This site offers you with different novels series from one writer, I hope this will educate and as well as entertain you..

LAIFIN WAYE? (Page 71)

💦 💦💦💦 💦
*LAIFIN WAYE??*
💦💦💦 💦💦💦

_Written by the Aplomb writer: *Hamagee*_

*In devotion to Maman Saif*
💦

Wattpad @ Hama_gee

Page 71 💦💦

   Bai jira su ba ya nemi taxi ya wuce gida kai tsaye,yana isa kuwa ya gabatar wa iyayen nasu da takardar. Hamdala sukayi da suka farga da wuri da aiki ya jiqa musu. Tambayar shi sukayi ina Fadeel d'in,yace musu yana zuwa sannan ya wuce ya fita. Sun jima suna juya maganar kafin daga bisani Baban yace zai je ya samu mahaifin ta anjima suyi magana dan wannan aure ba zai yiwu ba.

    Bayan tafiyar yayan Fadeel d'in sun jima a wajen kowa da irin tunanin da yakeyi. Daga qarshe dai ya d'auki Suhana ya mayar da ita gida sannan ya bata haquri kafin ya wuce ya tafi. Kai tsaye gida ya koma shima,nan mamansu ta sanarda shi duk abinda ke faruwa. Bai ji dad'in hakan ba sam dan harga Allah yana son Suhana,saidai duk yadda ya kai ga sonta ba zai yiwu ya gurb'anta rayuwar shi ba,shi kad'ai ya zauna yana tuno abubuwan da suka faru. A nan ya gano dalilin da yasa Suhana taqi amince mishi.

★★★
   Tunda Suhana ta koma gida take kuka,matar baffanta tayi-tayi da ita dan jin abinda ya faru amma taqi sanarda ita koma miye. Can Baffan ya dawo,shima yayi tambayar duniyar nan Amman taqi fad'i. Ana cikin hakan da yamma saiga su mahaifin Fadeel sunzo. Ba tareda b'ata lokaci ba sukayi sallama da Baffa ya fita yaje ya same su.

    Nan sukayi mishi bayanin komai,haquri ya shiga bayarwa dan shi ko kad'an bai san Suhana nada wata cuta ba ballantana ta HIV. Suka ce babu damuwa,daga bisani suka yi sallama tareda tafiya. Shikenan auren Suhana da Fadeel ya fasu,Allah ne ya taimake shi da yanzu ya zamo abin tausayi shima d'in.

    Idan ran Baffa yayi dubu to duka sun b'aci dan a ganin shi wannan abinda ya farun ba qaramin zubar mishi da mutunci bane. Sanin irin b'acin ranshi yasa baima shiga gidan ba kai tsaye ya wuce gidan wata yayarsu,ita Daddyn Suhana ke bi. Ya sanarda ita duk abinda ke faruwa,ita ma tayi baqin ciki matuqa saidai babu yadda suka iya,in hanunka ya b'aci ai baka yankewa ka yar,inji ta kenan.

    Da qyar dai Baffa ya haqura dan acewar shi bazai zauna da Suhana ba saidai a san yadda za ayi da ita kawai. Anan yake yi mata tad'in akwai wani abokin shi da yake ce mishi yana sonta dama dashi yake shirin had'ata,ganin zuwan Fadeel ne yasa ya jinkirta maganar. Amma yanzu shima d'in dole ya sanarda shi gaskiya dan inya zo daga baya ya gano to abin ba zaiyi kyau ba.

    Bayan ya bar gidan kai tsaye gidan abokin nashi ya nufa,babu laifi abokin yana da d'an rufin asiri dai-dai gwargwado duk da ba wani babba bane a fannin kasuwancin amma asirin shi a rufe yake. Har cikin palourn shi suka shiga kafin suka gaisa,Alhj.Suhan Abdullahi sunan shi kenan,shima d'in a Kaduna take da zama kuma nan ne tushensa. Matarshi d'aya me suna Rabi'atu wacce Allah yayi wa rasuwa shekaru uku kenan da suka wuce. Yaransu biyar da ita,biyu maza sai uku mata,qaramar cikin yanzu tanada shekaru biyar kenan a duniya.

    Haj.Rabi'atu ta kasance nurse dake aiki a babban asibitin Kaduna wato T.H,wata rana tsautsayi ya afka mata garin yin allura ma wata patient, wanda wannan patient d'in na d'auke da cutar HIV. A lokacin bata sani ba sai daga baya wanda already mijinta ya d'auka a wajenta a wannan lokacin. Haka tayi ta jinya har Allah ya d'auki ranta,wannan abin yasa Alhj.Suhan kasa yin aure har yau,maganar Suhana ma da yayi wa Baffa a wasa yayi mata dan babu yadda zaiyi ya aureta shi yanada cuta.

     hghausanovelseries.blogspot.com

Share:

No comments:

Post a Comment

Popular Posts

Translate

Archive

featured post

UNIVERSITY GIRL Final episode(Chapter thirty)

Powered by Blogger.

Contact Form

Name

Email *

Message *

Blog Archive