda saeda tasa ma baban hasken kafin nan tasa ma sauran al'ummar.. ©Hama G Muh'd [5:48pm, 1/6/2017] Hamagee: 🍁🌿🍁🌿 *MAFARKIN HAMAGEE 2* 🌿🍁🌿🍁 ®WISDOM OFFICIAL WRITERS *_In devotion to Sis Feedy_*❤ Page 034 Bayan ya gama bata labarin *Mafarkin* sae yace lallae wannan *mafarki* nawa ya tabbata dan kuwa gashi na gani,Zeedat bata bar sashen ba saeta ta tabbatar ta sanarda shi duk abunda ya kamata ya sani ta kuma mishi alwala sunyi azahar tare sannan tace koda bata samu ta dawo anjima ba saboda kar mutane su fuskanci wani abu to yyi sallahr shi daga kwance kamar yadda ta koya mishi. Zeedat bata tsaya ko ina ba sae sashensu inda ta tararda mamanta da Haima,Zeedat ta kwashe duk yadda sukayi da Sarki ta fad'a musu,a take suka karb'i musulunci suma,koda lokacin la'asar kuwa yyi sukayi alwala bayan sunyi wanka sae sukaje sashen sarki,basu samu kowa ba kuwa,suka gana dashi sannan sukayi sallahn la'asar d'in,inda sarki ya nemi gafarar Yaayi,ita kuwa tace ba komai ta yafe.Tare sukayi sallahr magrib da isha'i kafinnan suka koma sashensu bayan sun tabbatar yaci abinci kuma baya da buqatar komai. Wahiyya kuwa tunda aka maida Sarki sashen shi bata sake koda leqawa bane. Washegari kamar yadda Zeedat ta saba had'uwa da Mud'allib suka had'u,yaji dad'in nasarar da sukayi na ceto rayuka har uku daga kafurci zuwa musulunci,yauma basu wani jima ba suka rabu bayan ta biya mishi karatun yau.. ©Hama G Muh'd [5:49pm, 1/6/2017] Hamagee: 🍁🌿🍁🌿 *MAFARKIN HAMAGEE 2* 🌿🍁🌿🍁 ®WISDOM OFFICIAL WRITERS *_In devotion to Sis Feedy_*❤ Page 035 Nasan kuma kunyi missing gidan Niyad da ja'i,to nima nafi ku missing dan haka bari d'an tab'o kad'an daga wajensu.. Niyad ceh zaune a tsakar gidan Ja'i na ta faman hura wutan dafa qwai (egg) wanda Niyad tasa shi dan yanxu komai shi yakeyi a gidan kasancewar Niyad nada ciki,yanzu haka cikin nada wata 7 kenan,saboda wannan yasa ta sake mishi duk wani aikin gidan yakeyi shi kad'ae,shima kuma Ja'in be damu ba saboda d'okin da yake,yanxun cewa tayi tana son cin qwan zabi shine yaje ya sayo yazo yake tafasa mata. "Wai kai har yanzu baka iya had'a wuta tana ci bbu hayaqi neh?duk ka cika ni da hayaqi",Ja'i yace "kiyi haquri yanxun nan zae kama kuma zaki daena jin hayaqin",tace "daka taimaki kanka". Bayan ya gama dafa qwan sae ya d'auki wani kwano ya saka a ciki sannan ya kai mata,ya ajiye kwanon a qasa yana b'are qwan sae tace mishi "haba Ja'i so kke saena mutu neh kafin ka gama b'are mun qwan?",Ja'i ya dubeta yace "haba Niyad duk saurin nan da nakeyi baki gani?",Niyad bata sake cewa komai ba harya gama ya miqa mata.A hankali take ci abunda,bbu wata damuwa a ranta,Niyad kenan sarkin jaraba!! ©Hama G Muh'd [5:49pm, 1/6/2017] Hamagee: 🍁🌿🍁🌿 *MAFARKIN HAMAGEE 2* 🌿🍁🌿🍁 ®WISDOM OFFICIAL WRITERS *_In devotion to Sis Feedy_*❤ Page 036 Sarki na kwance wasu daga cikin fadawan shi suka shigo wajenshi,inda sukayi mishi batun murabus da zaiyi tunda wannan ciwo nashi bana tashi bane,sukace ya kamata ya barma magajinsa gadon mulki wato Yarima Jaheed,koda sarki yaji haka saeya ceh yaji amma a d'an bashi lokaci dan yyi nazari a kai tukunna,Fadawa sukace bbu komai ko zuwa nanda kwana uku zasu dawo dan jin sakamakon da ya yanke.Suka tashi suka fita aka bar Sarki da shiga damuwa,baya son Yarima Jaheed ya zamo Sarki dan tabbas muguwar uwarshi zata iya juya shi tasaka yyi zalunci saboda ya lura yanzu yana d'aukar maganar ta fiyeda daa.A halin yanxu Sarki ya san komai gameda abunda Wahiyya tayi da kuma wanda take kanyi yanxu,ya zuba mata ido neh kwae yaga gudun ruwanta. Bayan d'an