💦 💦💦💦 💦
*LAIFIN WAYE??*
💦💦💦 💦💦💦
_Written by the Aplomb writer: *Hamagee*_
*In devotion to Maman Saif*
💦
Wattpad @ Hama_gee
Page 63 💦💦
Suna zaune kowa da irin tunanin da yakeyi Suhana tace wa Mommy "yanzu Mommy haka zamu cigaba da zama kaman bamu da 'yanuwa da zasu taimaka mana,infa muka cigaba da zama a haka to wallahi sai mun wayi gari sisi ma bamu dashi so gwanda kawai mu san nayi",Mommy tace "Suhana kenan,kema kin san yanzu 'yanuwana ba kaman da bane,kowa na fama da kanshi to balle kuma dangin mahaifinki,ke kin san komai ai kin san cewa dashi suka dogara,koma ba haka ba idan yau aka taimaka mana ai gobe za a gaji damu ko".
Suhana taja wani ajiyar zuciya kafin tace "hakane amma gaskiya abin ya fara yin yawa,duba fa,yanzu daga ni har ke babu me kud'i in banda canjin daya rage d'innan ba",Mommy tace "to yaya zamuyi neh,ai dai baza mu barshi ya mutu da ciwon ba ko,dolenmu muyi mishi magani koda hakan na nufin tsiyacewar mune gabad'aya". Suhana ta juyo ta kalleta alamar rashin yadda da maganar ta sannan ta juya kai,daga nan bata sake cewa qala ba,itama Mommyn bata sake maganar ba.
Washegari tsaf suka shirya da sassafe suka nufi asibitin,koda suka isa ba'a bari sun ganshi ba dan bai farka ba tukunna kuma so ake yi ya tashi da kanshi,ba a son a tashe shi. Guri suka nema suka zauna inda kowaccen su ke tunani dan yanzu tunani ya zamo musu kaman jiki. Suhana kuwa ba komai take qullawa a ranta ba illa ta gaji da kashe ma Daddy kud'i kuma kullum abu guda babu wani d'an cigaba.
Har wajen qarfe sha biyu na rana bai farka ba,hakan ya bama Likitocin mamaki dan by now ya kamata ace ya d'an dawo daidai ma,wata allura sukayi mishi wacce tasa ya farka babu shiri. Instead of a samu cigaba tunda anyi aikin saima qaruwa da lamarin yayi fiyeda da d'inma. Ganin hakan yasa suka bama su Mommy a fidda shi waje kawai dan a halin yanzu basu san abinda zasu sake yi mishi ba.
Koda aka fad'a musu hakan instead of them su yadda da qaddara sai Suhana tayi caraf tace "why doctor? Why?,kusan cewa fa you people can't cure him to miyesa kuka ci mana kud'i,yanzu kun san muna da kud'in fidda shi wake ko bamu dashi neh?". Likitan yace "sai dai haquri dan muma bamu san hakan abin zai dawo ba,dama kun hanzarta kun san nayi ne because the patient is in a critical condition now, you have less time", yana kaiwa nan ya tafi ya basu a wajen.
In banda salati da koke-koke babu abinda Mommy keyi. Suhana ce ta dubeta tace "to kinji fa,ni wallahi na gaji haka,ya isheni". Mommy tace "yanzu ki kawo sauran kud'ad'en wajenki mana a samu ayi wasu shirye-shiryen in yaso wanda ya gagara sai mu saida gidan da muke ciki in yaso mu nemi koda d'aki d'aya ne da palour,sai kitchen da toilet".
Wani irin kallo Suhana ta zuba ma Mommy kafin tayi commenting "haba dai mu saida gida",Mommy tace "to yaya zamuyi shi kad'ai ya rage mana,ko kinada wata dabarar ce?". Suhana tace "ai dabarar kenan a barshi a gida a cigaba da yi mishi addu'a ko zai samu sauqi dan wallahi ni yanzu na gaji,kud'in ma da kike cewa in bada bazan iya badawa ba gaskiya",baki sake Mommy take kallon Suhana.
www.hghausanovelseries.blogspot.com
No comments:
Post a Comment