This site offers you with different novels series from one writer, I hope this will educate and as well as entertain you..

MAFARKIN HAMA (PART 1)

[12:02pm, 12/9/2016] Hamagee馃尫: 馃崄馃尶馃崄馃尶
             *MAFARKIN HAMAGEE*
                  馃尶馃崄馃尶馃崄

Bismillahir Rahmanir Raheem,ina me miqa yabo da godiyata ga ubangijin daya bani ikon fara wannan littafi nawa lfya,sannan ina roqonshi daya bani ikon qarewa lfya馃檹馃徑ya kuma sa mu amfana da lttafin.
       *SHARHI*
Wannan littafi dae kamar yadda na fad'a it's base on *MY DREAM*,wani mafarki nayi wanda na jima ina jinsa a qwaqwalwata,shine nake son nayi amfani dashi don fad'akarwa da kuma nishad'antarwa,the only fiction kuwa shine sunayen wasu daga cikinsu saboda a mafarki ba kowa ne zaka iya recognising sunansa ba.Allah yasa mu dace....

庐WISDOM OFFICIAL WRITERS馃摑
    
    *_In devotion to Sis Feedy_*鉂�

Page 01
   Shekaru da dama da suka wuce,anyi wani sarki me suna *JAISUS*Jaisus nada mata biyu wanda yanxu haka uwar gidan sa nada ciki ya kai wata bakwae,sunanta *YAAYI*,sarki baya kulawa da ita kwata-kwata baya sonta baya son ganinta,kullum saeta sha baqinciki a gidan,ba wani abu bane kuma ya janyo hakan illa sab'awa umarninsa da tayi,yyi yyi da ita ta sallami wata hadimarta me suna *HAIMA* amma firr taqi,saboda yadda suka saba kuma a iya zamanta da hadimar bata tab'a bijire umarninta ba,suna matuqar son junansu,wannan dalilin yasa sarki Jaisus qara wani auren,wato amaryarsa ta yanxu me suna *WAHIYYA*,yana matuqar jida Wahiyya amarya sosae,bata ganin darajar Yaayi ko kad'an,itama ta tsani Haima wato hadimar uwargidan sarki Jaisus..
   Jaisus neh da Hawiyya zaune a wani d'aki (wajen shaqatawar sarki da iyalensa neh),sai surutai sukeyi ba kai bbu qafa,ga wani abu kamar tulu a gabansu da cup a hannun kowannen su,wannan abu kamar tulun kuwa cike yake da barasa (giya),sae sha sukeyi suna ihu da sheqa dariya,a wannan yanayin Yaayi tazo ta samesu,koda ta ga hakan saetayi qoqarin neman gun zama ta d'au kofi itama zata d'ebi barasar,kwatsam taji sarki Jaisus ya riqe mata hannu gam,ihu tayi wanda shiyasa shi sake hannun duk yyi zanen jaa dake Yaayi fara ceh tass,a fusace ya miqe ya jata zuwa waje ya wurga,duk abunda ake yinnan Wahiyya na zaune tana binsu da ido,bayan ya jefa ta waje sae ya dawo ya zauna bece ko uffan ba sae d'aukan kofinsa da yyi ya kamfato barasar cikin abu kamar tulun nan,ya kalli Wahiyya wacce itama shi d'in take kallo,suka kwashe da dariya dukansu..
   Yaayi kuwa da qyar da taimakon hadimarta data sa aka kira mata ta samu ta tashi,d'akinta ta maidata sannan ta shiga yi mata sannu,da qyar Yaayi keh iya amsawa hakanma da kai.Fifita Haima ta shiga yiwa Yaayi,a haka har bacci ya d'auketa.Sarki da amaryarsa kuwa bayan sun qare shan barasarsu agun suka kwanta sae barci,basu suka farka ba sae washegari da rana..
    Wata mata ceh zaune a tsakar gidanta tana tsince hatsi wanda bazan iya cewa ga sunan shi nan ba,tanayi tana y'an waqe waqenta sae wata yarinya y'ar kimanin 7-8yrs ta shigo gidan,talle ta kawo mata,bud'an bakinta tace "shegiya gajeriya me kamada kunkuru",sae ta sheqe mata da dariya,mijin matar neh ya fito daga d'akinsu ginin kara ya dubi matar yace "haba Niyad,wannan wane irin abune haka,kullum yaran mutane suka zo saekin samu abunda zaki zagesu dashi?hkan bashida kyau wllh",a fusace ta miqe tana nuna shi da yatsa tace"kai Ja'i,sanin kanka neh cewa ba'a jaa dani in bari saboda haka ka rufa mun baki ka kiyayen idan kana son zaman lfya a garin nan",Ja'i dake mugun shakkar Niyad ya jaa baki yyi gum ya koma d'aki inda ya fito,yarinyar kuwa da sauri ta tafi ta bar gidan dan tasan jarabar Niyad sarae..


漏Hama G Muh'd
[1:28am, 12/13/2016] Hamagee馃尫: 馃崄馃尶馃崄馃尶
          *MAFARKIN HAMAGEE*
                  馃尶馃崄馃尶馃崄

庐WISDOM OFFICIAL WRITERS 

*_In devotion to Sis Feedy_*鉂�



Page 02
   Komawa Niyad tayi ta zauna ta cigaba da aikin da take,sae faman mita take da zage-zage wae inba rashin mutunci ba meyasa za'a ringa aiko mata yara cikin gida suna zuwa mata rashin kunya,haka tayi ta mita kamar tab'abb'iya..

*Waye Niyad da Ja'i?*
Niyad da Ja'i dai mata da miji neh wa'inda tunda sukayi aure basu tab'a haihuwa ba,yanxu aurensu kimanin shekaru bakwae kenan kuma bbu ko b'ari,hakan yasa Niyad ta tsani ganin wani yaro ya rab'eta,da yara sunzo gidan sae zagi da hantara,gashi wani abun haushi tana son zagin halittar mutum dan kwae batada d'a.Har yau har gobe Niyad taqi yin tawakkali da rashin haihuwarsu,ga shegen kamanta mutum da kunkuru,daga tace baki kamar na kunkuru sae tace gajarta kamar kunkuru..
   Sarki Jaisus neh ya tashi a firgice yana kalle kalle kamar wanda ya warke daga makanta,can ya hango Wahiyya kwance tayi shame-shame a gurin kamar wacce bata san dad'in jikinta ba,tashi yyi ya je inda take kwancen ya tasheta wae safiya tayi,da qyar ta tashi ta je d'akinta inda ake ta mata gaisuwar ban girma duk inda ta wuce,hadimarta na gani ta soma binta tana mata kirari,wae "gimbiya takawarki lfya,y'ar sarki jikan sarki matar sarki kuma uwar sarki nan gaba",kan Wahiyya ya huru fam sae bunqasa takeyi kamar qosasshiyar giwa,da sauri *AINA* ta bud'e ma Wahiyya wani abu shi dae ba qofa za'ace ba ba kuma labule ba,ta shiga sannan tabi bayanta,da taimakon ta Wahiyya tayi wanka ta sauya kaya sannan ta sake gyara mata gashin kanta saeta kawo mata fruits a kwando,Yailahi! Ban tab'a ganin irin wainnan Apples da ayaban ba,da kankana,fresh neh sosae gasu manya manya (ko dan sune favorites d'ina oho)..
  Bayan Wahiyya ta gama cin fruits d'in though ba wani sosae taci ba dan su mafi yawancin abincinsu barasa ceh (Allah ya kyauta),Aina ceh tayi mata rakiya zuwa fadar sarki,bayan sun iso Sarki Jaisus da ganin Wahiyya ya soma murmushi harta qaraso kujerarta dake gefenshi ta zauna cikin tinqaho,fadawan dake gurin kuwa duk suka shiga aikin gaisuwa itako dad'i take ji idan ana mata wannan ladabin,Aina na bayanta tana mata fifita..
  Kullum Sarki Jaisus na tareda amaryarsa Wahiyya,ko kad'an baya waiwayar uwargidansa hasalima idan ta nemi tazo inda suke,wulaqntata yake a gaban mutane bbu ruwansa,wannan dalilin neh ma ya sanya yanxu bata zuwa wajen su..

