🌸🦋🌸🦋🌸🦋🌸🦋🌸
*ALHAKI NEH!*
🌸🦋🌸🦋🌸🦋🌸🦋🌸🦋
® *_REAL PURE MOMENT OF LIFE WRITERS_*
_ɯɛ ɖơŋ'ŧ ơŋٳყ ɛŋŧɛřŧąıŋ ŋɖ ɛɖųĆąŧɛ, ცųŧ ɯɛ ąٳŞơ ŧơųĆɧ ŧɧɛ ɧɛąřŧ ơʄ řɛąɖɛřŞ_
By the applomb writer: *Hamagee*
Jan,2018.
# WWW.PMLWRITERS@GMAIL.COM
# IG PML WRITERS
# https://www.facebook.com/PML_-Writers-FANS-459256761123035
# http://maryamsbello.blogspot.com
Wattpad @Hama_gee
Page 08
°
Bayan sun iso SLT a dai-dai jikin wata bishiya akwai benches na zama so sai suka zauna a wajen shi kuma Aminu ya k'arasa ya shiga cikin SLT. Can sama ya hangota a zaune tana karatu,ga dukkan alamu ta gajiya tana son tashi ne don yaga tana tattara books d'inta dake kan desk d'in.
Hawa yayi har inda take zaune sannan ya nemi seat next to nata ya zauna tareda yi mata sallama. Ta amsa ba tareda ta kalleshi ko inda yake ba,yadda take abinta a nutse yana mugun birgeshi. Nan ya fara mata magana,ya sanarda ita dalilin zuwanshi da kuma inda ya fara ganinta da dai sauransu,sannan yayi mata introducing kanshi tareda nuna buk'atar itama ta gabatar mishi da kanta.
Bata wani bashi wahala ba saidai ita batace mishi ta amince da buk'atar shi a gareta ba. Amma yayi matuk'ar yin farin ciki tareda godema Allah da yasa ta yarda da shi duk da bata furta ba amma alamu sun nuna kansu. Nan Aminu ya taya ta had'a kan books d'inta tareda rik'o mata su,har kusada hostel ya rakota kafin ya bata books d'in sannan ya karb'i number d'inta tareda rok'on ta sanar mishi sunanta don daga farko bata fad'a mishi ba.
Nan ta bashi number tareda fad'in sunanta Amina amma Meena is her nickname dan amfi saninta ma ta hakan. Ya karb'a tareda yin godiya da yimata sallama sannan suka rabu zuciyar shi fal da farin ciki. A haka ya koma gun abokanshi ya sanar dasu yadda sukayi da ita,suma sunyi farin ciki sosai.
Amina Yaseen Ahmad (Meena) asalin 'yar Bauchi ceh,nan iyayenta suke kuma nan ne asalin su. Tana da yayyu uku,biyun farko maza neh sai yarta wacce take bi me suna Aisha,sa'annan tana da k'anne guda biyu ,namiji me suna Abdallah sai Aneesa wato 'yar autar su kenan. Su shida kenan a wajen iyayensu,babban yayansu me suna Aliyu yana da aure da d'anshi d'aya dan shekaru biyu kenan da auren nashi. Second born d'in kuma wato Auwal yana service d'inshi a Benue. Sai Aisha wacce Amina ke binta tana 400level anan ATBU,I.T kenan. Tanada aure da yaran ta biyu.
Sai Abdallah na SS2 yanzu,sannan Aneesa autarsu kenan tana Jss1. Kad'an daga tarihin Amina kenan..
***
A week ltr..
Da daddare wajen 8:30 Aminu ya kira wayan Amina inda suka sha hiransu kafin sukayi sallama daga baya. Soyayya ta k'arfi a tsakanin Amina da Aminu cikin k'ank'anin lokaci wanda hakan su kansu yana basu mamaki,hakama ga mutane dan dukansu ba masu hayaniya bane. Yawancin lokuta suna tare ko suna hira ko suna karatu,dan ya kan koya mata abubuwan da bata ganesu ba.
A kwana a tashi babu wuya,har suna shirin gama first semester exams,karatu kowannen su yasa gabanshi dan haka yanzu sun rage had'uwa ma,yawanci suna venue suna karatu. Amina ta riga shi gama exams dan haka bayan ta gama gida ta koma,kullum suna waya duk da ba sosai dan baya samun lokaci sosai amma tana bashi uziri dan tasan yanayin karatun nasu saida dagewa da naciya inba haka ba bazasu samu abinda suke so ba.
Bayan gamawanta da one week shima ya kammala nashi,a ranar ya koma gida dan da safe yayi exam d'in. Da daddare kuwa yaje wajenta,sun jima suna hira kafin yayi mata sallama ya koma gida. Bayan komawar shi gida saida sukayi waya kafin sukayi bacci.
hghausanovelseries.blogspot.com
No comments:
Post a Comment