This site offers you with different novels series from one writer, I hope this will educate and as well as entertain you..

LAIFIN WAYE? (Page 64)

💦 💦💦💦 💦
*LAIFIN WAYE??*
💦💦💦 💦💦💦

_Written by the Aplomb writer: *Hamagee*_

*In devotion to Maman Saif*
💦

Wattpad @ Hama_gee

Page 64 💦💦

   Abin ya bata mamaki,bata tab'a tsammanin Suhana zata ce hakan ba. Tace "haba Suhana, yanzu haka kike so mu zauna muna kallon Daddyn ki?". Suhana tace "oho,ni dai bazan iya bada wasu kud'in bane kuma babu gidan da za'a saida,ni ban hanaki kai mijinki ayi mishi jinya ba ni dai kawai na gaji da zubar da kud'i a asara ehe!". Mommy tace "yanzu mahaifin naki ne asarar".


    Suhana ta ja tsaki ta bar wajen ma,gida ta koma inda ta d'an dafa indomie taci daman yunwa take ji,bayan nan saita kwanta sai bacci. Mommy kuwa kasa d'aukanta qafafunta sukayi a wajen ta zube tana kuka me cikeda dana sani wanda mallam bahaushe yace qeya ceh. Tama rasa ta inda zata b'ullowa lamarin,daga qarshe dai ta yanke shawarar cin bashi a banki dan nan ne kawae zata samu biyan buqatar ta a yanzu,tashi tayi ta nufi banki inda ta samu taci bashin kud'in sannan tayi musu shirye-shirye akan anjima da daddare zasu wuce India.

    A asibitin ta bar Daddy bayan ta roqi alfarmar cewa su riqe shi kafin lokacin tafiyar tasu tayi dan yanzu idan ta maida shi gida ma bata san yadda zatayi dashi ba gwara yana gurin likitoci. Bayan ta koma gida kaya ta d'ayan had'a musu wanda basu wuce set biyu ba kowannen su,koda ta gama abinda zatayi zuwa qarfe biyar ta fito,har a lokacin Suhana na kwance tana ta sharar bacci kamar wacce bata san me ake kira da matsala ba,girgiza kai kawai Mommy tayi sannan ta fice.


    A ranta tana mugun son Suhana hakan yake hana idan tayi LAIFI tayi mata fad'a wanda hakan ba qaramin kuskure bane. Asibitin ta koma inda ta zauna a kusada Daddy tana ta qare mishi kallo. Saida lokacin tafiyar su ya kusa kafin suka bar asibitin,suna isa airport kuwa ana kiran sunan su sai suka shiga jirgi. Qarfe bakwai daidai jirginsu ya d'aga.


    Suna isa India kai tsaye asibitin suka nufa inda Likitoci suka karb'i Daddy cikin gaggawa suka shiga duba shi. Anan ne suka gano cewa allurar da akayi mishi jiya tayi mishi qarfi ainun wanda yinta ya katse hanyar yawon jikin a system d'in shi. A halinda ake ciki dai Allah yayi wa Daddy rasuwa run a cikin jirgin,kasancewar dama ba motsi yakeyi ba yasa ko kad'an Mommy bata fahimci hakan ba,sai dai babu yadda aka iya da ikon Allah,shine mahaliccin rai kuma shike d'aukan na wanda yaso kuma a lokacin daya so,sannan ta yadda yaso,Allah ya gafarta ma Daddy shine fatan mu.

    Koda aka sanarma Mommy a wajen ta yanki jiki ta fad'i sumammiya,nan aka ciccib'eta sai sick bay inda aka bata immediate treatment, Allah sarki Mommy bugawa zuciyar ta tayi a halin yanzu ta kamu da ciwon zuciya. Bayan an gama treating d'inta dan harta farfad'o ma sai akayi mata alluran bacci tareda d'aura mata drip sannan aka barta ta huta da fatan in ta farfad'o shikenan ta warware.


★★★
Sai can dare Suhana ta farka daga baccin da takeyi tun azahar har anyi sallahn isha yanzu. Tana tashi bata tsaya ko'ina ba sai toilet, wanka tayi sannan ta fito ko sallah babu,daman ganin idon iyayen ne yake sata wani lokacin tayi sallahn. D'akinsu ta nufa inda ta tarar har yanzu Mommy bata dawo ba,a ranta tace ko lafiya oho. Fita tayi ta koma palourn inda ta d'au wayarta ta shiga yin chatting,wanda rabonta da yi ya d'an kwana biyi,cikin jin dad'i take abinta.

    www.hghausanovelseries.blogspot.com

Share:

No comments:

Post a Comment

Popular Posts

Translate

Archive

featured post

UNIVERSITY GIRL Final episode(Chapter thirty)

Powered by Blogger.

Contact Form

Name

Email *

Message *

Blog Archive