Bayan wata biyu..
  Yaayi ceh ke kwance tanata murqususu a qasa,Haima da wata tsohuwa na kanta suna tayi mata sannu,da gani haiwuwa ceh tazo mata,tsohuwar dake kanta kuwa zai wani abu take ta d'irka mata tana wasu maganganunta,can Yaayi ta haifo y'arta fara sol,wannan tsohuwar da Haima neh suka gyara Yaayi da y'arta,sae suka gyara wajen suka wanke kayan tass suka shanya,tsohuwar da knta taje ta sanarwa sarki cewa matarsa ta haihu,ko a jikin Sarki,bece komai ba haka tsohuwarnan ta tashi ta tafi,koda ta dawo gun Yaayi bata fad'a mata cewa sarki beyi murnan haihuwarta ba,haka ta cigaba da kulawa da Yaayi da y'arta har sukayi arba'in,Yaayi ceh tayi ma y'ar suna dan su a al'adarsu haka sukeyi,sunan y'ar *ZEEDAT*,Yaayi naji da y'arta sosae,haka rayuwarsu ta cigaba bbu kulawar sarki....


漏Hama G Muh'd
[10:21am, 12/13/2016] Hamagee馃尫: 馃崄馃尶馃崄馃尶
          *MAFARKIN HAMAGEE*
                  馃尶馃崄馃尶馃崄

庐WISDOM OFFICIAL WRITERS 

*_In devotion to Sis Feedy_*鉂�



Page 03
   Haima ceh tazo wucewa kwae saetaci karo da Aina,Aina ta fad'i a qasa,a razane Haima ta soma bata hauri kan bada saninta bane tayi haquri,Aina ta miqe a fusace ta kwashe Haima da mari,sannan ta soma zaginta "shegiya tsinanniya,mayya to baki isa ka kasheni ba in fad'a miki kinyi kad'an,kuma ki shirya fuskntar hukuncin sarki a kanki tunda kka bugeni na fad'i",Bbu irin haqurin da Haima bata bama Aina ba amma sam bata jiba saeda taje ta had'a munafinci agun sarki,shikuma be tsaya yabi kam maganar ba kwae yace ayi masa kiran Haima,bayan Aina tabar wajen sae Haima taje ta fad'awa Yaayi abunda ya faru,ana cikin haka wani bafade ya shigo yace sarki yana magana da Haima,gabansu ya fad'i barinma Yaayi,amma bbu yadda suka iya haka aka tafi da Haima,hukuncin da sarki ya yanke mata kuwa shine ta kwanta Aina tabi ta kanta har sau goma,karku manta fa Aina tafi Haima da komai,girma,tsayi,nauyi,shekaru duka tafi ta amma ba yadda zatayi dan sarki baya sake magana idan yyi ta.Haka bbu imani Aina tayi ta bin ta kan Haima har sau goma,da qyar da taimakon mutane Haima ta tashi aka rakata wajen Yaayi,koda Yaayi ta ganta kuka kwae ta fara yi,nan bayin nan da suka kawo Haima suka bamasu Yaayi da wancar tsohuwar labarin abunda ya faru tass,tsohuwar tace karta damu Haima zata samu lfya dama ita kamar likita ceh a garin..
   Niyad ceh kwance a tsakar gidanta ta jiyo ihun yara a qofar gida,daga ji dae fad'a suke ko wasan banza,ran Niyad yyi mugun b'aci ace a rasa inda yara zasuzo suna iskanci sae qofar gidanta,da hanzari ta tashi ta fita,ai kuwa fad'an ta iskesu sunayi dan haka ta cakwamo su ta wurga cikin gidanta,ta dawo ta rufe qofa,banda had'iyan yawu bbu abunda yaran nan keyi dan sun san yau kashinsu ya bushe a hannun Niyad,nadamar zuwansu qofar gidan suka soma yi gashi dae yara neh amma sun san nadama,Niyad ta karyo wani qaton kara ta nufosu,dukansu ta shigayi saeda taji ta gaji gashi karan duk ya karkarye a jkinsu,yaran duk sun galabaita ta bud'e musu qofar suka fice a guje kamar basu aka gama jibga yanxunnan ba,Niyad ceh tayi dariya tace "shegun yara masu kamada kunkuru,ga yadda suke tiqan gudu kamar kunkurai",ta sake sheqewa da dariya kamar wacce ta zauce,Niyad kenan sae Allah ya shirya..
   *Gidan Sarki*,
  Wahiyyace kwance duk a galabaice,yau tunda ta tashi take ta amai,yanxunma aman neh yazo mata da sauri ta tashi tayi waje Aina na biyeda ita tana mata sannu,amai ta shiga kwararawa kamar zata fitoda hanjin cikinta,duk ta sauya kama ta rame,bayan ta gama da taimakon Aina ta wanke jikinta sannan ta koma d'akin,Aina ce tasa akayi mata kiran Sarki,bayan yazo yaga yanayin da Wahiyya take ciki sae Aina tayi masa bayanin komai,Lkita yasa akayi masa kira,bayan tazo ta duba Wahiyya da kyau sannan ta sanarda sarki sakamakon rashin lafiyar matarshi..

