💦 💦💦💦 💦
*LAIFIN WAYE??*
💦💦💦 💦💦💦
_Written by the Aplomb writer: *Hamagee*_
*In devotion to Maman Saif*
💦
Wattpad @ Hama_gee
Page 54 💦💦
Washegari sai 9 suka tashi daga bacci,suna shiryawa driver ya d'auke su sai airport. Qarfe 12 dai-dai jirginsu ya tashi,tafiyar awa uku sukayi so qarfe 3 da wani abu suna Nigeria. Taxi suka nema inda ya kai su har gidansu Suhana. Sun sha tarba gun Mommy ranan,taji dad'in ganinsu a haka dan ba qaramin kulawa da Suhana Farhan ke yi ba yanzu dan harma yafi nada.
D'aki guda Mommy ta ware ta gyara musu tareda wanke toilet tun kan su iso,sannan ga ruwan wanka yana nan yana jiransu. Saida suka ci abinci kafin sukayi wanka,Farhan ya kwanta dan ya gaji akan sai zuwa gobe su fita zagawa. Suhana kuwa da Mommy suka fita,basu tsaya ko ina ba sai gidan bokan nan wanda Mommy take zuwa a kwanakin nan.
Nan tayi ma bokan nan introducing d'in Suhana cewa ita yarinyar tan da take so ayi mata aiki,yanzun ta kawo ta koda wani taimakon da za a qara mata dan ba'a qasar suke zama ba yanzunma zuwa sukayi kuma bazasu fi kwana uku zuwa hud'u ba zasu koma. Shi bokan nan tunda ya sanya Suhana a idon shi kawai yaji tayi mishi kuma kota halin qaqa saiya sameta koda sau d'aya neh kuwa. Maganganun da Mommyn take ta yi kuwa baima san tana yinsu ba dan gabaki d'aya ya tattara hankalin shi guri guda wato kan Suhana.
Itama Suhanan ta fahimci irin kallon da yake yi mata dan harta fara tsarguwa ma. Can bayan ya dawo hankalin shi saiya ceh "hajiya kika ceh wannan ne 'yarta ki?". Mommy tace "eh,itace". Boka yace "ai akwai babban aiki neh shiyasa kika ji nayi shiru,muna tattaunawa da sarkin aljanu neh",Mommy tace "tooooo,lafiya dai koh?". Boka yace "eh toh,in kunso ya zamo lafiyan kenan!".
Cikin rashin fahimta Mommy ta tambaya "ban gane ba fa,me kake nufi?",Boka yace "wata babbar matsala ceh ke shirin taso musu a cikin zamantakewar su wanda idan akayi sakaci rabuwar tazo qarshe kenan". Mommy ta rud'e,ta dube shi da kyau tace "wace matsala kenan? Kuma kana ganin za a iya magance ta?". Boka yace "ai babu matsalar da bazata magancu ba,sai dai iya magance tanne aiki".
Mommy tace "karka damu koma nawa kake so zamu baka ai tazo da mijin nata,tare suke dan haka koma nawa kake so zaka samu babu matsala". Boka yayi irin dariyar nan tasu "hahhhaahhhaa". "Kada ki damu ba kud'i ko dukiya muke buqata ba,indai har zata amince damu shikenan",ya qarasa maganar yana nuna Suhana.
Har yanzu Mommy bata fahimci nufin shi ba dan haka tace "amincewar me kuma? Ai da saninta ta san duk wani abinda ake qullawa tunda itace tayi ta turo mun kud'in dana yi ta baka". Boka yace "ya kika neman cewa baki fahimta bane? To ina nufin sai nida ita mun had'a makwanci kafin aikin ya yiwu ina fatar yanzu kin fahimta?".
Wani ras Suhana taji a qirjinta,ba ita kad'ai ba harta Mommy saida taji fad'uwan gaba da jin maganganun Boka. Mommy ceh ta shiga bashi haquri "dan Allah boka kayi mana afuwa,wannan buqatar tayi tsauri da yawa. Mata da mijinta kuma kace zaka sadu da ita,gaskiya ba zai yiwu ba". Boka ya daka mata tsawa "to ku tashi ku bar nan,kuma ina me tabbatar muku da cewar bazai koma da ita gidan shi ba,anan zai saketa ya tafi ya barku da jaraba. Kwanciyar hankalin ku kad'ai shine ku bani had'in kai,in kuma ba haka ba to zaku Sani".
www.hghausanovelseriesblogspot.com
No comments:
Post a Comment