This site offers you with different novels series from one writer, I hope this will educate and as well as entertain you..

ALHAKI NEH! (Page 7)

🌸🦋🌸🦋🌸🦋🌸🦋🌸

*ALHAKI NEH!*

🌸🦋🌸🦋🌸🦋🌸🦋🌸🦋

® *_REAL PURE MOMENT OF LIFE WRITERS_*

_ɯɛ ɖơŋ'ŧ ơŋٳყ ɛŋŧɛřŧąıŋ ŋɖ ɛɖųĆąŧɛ, ცųŧ ɯɛ ąٳŞơ ŧơųĆɧ ŧɧɛ ɧɛąřŧ ơʄ řɛąɖɛřŞ_

By the applomb writer: *Hamagee*

Jan,2018.

# WWW.PMLWRITERS@GMAIL.COM
# IG PML WRITERS
# https://www.facebook.com/PML_-Writers-FANS-459256761123035
# http://maryamsbello.blogspot.com

Wattpad @Hama_gee

Page 07

°
A dai-dai k'ofar Maharaj (restaurant) ya tsaya ganin sun riga sun iso,dan daga gani a Zion (sunan hostel) take saboda babu wani hostel gabada da wannan. Sai da ya jira yaga shiganta kafin ya yi gaba dan shima hostel d'insu ta wajen ake bi. Ranan Aminu ya sha mafarkai dan ba k'aramin kamuwa da son yarinyar nan yayi ba.

Washegari tun bayan sallahr asuba Aminu ya nufa Science Lecture Theatre (SLT) dan yin karatu saboda already sun fara test,kuma yauma sunada wani k'arfe 2. Bai bar hall d'innan ba sai k'arfe 9 na safe,ya taso kenan yana saukowa saiga yarinyar jiyannan ta shigo ita kuma tana hawowa dake steps neh wajen.

Tsayawa yayi cak harta zo ta wuce ta gefen shi,jikin shi yayi matuk'ar yin sanyi harma ya rasa abinda zaiyi,nan ya fara tunani yaje ne ko ya barta ba yanzu ba tunda karatu zatayi karya hanata yi. Daga k'arshe dai ya yanke shawarar tafiya inyaso in yaje ya karya saiya dawo kafin nan ta gama karatun,hakan kuwa yayi.

Nan ya ja jikin shi yabar cikin SLT yazo ya tsallaka titi ya shiga hostel. Bayan ya shiga d'aki ya ajiye takardun dake hannun shi ya d'an zuna a gefen katifar shi yana wani nazarin. Sulaiman abokin shine yayi sallama ya shigo,Aminu bai ma ji sallamar ba dan tunani da sak'e-sak'e yake tayi,Sulaiman ya dube shi kafin yaje ya sauk'e abinda ke kan wuta dan harya fara kamawa duk Aminu na zaune a d'akin kuma bai ji ba.

Bayan ya sauk'e sai ya dawo gareshi tareda yi mai tambayar "lafiyar ka kuwa?",sai lokacin Aminu ya san da shigowar shi,yace "ah! Yaushe ka shigo kai kuma?". Sulaiman yace "ina zaka sani ka zauna nan kana ta tunani". Aminu yace "bari kawai wallahi".

Sulaiman yace "gashi ka d'ora girki harya fara k'una,amma na dauk'e maka",Aminu yace "anya kuwa,bani na d'ora ba inajin nima na shigo na sameshi don banma san dashi ba". Sulaiman yace "ba mamaki Sadiq ne to,yanzu haka ya d'ora ya tafi d'akinsu Ustaz don ina wucewa na jiyo shewarsu". Aminu yace "maybe".

Suna cikin haka saiga Sadiq yayi sallama ya shigo d'akin tareda fad'in "subhanallah,harya fara k'una". Sulaiman ya harare shi tareda fad'in "kai dai you never change wallahi,ace mutum ya d'ora abu inba ganganci ba ya tafi ya bari kuma babu kowa a d'akin". Sadiq yace "da nasan hakan zata faru neh? Kuma ma ba don ku nake girkin ba wai karku dawo ku nemi abinci".

Aminu dake shi yana biyewa Sadiq d'in yace "don't worry my aboki,leave him ai kayi k'ok'ari". Sulaiman ya ja tsaki tareda mik'ewa ya basu waje,ai kuwa dariya sukayi mishi,nan Sadiq yayi serving d'insu suka zauna suka fara ci,da k'yar Sulaiman ya hak'ura ya jona su suka ci abincin. Bayan suna gama ne Aminu take basu labarin yarinyar nan tun daga ganinta jiya zuwa yau dan bashi da wasu abokai da suka wuce Sadiq da Sulaiman.

Sadiq ne ya dubeshi yace "ai kuwa tashi zakayi yanzun nan muje mu tsaro ta,koya kace" ya k'arasa yana kallon Sulaiman,shi kuma Sulaiman d'in harda gwaleshi tareda fad'in "kaifa ka fiye rawar k'afa,wane irin kuje ku tsaro ta,shi dai yaje ya tsara abinshi haka yafi". Sadiq yace "kaima kace wani abu" ya juyo ya kalli Aminu kafin yace mishi "tashi zamuyi yanzu mu raka ka amma ki zaka k'arasa kayi mata magana,in yaso daga baya idan kun daidaita ma gaisa muma ko", Sulaiman yace "yanzu kayi magana mutumi na". Ya bashi hannu suka tafa,nan suka fice tareda zuwa SLT.



     hghausanovelseries.blogspot.com

Share:

No comments:

Post a Comment

Popular Posts

Translate

Archive

featured post

UNIVERSITY GIRL Final episode(Chapter thirty)

Powered by Blogger.

Contact Form

Name

Email *

Message *

Blog Archive