漏Hama G Muh'd
[10:22am, 12/13/2016] Hamagee馃尫: 馃崄馃尶馃崄馃尶
          *MAFARKIN HAMAGEE*
                  馃尶馃崄馃尶馃崄

庐WISDOM OFFICIAL WRITERS 

*_In devotion to Sis Feedy_*鉂�



Page 04
  Sakamakon kuwa shine Wahiyya na d'aukeda ciki harna wata biyu, murna wajen Sarki kuwa ba'a magana dan har liyafa ya had'a na murnar samun cikin Wahiyya,anci naman dabbobi ansha barasa kamar ba gobe,duk sun bugu kamar tab'abb'u sae ihu sukeyi..
   Har yau Sarki Jaisus be tab'a sa Zeedat a idonsa ba,yarinyar harta d'an fara wayo gata kyakyawa ta qarshe,har yau har gobe kuma wannan tsohuwar likitan tana zuwa duba Yaayi da y'arta kusan kullum dan ganin yaya lfyarsu take tareda tausan Yaayi kan abunda sarki ke yimata,Yaayi kuwa cewa take bbu komai ze wuce watarana.
  Bayan an gama liyafa kowa yyi tatur da barasa da qyar sarki ya iya dawowa gida shida Wahiyya,amma ita bata sha barasar ba saboda wancan taohuwar likitar tace ba'a so me ciki tana shan abun wae zae iya lalata cikin,gashi Sarki da Wahiyya na mugun son cikinnan kamar a haifeshi yau sukeji,suna shigowa d'akin Sarki ya zube kamar an sauqe kayan trailer tsabar irin yadda ya zube a qasa kamar asara,a haka nannauyan barci yyi gaba dashi,ita kuma Wahiyya ta d'an jima kafin tayi bacci duk ta gaji.Sauran mutanen kuwa duk agun suka zube suka shiga sharara barci kamar kasa,da asuba wasu suka shigo gidan sarki dan satar abinci saboda tsanin yunwa da sukeyi,wae a garin idan anyi noma rabinsa wa sarki ake kaiwa rabin kuma shine na mutum kuma dududu abinda suke nomewa befi buhu biyu zuwa uku ba  shekara so baya isarsu da iyalansu,koda sukaga fadawa kowa yyi barci kwae sae suka shiga suka d'iba iya d'ibarsu suka gudu,kowa ya nemi wajenda zae b'oye nasa yadda ko anzo bincike baza'a samu ba..
   Saeda rana ta fito rau a sama kafin fadawan nan suka tashi,koda d'ayansu kuwa yazo ta wurin ma'ajiyar abincinsu sae yaga an zuzzubar a qasa kuma ba haka aka rufe qofarba da dan haka sae yyi sauri ya janyo hankulan sauran zuwa wajen ya nuna musu,cikin kowannensu ya shiga qara dan sun tabbatar yau akwae daru da Sarki kuma wasu zae bama laifin zaece meyasa sukayi bacci har hakan ta faru.D'aya daga cikinsu neh yyi azamar bud'e qofar,yana jaa kuwa ta bud'e alhalin da sai mutane biyu zuwa uku sunji jiki kafin qofar take bud'ewa amma sae gashi yanxu mutum d'aya be sha wahala ba ta bud'u dan haka suka sake tabbatarwa anshiga d'akinnan da dare,koda suka leqa ciki sunga abincin yyi mugun raguwa,zufa kowannensu ya shiga sharewa bayan lokacin sanyi neh,haka suka tattara wanda ya zuzzuba suka had'a tareda refe d'akin sunata zullumin abunda yau zae faru idan sarki yazo yaga abincin haka bayan wancan satin dayazo yaga yawan abincin kuma baci sukeyi ba balle yace ko anci a gidan,daman sayarwa yakeyi ma garuruwan makwabtansu,kuma tun wancen satin daya wuce bbu wanda aka siyarma abincin kuma tabbas yau zaezo dubawa dan dama kowane qarshen sati yakan zaga gidan yaga meke wakana ciki kuwa harda d'akin abincin nan..

漏Hama G Muh'd
[11:21am, 12/13/2016] Hamagee馃尫: 馃崄馃尶馃崄馃尶
          *MAFARKIN HAMAGEE*
                  馃尶馃崄馃尶馃崄

庐WISDOM OFFICIAL WRITERS 

*_In devotion to Sis Feedy_*鉂�



Page 05
    Sae kusan yamma sarki ya fito zaga gida dan be tashi da wuri ba,aikuwa yana zuwa d'akin abincin nan qirjin su ya fara bugu da qarfi,sunyi sunyi su tuno dabarar da zasuyi kar sarki ya duba d'akin nan amma ina basu tuno ba dan haka kwae suka sadaqar,ana bud'ewa Sarki yaga d'akin duk a rame bbu kayan abinci,ya juyo ya kallesu sukuma suka sunkuyar da kai dan dokace duk wanda ya kalli idon sarki akwae hukunci me tsanani akansa,Sarki Jaisus yace "munyi baqi masu siyen abinci neh?",shiru sukayi bbu wanda yace qala sae b'ari da sukeyi,Sarki da ranshi ya fara b'aci ya daka musu tsawanda saeda suka ji kamar su nitse tsabagen tsoro,"ba magana nakeyi ba neh?",d'aya daga cikin fadwan yayi qarfin hali ya ceh "ran Sarki ya dad'e bbu wanda yazo ya siya abinci,muma tashin mu mukaga abun haka,na tabbatar shigowa akayi da dare aka sace saboda nauyin baccin da mukayi",ran Sarki ya sake baci,a fusace yace "wane irin barcine kuke yi da har a shigo ayi min sata baku ji ba?",kowannensu ya shiga cewa "ran sarki ya huce,ranshi ya kuma dad'e",wani bafaden yace "ran sarki ya jima barasar da muka sha jiya ceh tasamu wannan barcin amma tubanka muke nema ya me komi",Sarki yace "yafiyata kenan aje a nemo min wanda ya saci abincin nan,idan kuma ba haka ba zaku fuskanci fushina ba kad'an ba",kowannen su ya yarda da hakan,Sarki ya bar wajen tareda wasu mutanensa,aka bar wainnan fadawan da tunanin yadda zasu b'ullowa lamarin,daga qarshe dae suka yanke shawarar bi gida-gida dan yin bincike,suka raba kansu kashi-kashi,wasu suyi nan wasu suyi can,haka sukayita bincike gida-gida amma har dare basu gano ko gida d'aya ba,dan haka suka rasa yadda zasu tunkari sarki da wannan maganar..
   Qarshe dai gidan suka koma suka sanarda sarki cewa sun fara bincike kuma gobe zasu gama zasu kawo mishi wanda yyi wannan aika-aikan,sarki ya barsu akan goben amma yace indae zuwa gobe basu kawo mishi wani bayanin ba to tabbas zasu fuskanci hukuncin shi,sukayi godia sannan suka tashi jiki bbu qwari suka fita..

漏Hama G Muh'd
[10:10am, 12/16/2016] Hamagee馃尫: 馃崄馃尶馃崄馃尶
          *MAFARKIN HAMAGEE*
                  馃尶馃崄馃尶馃崄