wani lokaci Zeedat ta shigo dan taimaka wa babanta yyi alwala yyi sallah,bayan ya idar saeta bashi abinci yaci ya qoshi,bayan nan suna cikin hira sae sarki ya kira sunanta "Zeedat!!",Zeedat ta ansa da "naam me martaba",ya cigaba "ina son muyi wata magana dake wanda kuwa maganar nada matuqar muhimmanci gare mu baki d'aya,magana ceh wadda ta shafi kyautuwar al'ummar garin nan namu wanda idan akayi wasa gyaran da muke neman yi ko ince kke neman yi lallae zai b'aci" ©Hama G Muh'd [5:50pm, 1/6/2017] Hamagee: 🍁🌿🍁🌿 *MAFARKIN HAMAGEE 2* 🌿🍁🌿🍁 ®WISDOM OFFICIAL WRITERS *_In devotion to Sis Feedy_*❤ Page 037 A rud'e tace "Allah ya baka nasara wace magana ceh haka?",sarki yace "ki kwantar da hankalin ki,idan har aka sab'a yin abunda nake so na fad'a neh shine za'a fuskanci matsala babba,d'azu daff shigowar ki waziri,galadima da kuma sarkin fada suka zo suka sameni kan maganar yin murabus a bama Yarima sarauta,ni kuma gaskiya nasan cewa idan har Yarima ya karb'i sarauta toh lallae irin sarautar da zaa cigaba dan koda ace yyi niyyar sauyawa bazae yiyu ba saboda Wahiyya bazata barshi ba dan ko nima ita tayi ta sani yin wasu abubuwan ballantana kuma d'anta,sannan tabbas rayuwarki na cikin had'ari shiyasa nace musu su bari nayi tunani akai tukunna",Zeedat ta d'an nisa sannan tace "toh yanzu me ka yanke? Kasan dole Yarima neh zae gaji sarautarka dan baka da wani magaji illa shi",Sarki yace "eh haka neh amma dole in samu mafita kafin nanda kwana uku da suka bani zasu dawo",Zeedat tace "toh Allah ya zab'ar da abunda zefi kasancewa alkhairi",Sarki yace "ameen",Zeedat tayi mishi sallama ta tafi,shi kuma sae tunani yakeyi. Koda su waziri suka bar sashen Sarki kai tsaye sashen Wahiyya suka nufa inda suka aiki wata baiwa ta sanarda ita zuwansu,koda baiwar ta fito saeta ceh wae su shiga.Bayan sun shiga suka zauna sannan suka karanto mata yadda sukayi da sarki,da jin hakan sae Wahiyya tace "koma miye dae bbu yadda zaeyi dan dolensa yyi murabus kuma Yarima neh zae hau dan bashida wanda yafi shi",sukace "wannan gaskiya ceh",sukayi mata sallama suka tafi.. ©Hama G Muh'd [5:50pm, 1/6/2017] Hamagee: 🍁🌿🍁🌿 *MAFARKIN HAMAGEE 2* 🌿🍁🌿🍁 ®WISDOM OFFICIAL WRITERS *_In devotion to Sis Feedy_*❤ Page 038 2 days later,, Zeedat na cikin tafiya zata gurinda suke had'uwa da Mud'allib kwae sae taji kamar motsin mutum a bayanta,abun ya bada tsoro matuqa dan a iya saninta ko Sanam bata yarda ta biyota balle kuma wasu,yau kimanin kwana uku kenan kullum sae taji irin wannan gashi idan ta juya bata ganin kowa dan wajen cike yake da dogayen ciyayi gasu green abun sha'awa kasancewar lokacin damina neh saedae daminar bata shiga sosae ba dan ba kullum ake ruwan ba ma,tayi qarfin hali ta cigaba da tafiya amma duk hankalinta na baya,a cikin kwanaki ukun data fuskanci ana binta canza hanya takeyi taje wani wajen sae daga baya saeta je inda suke had'uwan amma yau batada niyyar sake hanya dan haka kai tsaye taje wajen abunta. Ba wani bane me binta illa wani bawa daga cikin bayin Jaheed wanda shi Jaheed d'inne yasa shi ya gano mishi inda Zeedat ke zuwa kullum kuma a irin wannan lokacin gashi kuma ya gano wajen dan haka ya koma ya sanarda Jaheed komai,Jaheed yace mishi ya gode gobe zae raka shi wajen,ba kad'an ba Jaheed yyi mamakin ko waye wannan wanda Zeedat take zuwa kullum su had'u kuma ko tad'inshi bata tab'a yi mishi ba,shidae ya barma ranshi cewa koma wanene zae ganshi gobe kuma idan ya gano cewa cutarda ita yake neman yi toh bbu makawa zaesa a fille mishi kai kuma ko wanene shi.. ©Hama G Muh'd [5:50pm, 1/6/2017] Hamagee: 🍁🌿🍁🌿 *MAFARKIN HAMAGEE 2* 🌿🍁🌿🍁 ®WISDOM OFFICIAL WRITERS *_In devotion to Sis Feedy_*❤ Page 039 Bayan sun gama sae sukayi sallama Zeedat ta dawo gida,bayan ta shiga sashensu ta gaida maman saeta nufa sashen sarki kamar yadda ta saba kullum,ta gaida shi tayi mishi alwala yana kwance yyi sallah,haka itama tayi alwala tayi sallahr azahar,bayan sun idan ta saba sae sun d'anyi hira ta bashi abinci kafin ta tafi dan yanxu tace ma masu kulada shi cewa su barshi kwae ita zata ringa yi mishi komai dan ko kad'an Zeedat bata yarda da masu aikin gidan ba gani take kowa da maganar Wahiyya yake aiki bbu imani ko kad'an azuqatansu.Bayan ya gama cin abincin sae ya kirata "y'ata!",Zeedat taji dad'in wannan suna da ya kira ta shi saeta ansa mishi da "naam babana",ya cigaba "batun hukunci da nace zan yanke akan murabus neh,lallae nayi nazari sosae kuma na yanke hukunci cewa make zan barwa kujerata ta mulki bbu wata mafita idan ba ita ba",Zeedat cikeda damuwa tace "ni kuma baba?",yace "qwarai ke d'in,kuma inason ki karbeshi hannu bibbiyu dan hakan neh kwae zaesa addinin gaskiya wato addinin musulunci ya fad'ad'a a wannan garin,kuma na sanki da biyayya saboda haka nake roqonki don Allah karki qi,idan kuma d'an uwanki kke tunani toh ki daena dan na tabbatar bazae damuba saedae kwae Allah ya tsareki da sharrin Wahiyya",Zeedat da tuni ta fara kuka tace "ameen baba,kuma na amince zan karb'a amma saboda kare addini nah kad'ae",yace "Allah miki albarka amma kada ki fad'a ma kowa",tace "ameen babu meji insha Allah saedae Mud'allib dan bana iya b'oye mishi wani abu a kaina",yace "bbu damuwa",sukayi sallama sannan ta tafi.. ©Hama G Muh'd [5:51pm, 1/6/2017] Hamagee: 🍁🌿🍁🌿 *MAFARKIN HAMAGEE 2* 🌿🍁🌿🍁 ®WISDOM OFFICIAL WRITERS *_In devotion to Sis Feedy_*❤ Page 040 Washegari,, Da sassafe su waziri suka dawo mishi akan batun kwana uku da suka wuce,batareda b'ata lokaci ba Sarki yace dasu "na zauna nayi tunani da kaina kuma na yanke hukuncin zuwa nanda sati d'aya tak zanyi murabus kuma ba kowane me hawa kan karagar nan ba illa babbar y'ata wato Zeedat dan a iya tunani na bbu wanda ya dace face ita dan Yarima har yanxu yarone qarami be gama sanin zafin kansa bama balle yasan na al'umma",gaba d'ayansu suka cika da mamakin maganganun sarki dan su a tunaninsu bazae ko jaa da maganarsu ta bama Yarima sarauta ba dan a iya ganinsu yafi son Yarima fiyeda komai a kowa a duniya. Yau Jaheed tun sassafe ya shirya yake jiran fitan Zeedat dan binta yaga wanda suke ganawa dashi,be jima ba kuwa ta fito ita kad'ae ta tafi,seda ya bari ta d'anyi nisa kafinnan yace da bawan nashi su bita,tana tafe tana tsoron kar wani ya biyota kamar sauran ranakun amma sae taji shiru yau babu me binta dan haka ta saki jikinta tayi ta tafiyar ta har ta iso wajen,suka gaisa da Mud'allib sannan ta sanarda shi yadda sukayi da Sarki jiya,shikuma dajin haka sae yace "abunda za'ayi ina kince Jaheed d'in na jin maganar ki?",tace "eh",yace "toh ko zaki gwada mishi maganar shiga musulunci ko Allah zaesa ya karb'a kinga kin kub'utar da abu biyu,na farko zae musulunta kuma zae musuluntar sannan na biyu kin kare sarautar garinku dan zaeyi mulki neh bisa tafarkin addinin musulunci",tace "wannan gaskiya ceh amma ina tsoron mahaifiyar shi dan ta wuce inda kke tsammani,ina...."bata qarasa ba taji mutum a kansu,da juyawar ta sae sukayi ido hud'u da Jaheed....... Mu had'u a littafi na uku dan jin yadda zasu qare!!,taku har kullum Hamagee. ©Hama G Muh'd
Home »
» MAFARKIN HAMA (PART 2)
No comments:
Post a Comment