This site offers you with different novels series from one writer, I hope this will educate and as well as entertain you..

LAIFIN WAYE? (Page 56)

💦 💦💦💦 💦
*LAIFIN WAYE??*
💦💦💦 💦💦💦

_Written by the Aplomb writer: *Hamagee*_

*In devotion to Maman Saif*
💦

Wattpad @ Hama_gee

Page 56 💦💦

    Washegari kuwa zaga garin suka fita yi tunda hantsi da suka tashi sukayi wanka suka karya. Suhana ta nuna mishi wurare da yawa,sai dai bata kai shi gidan 'yanuwan su koda guda d'aya ne ba. Shima kuma bai damu daya tambayi hakan ba,saida yamma suka koma gidan. Yauma kamar jiya takeaway d'in suka sake yi.

   Kwanan su uku suka koma Uganda ,kafin su tafi kuwa saida suka bama Mommy kud'i mai yawa da zata kula da kansu tukunna. Randa suka dawo Farhan yaso ya kwanta da Suhana amma fir taqi saboda sharad'i na biyun na boka ya bata kenan,akan kada ta yadda mijinta ya kusanceta sai nan da wata guda tukunna inba haka ba da matsala babba. Tana son shi kuma tana son faranta mishi rai amma babu yadda ta iya dole haka ta haqura.

    Akan hakan Farhan kullum cikin kyauta yake mata amma taqi amincewa dashi. Ya rasa abinda zaiyi mata ta yadda dashi,gashi kullum tana cikin kuka. Koda ya tambayeta kuwa ce mishi takeyi babu komai,daga qarshe dai asibiti ya kaita. Bayan an dubata ko tana da matsalar qwaqwalwa sai aka ga lafiyar ta lau,babu abinda ya samu brain d'inta. Hakan ba qaramin qara d'aga ma Farhan hankali yayi ba,in bata da matsala ta lafiya to miyesa take yawan yin kuka?.

Kwanaki sai wucewa sukeyi,
    Ga kud'i ga lafiya amma gaba d'aya Suhana bata cikin jin walwala da jin dad'i,ita kanta bata san miye d'aya ke damun ta ba. Shiyasa mutane su tunanin wai auren miji me kud'i shine jin dad'in rayuwa,wallahi ba haka bane dan wanin sanadiyyar tarwatsewar rayuwar shi kenan. In Allah ya wadata ka da miji me hali saika gode mishi amma kada kace wai dole sai me halin,yin hakan yana iya jefa ka ga halaka,Allah yasa mufi qarfin zuqatanmu ameen.

    Watarana da yamma suna zaune suna kallo Farhan ya fara jin zazzab'i,kamar wasa dai ya fad'a mata. Magani yasa sannan tace ya samu yayi bacci ko inya tashi zai ji sauqi,hakan kuwa akayi bai jima da kwanciya ba bacci ya d'auke shi. Bashi ya tashi ba sai wajen qarfe 9 na dare.

     Zazzab'i me zafi ya tashi dashi,wannan karon kanma harda su amai da gudawa ga murd'ewan da cikin shi keyi. Hanalin Suhana yayi matuqar tashi ganin halinda yake ciki. Batayi wata-wata ba tasa aka kaisu asibiti inda Likitan dake duba shi ya karb'e shi. Tambayoyi ya shiga yiwa Suhana gameda magungunan shi akan yana shansu,tace yana sha.

   Likitan yace lallai akwai abinda ya shafi shan maganin shi,maybe akwai wanda ya kamata dasha sai yayi mistake ya sha wanda bashi bane. Drip aka d'aura mishi bai ma san inda yake ba. Da daddare kuma aka sake yin wasu gwaje-gwajen kafin nan akayi mishi wata allura tareda saka mishi wani ledan ruwan.

    Suhana kuwa bata iya cin komai ganin yanayin jikin nashi. D'azu ta kira Mommy ma ta sanarda ita halinda ake ciki,bayan Mommy ma saida sukayi waya da Suby. Abin dai babu dad'i,gabad'aya ta gaji da rayuwar ma a fad'inta. Mijinta babu lafiya,ga abinda ya faru tsakaninta da Boka wanda a koda yaushe ta tuna sai taji takaici da baqin ciki mara misaltuwa,ga kuma halinda iyayenta me ciki,Babanta raina hannun Allah gata itama kanta batada lafiyar. Dana sanin wasu aiyukan da tayi a baya ta fara yi amma a yanzu ba amfani hakan zaiyi mata ba,abinda ake gudu ya riga da ya faru.

     www.hghausanovelseries.blogspot.com

Share:

No comments:

Post a Comment

Popular Posts

Translate

Archive

featured post

UNIVERSITY GIRL Final episode(Chapter thirty)

Powered by Blogger.

Contact Form

Name

Email *

Message *

Blog Archive