庐WISDOM OFFICIAL WRITERS 

*_In devotion to Sis Feedy_*鉂�



Page 06
   Suna fitowa suka d'anyi tafiya can bayan sunsha wata kwana sae suka zuba a wajen kamar asara,kowa tunanin mafita yake dan lallae idan zuwa gobe basu kaima sarki wani bayani ba to lallai zasu fuskanci hukun shi,ana cikin haka d'aya daga cikinsu yyi zumbur ya miqe yana cewa "na samo mafita,kuu na samo mana mafita",dukansu suka fara tambayarsa "wace mafita kenan?",yace "kun san ni gwani neh wajen iya gano shatin takalmi koh",suka d'aga kawunansu alamar eh suna dad'a zuba masa ido,yace "yace kuma ina iya gane takun da akyishi yau da jiya,saboda haka me laifin na duba mana shatin,takalman jiya zuwa yau,kunga idan kowa a cikinmu ya tantance nashi sannan muka tantance na Sarki,toh tabbas sauran na b'arawon Sarki neh tunda bbu masu wucewa tanan inba mu ba",wani ihu suka kurma dukaninsu suna cewa "sae kai",haka suka tashi suka d'unguma wajen dukansu,biyu daga cikinsu suka nemo takarta da al'qalamin rubutu suka kawo,ta gefe ya nuna musu suka tsaya dukansu,d'aya bayan d'aya yabi kan shatin takalman nan ya zanasu,kowannensu ya nuna nashi shatin sannan suka nuna na Sarki,sauran guda uku wanda basu samu meshi ba dan haka suka yanke hukuncin zuwa gidaje-gidaje suna duba me irin wannan zanen takalmin.Yanzu ma kamar d'azu,suka raba kansu kashi-kashi,way'annan suyi nan way'ancan suyi can,kowa ya bazama nema bayan kowane tawaga an basu irin zanen takalman da ake nema,a cikin tawagar nan kuwa wasu sun sami d'aya daga cikin zanen takalman yyi iri d'aya da takalmin wani mutumi dan haka suka jashi suka tafi dashi,koda suka had'u da sauran suma sun samu zane d'aya da yyi kama dana wani mutum,dukda dae basu samu na duka zanen ba,amma sun rage hanya tunda sun samu mutum har biyu,kuma su mutane biyunnan zasu iya fad'an sauran b'arayin.
   Haka suka ja mutane biyunnan zuwa fada,suka kullesu a wani d'akin hora masu laifi,suka fito suka je suka kwanta bayan sun bar wanda zena gadin su,a haka har gari ya waye musu,da safe bayan sarki yazo fada saeya sa amasa kiran way'annan fadawa masu gadin gidan,suna zuwa suka fad'i qasa suna masu miqa gaisuwa ga Sarki Jaisus,sarki yace "ina fatan kun cika umarnina?",d'aya daga cikin fadawannan yace "ran sarki ya jima,ae bbu wanda isa jinkirin cika umarnin ka,tabbas mun nemo b'arayinka a halin yanxu ma muna kulle dasu",sarki yyi wani dariyar qeta sai yace da wani bafaden aje azo masa dasu,haka bafaden nan ya tashi yaje inda aka kulle mutanen nan,yana zuwa yyi wata magana da me gadin wajen yace dashi sarki neh ya aiko shi yazo ya tafi dasu,bbu b'ata lokaci megadin yaje ya bud'e su ya taho dasu ya damqa ma wannan bafaden,bafaden ya riqesu sae ya sasu a gaba ya soma tafiya dasu zuwa fadan Sarki..
    Niyad ceh tafe da wata qatuwar jaka zata kasuwa,ko meh zata siyo haka ohonta! Tazo daedae wani gida sae taci karo da wasu yara y'an mata su hud'u sunata carafke,da ganinsu saeta fara zaginsu kamar aiko ta akayi..

漏Hama G Muh'd
[11:48am, 12/17/2016] Hamagee馃尫: 馃崄馃尶馃崄馃尶
          *MAFARKIN HAMAGEE*
                  馃尶馃崄馃尶馃崄

庐WISDOM OFFICIAL WRITERS 

*_In devotion to Sis Feedy_*鉂�



Page 07
   "Shegu masu hana ayi ruwan sama,da shegen baqaqun qafafuwan ku kamar na kunkuru,ga guntancin tsiya sae shegen rashin mutuncin tsiya,idan baku tashi anan ba saena karkarya ku",da gudu yaran nan suka miqe suka shiga gida,Niyad kuwa ta kama hanya tayi tafiyar ta tana ta faman zage-zagen ta. 
   Bafaden nan da Sarki ya aika ya kawo masu laifin nan neh ya shigo dasu,wurgasu qasa yyi saeya sunkuya ya gaida sarki yace "ranka ya dad'e,ga b'arayinka nan a gabanka",mutanen nan suka gaida sarki,sarki yace "kune kuka saci abincin sarki kou?",kowannensu ya kalli d'an uwanshi sai d'aya yace "ran me martaba ya dad'e mune amma bamu kad'ae ba",Sarki ya dube su yace "ku dawa ye?",sae mutumin ya shiga lissafo sunayen su,da sarki yaji haka sae yace lallae yaje ya nuna ma fadawan shi suzo dasu gaban shi,hakan kuwa akayi uku daga cikin fadawan sarki suka sa mutumin nan a gaba zuwa kamo barayin sarki.Koda suka jesu gidajen basusha wuya ba suka kamo b'arayin d'aya bayan d'aya, har gaban sarki suka je,b'arayin sun kai su goma duk aka sa sukayi layi a gaban sarki,Sarki ya d'ago ya qare musu kallo d'aya bayan d'aya sannan yace "kune b'arayin da kuka sace mun abinci kou?",kowannen su bece qala ba,sae wani bafade yace "wae bada ku sarki ke magana bane?"ranshi a b'ace yyi maganar,sae kuma ya jyo yana kallon sarkin yace "ran sarki ya jima ko tantama bbu,way'an nan sune b'arayinka",Sarki yyi gyaran murya sae ya ceh "lallae zaku fuskanci hukunci nah me tsanani",d'aya daga cikin b'arayin nan yace "ranka shi dad'e ayi mana afuwa mana,ba laifin me bane yunwa ceh tasa mu yin hakan,amma tuba muke yi",wani bafade neh ya buge bakinsa yace "ko kunya baka ji ba,har ka kalli idon sarki kace yyi haquri bayan wannan mumunan laifin da kuka aikata?",ya juya ya kalli sarki yace "ran Sarki ya jima hukuncin ka kwae suke jira",sarki yace "hukun da na yanke shine,aje a d'ebo mun dukkanin iyalanku wato matanku da y'ay'anku,ni nasan yadda zanyi dasu,ku kuma za'a fille muku kai"..

漏Hama G Muh'd
[11:49am, 12/17/2016] Hamagee馃尫: 馃崄馃尶馃崄馃尶
          *MAFARKIN HAMAGEE*
                  馃尶馃崄馃尶馃崄

庐WISDOM OFFICIAL WRITERS 

*_In devotion to Sis Feedy_*鉂�



Page 08
   Gaban b'arayin nan ya soma fad'uwa dan sun san maganar sarki dutse neh,baya magana ya sauya ta,haka sarki yasa aka kwaso dukkanin iyalan b'arayinnan sannan aka filewa mazajen kai a gaban su,masu kuka nayi masu suma sunayi, bayan an gama sarki yace matayen sun zamo bayinsa haka nan yaran kuma za'a sayar dasu a matsayin bayi,tashin hankali suka shiga ba kad'an ba,lallae Sarki Jaisus da fadawan sa sun cika azzalumai na qin qarawa..

鈽呪槄鈽呪槄鈽呪槄鈽呪槄鈽呪槄鈽呪槄鈽�
Bayan wata takwas...
   Sarki da Wahiyya na zaune a d'akin hutawa sae Wahiyya tace mishi cikin ta na mata ciwo,da gaggawa yasa aka kira mishi likitan su,tana zuwa data duba ta sae tace ae haihuwa ceh tazo mata,da gaggawa aka maida ita wani d'aki inda anan ta sauqa lafiya,ta haifo d'anta namiji me kamada sarki Jaisus,nan da nan fada ya amsa ai matar sarki ta haifi d'a namiji me kama da sarki,koda zancen ya isa kunnen Sarki,yyi matuqar farin ciki ya samu me gadan sa,so da qaunar Wahiyya ya ninku a zuciyar shi,ya taso yazo d'akin Wahiyya dan ganin babyn shi,a kwance ya sameta d'an na gefenta da alamu barci yakeyi,ya qaraso inda take yyi mata sannu,bata ceh komai ba sai d'aga kai da tayi alamar yauda,ya d'au yaron yana kallo,wani sonshi neh ke ratsa shi ganin yadda yake kama dashi tun a jaririnsa ma kenan,bayan ya gama kallon yaron saeya kwantar da shi a gefen uwar sannan ya kwanta ta gefe shima.
   Yaayi ceh zaune da Haima a gefenta tana bata labarai,Yaayi ko sae dariya take dan labarin abun dariya take bata,Zeedat ceh ta shigo d'akin da gudu tana kiran mamanta,wae taga tsutsa shine take wannan ihun,da maganarta ta yara tace mama tsutsa,tanayi tana haqi,yarinya ceh y'ar kimanin shekara d'aya da watanni goma amma ta iya tafita ga kaifin tunani,tana da matuqar hankali da fahimtar abu.Yaayi tayi dariya tace "haba zeedat,ma tsutsa kke wannan ihun kamar kinga kura?",yarinyar tayi dariya kamar ta fahimci me uwar ta fad'i,Haima tajaa ta ta zaunar sae ta cigaba da musu labaran tare suna dariya..

漏Hama G Muh'd
[11:50am, 12/17/2016] Hamagee馃尫: 馃崄馃尶馃崄馃尶
          *MAFARKIN HAMAGEE*
                  馃尶馃崄馃尶馃崄

庐WISDOM OFFICIAL WRITERS 

*_In devotion to Sis Feedy_*鉂�



Page 09
   Koda labarin cewa Wahiyya ta haihu kuma d'a namiji neh yazo kunnen su Yaayi,Yaayi bata damu ba ko irin jin kishin ita ta haifi mace wancan kuma ta haifi namijin nan batayi ba,ita dae kwae fatanta shine y'arta ta taso da irin wannan halin nata kuma sarki ya gano kuskurensa.
   Washegari aka rad'a ma yaro suna *JAHEED*,anci ansha kamar ba gobe,tun safe ake d'aya har dare kafin aka gama,duk wani mutum a garin ya halacci wannan taron kuma kowa yaci ya qoshi har ya bar abinci.

掳掳掳掳掳掳掳掳掳掳掳掳掳掳掳掳掳掳掳掳掳掳掳掳掳
Bayan kwana biyu..
   Sarki da Wahiyya na zaune a fadar Sarki tareda fadawan sarki,fadawan sunata musu kirari su kuma suna jin dad'i,can saega Zeedat ta shigo da wata hadimar data rakota,hadimar ta tsuguna ta gaida Sarki sannan ta sanarda shi dalilin zuwansu "ran Sarki ya dad'e,babbar y'arka ceh ta matsa tace sae an kawota gun baban ta toh shine na kawo ta",lallae dama haka yarinyar take da kyau,sarkine ke ayyana hakan a ranshi dan yarinyar ta tafi dashi,kamarta d'aya da uwarta,wani irin hararar da Wahiyya tayi mishi neh yasa yace da hadimar ya tafi da yarinyar baya son ganinta.Bada son ranshi yasa aka fitar da yarinyar ba,tana kallonshi shima yana kallonta haka hadimar nan ta d'auketa tayi waje da ita,Sarki beji dad'i ba kwata-kwata amma beko nuna hakan ba sae ma sawa da yyi fadawan suka cigaba da hirar da suke musu,Wahiyya kuwa dad'i taji a ranta ganin yadda Sarkin ya nuna yarinyar bata dame shi ba.
   Koda hadimar ta d'auki Zeedat wajen Yaayi ta kaita ta kuma sanar da ita yadda sukayi a gaban sarki,da irin abunda ya nuna musu,ko a jikin Yaayi tace "koma miye dae shine ubanta ba'a canza ma miya suna dan haka ko ba dad'e ko ba jima sae yazo yyi alfahari da ita dan Zeedat ba qaramin baiwa ceh da ita ba",Haima ceh tayi ta kwantar masu da hankali har suka mance sukayi ta nishad'in su..


漏Hama G Muh'd
[8:08am, 1/1/2017] Hamagee馃尫: 馃崄馃尶馃崄馃尶
          *MAFARKIN HAMAGEE*
                  馃尶馃崄馃尶馃崄

庐WISDOM OFFICIAL WRITERS 

*_In devotion to Sis Feedy_*鉂�



Page 010
   Yau ma kamar kullum Haima na zaune da Zeedat tana mata wasa,Yaayi kuwa tuni tayi bacci.Bayan d'an wani lokaci Zeedat ta tashi ta fita waje,bata tsaya ko'ina ba sae sashen su Jaheed,tsayawa tayi cak ganin kallon da Wahiyya da Aina keyi mata,Zeedat yarinya ceh qarama amma tasan abunda ake nufi da wasa da kuma rashin sa,kafin Wahiyya ta bud'i baki sae Zeedat tayi saurin cewa "sannu da hutawa ranki shi dad'e",kamar Wahiyya bata ji abunda ta fad'i ba tayi gumm..
   Ta kai kamar mintuna 2 zuwa 3 tana hararan Zeedat kafin tace "me ya kawo ki sashe nah?"fuska a d'aure,wani gajeren fitsari Zeedat taji yana shirin fito mata da qyar ta riqe shi tsaban tsoron Wahiyya da ta ji,bata iya ansa tambayar ta ba a maimakon hakan saeta tsura mata idanu,a fusace Wahiyya tayi mata magana wanda yafi na farkon tsawa tace "ba tambayar ki nake bane?",Zeedat tayi maza tace "ranki shi dad'e nazo wajen qanina neh muyi wasa"cikin muryar kuka tayi maganar,Wahiyya tace "to dama ae ko baki fad'i ba raena zae dad'e dan nafi qarfinku kiji in gaya miki daga keh har uwartaki a tafin hannuna kuke,sannan kuma waye qaninki anan?",Zeedat ansa "Jaheed",Wahiyya ceh tayi maza ta miqe tana fad'in "kambuuu,Jaheed d'inne qanin naki? To koda wasa ban yarda ba shegiya mayya me halin uwarta",hawayen da Zeedat ke maqale dasu suka soma zubowa,Wahiyya ta qaraso inda take taja hannunta tayi waje da ita ta wurga kamar kayan wanki..


漏Hama G Muh'd
[8:09am, 1/1/2017] Hamagee馃尫: 馃崄馃尶馃崄馃尶
          *MAFARKIN HAMAGEE*
                          馃尶馃崄馃尶馃崄

庐WISDOM OFFICIAL WRITERS 


*_In devotion to Sis Feedy_*鉂�



Page 011 
   Zeedat ta kai 30mins a wajen tana kuka,can saega Jaheed ya zago ta gurin,tsayawa yyi cak ganin Zeedat a yashe tana kuka duk jikinta ya b'aci da qasa,ya qaraso wajen duk jikinshi bbu qarfi ya shiga lallamnta yana tambayar wanda yasa kuka,kamar a sama Wahiyya ta fito ta tsaya a kansu,da sauri taja Jaheed a jikin Zeedat tana ta faman huci tana zagin Zeedat wae mayya wato saeda ta lallab'a tasan yadda tayi taja mata d'a,to idan ta fito ta sameta agun saeta karya qafarta,taja hannun Jaheed tayi ciki dashi tabar Zeedat agun tana ta kuka abun tausayi.
   Da sauri Zeedat ta tashi ta nufa sashen su dan sarae tasan idan har Wahiyya ta fito ta sameta to lallae kashinta saeya bushe,koda ta fad'a ma mamarta,batace komai ba sae cewa da tayi tai haquri.
   Wahiyya ceh ta fito,ganin Zeedat bata gurin yasa tayi qwafa ta shige ciki tana mita,taje ta samu Jaheed yana ta kuka saeta shiga lallaminshi,da qyar yayi shiru Aina tana mishi wasa.Bayan wani lokaci,Sarki ya shigo cikin gida sae yake tambayar Wahiyya meya samu magajin sa dan yaga alamun yyi kuka dukda bacci yakeyi,nan Wahiyya ta fad'a mai qarya da gaskiya,abunda akayi dama wanda ba'a yi ba,ranshi yyi matuqar baci yace "lallae yau zan koya ma Yaayi da y'arta hankali,zan gwada musu ba'a tab'a magajin sarki a kwana lfya",yyi zumbur ya miqe ya fito waje yana neman bafaden dake gadin wajen.
   Fadwa sun kai suu hud'u way'inda suka zo suka durqusa gabansa suna gaisuwa,be ansa wa koda d'ayansu ba sae umarni daya bama d'aya daga cikin su na cewa aje azo mishi da Yaayi da y'arta,bbu b'ata lokaci ya miqe yana fad'in "maganar Sarki dutse neh,yanzu yanzunnan za'a kawo maka su,ran Sarki ya huce",yyi wuuf ya miqe da hanzari ya nufa sashen Yaayi dan cika umarnin Sarki..


漏Hama G Muh'd
[7:56pm, 1/1/2017] Hamagee馃尫: 馃崄馃尶馃崄馃尶
          *MAFARKIN HAMAGEE*
                  馃尶馃崄馃尶馃崄

庐WISDOM OFFICIAL WRITERS 

*_In devotion to Sis Feedy_*鉂�



Page 012
   Yaayi na kwance Zeedat na gefenta tana bacci inda ta gama kukan ta  a gurin tayi bacci,maganar bafaden nan neh ya tashi Yaayi gashi lokacin Haima bata nan ta barsu suyi bacci neh,haka Yaayi ta tashi taje ta duba,koda taje saeta bafaden nan ya sanarda ita abunda sarki ya aiko shi yyi,bbu musu Yaayi tace "ba komai barin d'auko Zeedat d'in muje",yace "toh ranki shi dad'e".Ta juya kenan saega Haima ta dawo Yaayi tace "yauwa gara da kka dawo yanzu,muje ciki".
   Haima tasha jinin jikinta amma bata ceh komai ba sae bin Yaayi da tayi suka shiga ciki,nan Yaayi ta sanarda ita abunda ke tafe da wancen bafaden,Haima tayi mamakin dalilin kiransu da sarki yyi amma sae Yaayi tace mata ba abun mamaki bane dama tasan dole Wahiyya sae tayi musu wani munafincin agun sarki,Haima ta tausaya mata sosae amma bbu yadda suka iya haka Haima ta d'auka mata Zeedat sannan suka fito dan zuwa kiran da Sarki yyi musu..
   Suna tafe bafaden nan na biye dasu har zuwa sashen Wahiyya,bayan sun isa sae Yaayi tace da Haima ta bar wajen kar ya had'a da ita in ya ganta.Haima taqi tafiya wae koma miye yyi musu tare dan bazata iya tafiya ta barsu a haka ba,da qyar Yaayi tashawo kan Haima har ta yadda ta bar wajen..


漏Hama G Muh'd
[8:00pm, 1/1/2017] Hamagee馃尫: 馃崄馃尶馃崄馃尶
          *MAFARKIN HAMAGEE*
                  馃尶馃崄馃尶馃崄

庐WISDOM OFFICIAL WRITERS 

*_In devotion to Sis Feedy_*鉂�



Page 013
   Bayan Haima ta bar wajen neh bafaden nan yyi magana da Sarki ya sanarda shi ya kawo su,bbu jimawa Sarki ya fito ya nufa fadan shi sannan yace da bafaden ya kawo mishi su,bbu b'ata lokaci bafaden nan ya sasu gaba yana biye dasu har fadan Sarki,bayan sun gama settling sae Sarki yyi gyaran murya sannan ya fara magana kamar haka "dalilin kiran ku dana sa akayi ba wani abu bane illa zantar da hukunci akan ku gwargwadon laifin da kuka aikata keh da kuma y'arki wanda ba saena wani b'ata lokaci nah wajen tunasar daku ba saboda ku kunfi kowa sanin laifinku",Wahiyya ceh ta shigo tana wata bunqasa tana jin kai,tazo kujerar dake gefen ta Sarki sae ta zauna tana wani shagwab'a irin ta makircin nan,Sarki kuwa tunda ta shigo yake wani kallonta yana murmushi kamar bazawarin da yyi kwantai ya samu mata.
   Bayan ta gama zama sae Sarki ya juyo ya cigaba da cewa "yanxu hukuncin dana yanke shine zaku kwana a d'aya daga cikin d'akunan horo (prison),sannan kuma sae an dubi d'aki mafi sauro da kuma duhu saboda ku ladabtu da kyau",ya juya ya kalli Wahiyya wadda itama shi take kallo tuntuni yace "wannan hukuncin yyi?",Wahiyya ta washe baki tace "wannan yyi,hukuncin ka wuqa me martaba"ta qarasa maganar tana sunkiye da kai alamar girmamawa,Sarki kuwa yaji dad'i ganin ya burge Wahiyya dan bashi da wani buri illa yaga yasa ta farin ciki ita da d'anta a kullum..


漏Hama G muh'd
[8:04pm, 1/1/2017] Hamagee馃尫: 馃崄馃尶馃崄馃尶
          *MAFARKIN HAMAGEE*
                  馃尶馃崄馃尶馃崄

庐WISDOM OFFICIAL WRITERS 

*_In devotion to Sis Feedy_*鉂�



Page 014
   Ba tareda wani b'ata lokaci ba aka kira bafade me kula da gidan yari (prison) yazo ya tafi dasu Yaayi dan cika umarnin sarki,bayan ya rufe su saeya dawo yazo ya sanar da Sarki cewa ya cika umarnin sa,Sarki yace mishi yyi kyau,Wahiyya ta kalle shi tace "kada a sake a basu abinci har sae an fitar dasu daga d'akin",bafaden nan ya ansa mata cikin girmamawa saeya fice,Sarki da Wahiyya suka tashi suka nufa cikin gida inda fadawa suka rufa musu baya.
    Bayan bafaden nan ya bar wajen bbu abunda Zeedat keyi illa kuka mamanta na rarrashin ta tana bata baki kan tayi haquri zaman kwana d'aya zasuyi kawae,Zeedat yarinya y'ar kimanin shekaru 8 da wani abune amma tasan cewa masu laifi ake kawowa nan wajen kuma a iya saninta bbu laifin da sukayi amma bbu yadda suka iya dole su kwana a wannan d'akin dukda darajarsu da martabar su. 
   Da yamma lis Zeedat ta tashi daga bacci tana jin yunwa dan yau bata wani ci abun kirki ba,bata sanarda mamanta ba saboda bata son tashin hankalinta dan tasan cewa bbu abinci a halin yanxu,saedae tsakanin d'a da uwa ya wuce wasa Yaayi ta fahimci Zeedat najin yunwa qwarae,batace mata komai illa ciro wani d'an abun da ta ciro ta miqa mata tace "ga wannan kici dan nasan a halin yanzu yunwa kke ji",mamaki ya ishe Zeedat amma bata ceh komai ba illa qarb'an abincin da tayi dan yunwa take ji,abunka da masu sarauta bata wani ci abun kirki ba taji ta qoshi ta d'au ruwan ma tasha,Yaayin ma taci tasha ruwan ta qoshi suka rage wani,cikeda mamaki Zeedat tace "mama dama kisan zamuzo nan neh?",Yaayi tayi murmushi tace "ina fa,kwae dae sanin hali nasan hakan zata iya faruwa gashi kuwa ta faru".


漏Hama G Muh'd
[8:06pm, 1/1/2017] Hamagee馃尫: 馃崄馃尶馃崄馃尶
          *MAFARKIN HAMAGEE* 
                  馃尶馃崄馃尶馃崄

庐WISDOM OFFICIAL WRITERS 

*_In devotion to Sis Feedy_*鉂�



Page 015
   Zeedat ta rungume tana mejin dad'in kasancewar ta mahaifiya a gareta.
   Jaheed ko tunda ya tashi a barci Wahiyya ta hana shi fita dan karya gano abunda ake ciki,dan tabbas tasan idan ya sani to lallae saeya san yadda akayi aka fito dasu,dan haka ta tsare shi a gida ta hana shi fitowa dukda yadda ya matsa ya fito,a jikin shi yana jin akwae abunda ya faru bayan barcin sa amma bbu yadda ya iya dole ya haqura ya kwanta dan yasan ba barinshi maman zatayi ya fita ba.
   Koda dare yyi Yaayi da Zeedat sunyi barcinsu cikin jin dd'i bayan sun qarasa cin abincin su na d'azu,saedae cikin dare suka tashi saboda tsananin sauro da suka addabe su,duk tasu susa suke bbu sanya,a rayuwarsu kaff basu tab'a shan azaba irin ta wannan da suke ciki yanzu ba,alla alla suke gari ya waye amma ina gani suke kamar daren yau yafi na kullum jimawa,sun zamo abun tausayi dasu,ga sauro ga shegen duku dan ko idon mutum ba'a gani,Zeedat tayi kuka harta gaji tayi shiru.
   Saeda asuba suka dan samu sauqin yanayin,koda safiya kuwa tayi basu iya sun kwanta ba tsabagen rad'ad'i da jikin su ke musu duk jikinsu quraje neh jajaye gasu dama farare neh su.
   Saeda suka sake wuni kafinnan aka fitar dasu,Haima ceh tayi jinyarsu duk tausayinsu ya kama ta,bayan ta gyara Zeedat ta kawota ta kwantar bada jimawa ba kuwa tayi bacci,haka ma Yaayi bayan tayi wanka saeta kwanta tayi bacci..


漏Hama G Muh'd
[8:16pm, 1/1/2017] Hamagee馃尫: 馃崄馃尶馃崄馃尶
          *MAFARKIN HAMAGEE*
                  馃尶馃崄馃尶馃崄

庐WISDOM OFFICIAL WRITERS 

*_In devotion to Sis Feedy_*鉂�



Page 016
    Yaayi da Zeedat sunyi zazzab'in fiyeda sati sakamakon kwana cikin sauron da sukayi,gaba d'aya sun zamo abun tausayi bama yaZeedat da ita yarinya ceh,Haima ceh tayi ta musu jinya har suka fara samun sauqi.A kullum Yaayi qara son Haima takeyi,ta zame mata kamar yar uwa,itama Haiman tana son Yaayi da y'arta Zeedat.
    Wahiyya ko kullum cikin qulla munafurci take,tace anyi wannan tace anyi wancan,qarya ko a bakinta kamar tub'abb'en Sarki,tayi tayi ta raba Jaheed da zeedat amma inaa ta kasa dan ba kad'an ba Zeedat da Jaheed sun shaqu ga kishin juna da suke.
    Saedae yanzu Zeedat ta rage shiga ma Jaheed saboda halin mamarshi,Yaayi ceh tayi mata wannan nasihar gwanda abi komai a hankali sannan sae a zauna lfya da kowa lfya.
     Wahiyya na cikin bacce Jaheed ya saci hanya ya fito dan kar ta tambayi inda zai je,a hankali ya tashi kuma harya fita bata sani ba,yana fitowa ya nufa wajen wasu fadawa masu gadin gida,da zuwanshi kuwa saeya tambayesu "shin kunada labarin inda aka kai mun yar'uwa ta kwana biyu?",fadawan suka kalli juna cikin mamaki sukace "bamu da masaniya magajin Sarki",a fusace Jaheed yace "kun sani mana,idan kuma baku sanarda niba ku tabbatar kuna da munmunar hukunci agurin Sarki"..


漏Hama G Muh'd
[12:08pm, 1/3/2017] Hamagee馃尫: 馃崄馃尶馃崄馃尶
          *MAFARKIN HAMAGEE*
                  馃尶馃崄馃尶馃崄

庐WISDOM OFFICIAL WRITERS 

*_In devotion to Sis Feedy_*鉂�



Page 017
    Daga jin haka sae jikin fadawan nan ya soma rawa sukace "ranka shi dad'e ae abun be kai har haka ba,sarki neh yasa a rufesu a d'aki me duhu da sauro na kwana d'aya daga cikin d'akunan horo",wani irin tausayin sune ya d'arsu a zuciyar Jaheed wanda hakan yasanya shi zubar da qwalla,gashi dae yaro neh d'an kimanin shekaru 6 ya'n watanni amma sarae yanada feelings akan abu,bece dasu komai ba ya juya ya nufa sashen su Zeedat,a ranshi yana tunano abunda zaece mata dan yasan,bbu tsoro ko kad'an a ranshi dan haka yasa kai ya shiga qofar.
    Mamaki neh da al'ajabi suka ishe Fadawan can kowa da irin abunda yake cewa,wani yace "kai amma yaron nan bbu tsoro a ranshi",wani yace "ina kaga tsoro kuwa tunda har iya tunkaro mu da wannan maganar",wani daga cikin su yace "gashi da tunani da kaifin basira in ba haka ba ta yaya akayi yasan cewa basu kwana a gidan su ba!",d'ayan yace "gashi d'an yaro,inba na manta ba befi shekaru shida bafa",sae d'ayansu yace "baka manta ba shekarunsa shida neh da y'an kai yanxu",d'aya daga cikinsu yace "kaii,akwae kallo nan gaba to,dan yanda yaran nan suka d'auko hanya bbu alamun gaba a tsakanin su dan haka zasu iya janyo ra'ayin iyayen ma",wani yace "haka neh kam",haka sukayi ta tsegumi tsakanin su...


漏Hama G Muh'd
[12:09pm, 1/3/2017] Hamagee馃尫: 馃崄馃尶馃崄馃尶
          *MAFARKIN HAMAGEE*
                  馃尶馃崄馃尶馃崄

庐WISDOM OFFICIAL WRITERS 

*_In devotion to Sis Feedy_*鉂�



Page 018
    Yaayi na kwance tana bacci Zeedat ko na zaune suna ta shan hirarsu da Haima kamar wasu sa'anni dan yanxu ta samu sauqi bbu laifi,Zeedat ceh meyi wa Haima tambayoyi ita kuma tana bata ansoshin tambayar,bud'e qofar sukaji anyi,koda suka d'aga kai sai sukayi ido hurhud'u da Jaheed wanda shima kallo yabi su dashi,qarasowa yyi ya zauna kusa da Zeedat inda ya bata haquri kan abunda ya faru,Haima ko kallonsu kwae take dan ba kad'an ba yaran na burgeta yadda suke nuna kulawa a tsakaninsu ko a gaban waye dukda cewa iyayensu sunyi hannun riga.Zeedat tace dashi "bbu komai qanina daman baka mun komai ba,kuma dan baka zo ka taimake mu ba a lokacin a ba laifin ka bane,na tabbatar rashin sani neh don da ace kasani to daka zo inda muke,nagode da kulawarka",yace "ba komai",tace "yanxu abunda za'ayi ka tashi ka koma kar mamarka ta tashi ta neme ka bata samu ba kasan bazae mana dad'i ba koh",ya marairaice yace "nikam sae mamarki ta tashi na bata haquri dana tafi",Zeedat tace "aa Jaheed kasan halin ummar ka fa,yanxu idan ta farka bata ganka ba zata nemeka kuma idan tasan cewa nan kazo to zamu fuskanci fushinta",ta karya murya tace "ko kana so tasake sawa a hukunta muneh",da sauri ya girgiza kai..


漏Hama G Muh'd
[12:09pm, 1/3/2017] Hamagee馃尫: 馃崄馃尶馃崄馃尶
          *MAFARKIN HAMAGEE*
                  馃尶馃崄馃尶馃崄

庐WISDOM OFFICIAL WRITERS 

*_In devotion to Sis Feedy_*鉂�



Page 019
    Zeedat tace "tou ka tashi muje na raka ka idan Mamata ta tashi zan fad'a mata kazo kuma kace tayi haquri kan abunda ya faru",ta qare maganar da murmushi a fuskarta,shima murmushin yyi mata sannan ya tashi,itama ta miqe ta raka shi har qofa sannan ta dawo ta barshi ya tafi.
    Jaheed na komawa ya samu mamarshi ta tashi a bacci da gani kuma neman shi take bata ganshi ba,koda ta tambaye shi inda yaje saeya ce mata ya duba waje neh yaga ko baban shi na nan,tayi murmushi sannan ta kwad'a ma Aina kira,da hanzari Aina ta gabatar da kanka a gaban Wahiyya,tace "gani ranki shi dad'e",Wahiyya tace "Jaheed ke son ganin mahaifinsa dan haka nake so kiyi mishi jagora zuwa ga fadansa",tana qare maganar Aina tace "an gama gimbiya matar Sarki kuma uwar Sarki nan gaba",cikeda jin kai Wahiyya tace "a yanxun ma uwar Sarki nake",Aina ta murmusa sannan ta riqo hannun Jaheed ta d'orashi abayanta tana mai wasa saeta fito dashi zuwa fadar sarki,a hanya ko Jaheed yana ta jin haushin meyasa yace yana neman babansa,dama yace kwae ya leqa waje neh dan da gaske Jaheed baya son had'a hanya da babansa saboda ko kad'an baya son abunda yake yiwa yayar shi Zeedat da mamarta,don dae kwae bbu yadda zaiyi neh.Koda suke tafiyar kuwa kowa suka wuce sae yayi musu gaisuwar ban girma har suka iso fadan Sarki...



漏Hama G Muh'd
[12:58pm, 1/3/2017] Hamagee馃尫: 馃崄馃尶馃崄馃尶
          *MAFARKIN HAMAGEE*
                  馃尶馃崄馃尶馃崄

庐WISDOM OFFICIAL WRITERS 

*_In devotion to Sis Feedy_*鉂�



Page 020
    Sarki da Fadawan sa suna ganawa,a lokacin Aina ta shigo da Jaheed a bayanta,da ganin Jaheed ko fadwan suka fara masa kirari 'takawarka lafiya sarki me jiran gado,d'an sarki jikan sarki tattab'akunnen sarki,ta ko'ina d'an sarauta kke,ta uwa ta uba',Jaheed beyi wata wata ba yaje ya zauna a kujerar gefen babanshi,har lokacin kirari ake musu shida baban,shiko sarki wani irin dad'i yake ji gashi ga magajinsa dan ba kad'an ba yana mugun son Jaheed,shi kuma Jaheed be damu da kirarin da ake mai ba tunanin sa kwae Zeedat d'inshi,inda baban zae daena wulaqanta su toh daya fi kowa samun nutsuwa da farin ciki.Haka suka qare zaman su yau a fada,tareda sarki Jaheed ya koma cikin gida.
   Koda Yaayi ta farka a bacci sae zeedat ta sanarda ita zuwan d'an uwanta wato Jaheed da saqon daya bayar ta baiwa maman,har a ran Yaayi taji dd'i sosae amma saeta nuna ma Zeedat kamar bata ji dd'i ba,Zeedat yarinya ceh me kaifin tunani saboda haka ta fahimci sudden change dake fuskar maman dan haka saeta ceh "mama,meyasa kka b'ata rai?"kamar zatayi kuka dan ko kad'an bata son ganin fushinta,ganin hakan yasa maman tayi murmushi tace "aa Zeedat,ba komai kwae dae bana son kina yawan huld'a da Jaheed duk da cewar shi d'an uwanki neh amma gudun sake faruwar abunda ya faru a baya nake so ki jaa jiki da shi kinji",Zeedat ta fahimci abunda maman ta hango dan haka tayi murmushi tace "na gane Mama,nima bana son shiga mishi amma yau d'in shi yazo kinga kuma bazan kore shi ba kou",maman tayi murmushi tace "hakane y'ata",duk abunnan da akeyi Haima na zaune tana kallonsu a ranta suna burgeta matuqa,haka rayuwarsu taci gaba..



漏Hama G Muh'd
Share:

No comments:

Post a Comment

Popular Posts

Translate

Archive

featured post

UNIVERSITY GIRL Final episode(Chapter thirty)

Powered by Blogger.

Contact Form

Name

Email *

Message *

Blog Archive