This site offers you with different novels series from one writer, I hope this will educate and as well as entertain you..

ALHAKI NEH! (Page 10)

🌸🦋🌸🦋🌸🦋🌸🦋🌸

*ALHAKI NEH!*

🌸🦋🌸🦋🌸🦋🌸🦋🌸🦋

® *_REAL PURE MOMENT OF LIFE WRITERS_*

_ɯɛ ɖơŋ'ŧ ơŋٳყ ɛŋŧɛřŧąıŋ ŋɖ ɛɖųĆąŧɛ, ცųŧ ɯɛ ąٳŞơ ŧơųĆɧ ŧɧɛ ɧɛąřŧ ơʄ řɛąɖɛřŞ_

By the applomb writer: *Hamagee*

Jan,2018.

# WWW.PMLWRITERS@GMAIL.COM
# IG PML WRITERS
# https://www.facebook.com/PML_-Writers-FANS-459256761123035
# http://maryamsbello.blogspot.com

Wattpad @Hama_gee

Page 10

°
K'arfe 3:30pm...
Zuwaira na zaune ta had'a uban tagumi,gabad'aya abin duniya ya isheta. Ta rasa yadda zatayi kan lamarin Aminu,gashi girma yake dad'a yi amma babu wata alamar canzawa a tattare dashi,hakan ba k'aramin tayar mata hankali yake ba. Gashi bata sake haihuwa ba balle tace inba wancen akwai wani. Hakan yasa ta fara mugayen tunani da shawarwari.

Akwai wata k'awarta ko ince aminiyarta dan tun suna yara suke tare,sunanta Hafsa ana ce mata Adda Hansatu. Itace ta fad'o ma Zuwaira a tunani,tashi tayi babu shiri ta sab'i hijabinta ta sanya. Ta rufo k'ofar ta fice,Mahdi baya gida balle ta sanar mishi zata fita,ko dayake ko yananan ma ba hanata zaiyi ba dan ta raina mishi dama.

Adda Hansatu na zaune tana kwashe tuwo dan da wuri take girginta itakam. Tana yi tana y'an wak'e-wak'en ta,sallamar Zuwaira da ta jiyo yasa tayi shiru tana sauraron me shigowa. Sallama Zuwaira ta sakeyi ita kuma ta amsa tareda yi mata iso. Shigowar Zuwaira yasa ta sake muciyar da ke hanunta ta taso da sauri tana yi mata maraba sannu da zuwa.

Har uwar d'aki ta kai Zuwaira sannan ta bata wuri ta zauna sannan ta fito ta lek'a d'akin Zainab 'yarta kenan tace tazo ta kawo ma bak'uwarta ruwan sha,saida Zainab ta gama mitarta tukun na ta tashi kai ruwan.

Bayan ta gama lallashi da rok'on Zainab saita koma d'aki gun Zuwaira,suka gaisa suna masu farin cikin ganin junansu dan sun jima basu had'u ba dama. Halinsu d'aya babu banbanci ko kad'an hakan yasa k'awancen su jimawa,itama Adda Hansatun sai abinda tace a gidan ake yi dan ita kanma bata zauna da uwar mijinta ba dan tace bazata iya ba,amma a halin yanzu uwar mijin batada rai.

Nan suka shiga gulmace-gulmace kan abinda be shafe su ba suna tafawa da dariya. Zuwaira ta gyara zama kafin tace "k'awata kin san ko abinda ke tafe dani?",Adda Hansatu tace "saikin fad'a". Zuwaira tayi gyaran murya kafin tace "maganar d'ana dai,Aminu!". Adda Hansatu tace "me kuma ya samu Aminu dake birni?",kafin Zuwaira ta bata amsa sai Zainab ta bankad'o labulen d'akin babu ko sallama ta shigo tazo ta ajiye ruwa da cup d'in da mamanta tace ta kawo.

Ba tareda tayi wa Zuwaira kallon mutunci ba tace "sannu da zuwa",kafin Zuwaira ta amsa kuwa ta juya kai zata fice,muryar maman neh ya dakatar da ita "baki ganeta bane Abuwa?,Maman Aminu ce fa". Zainab ta juyo tareda washe baki sannan tace "au,kin san ban ganeta ba Umma".

Ita dai Zuwaira kallonsu kawai take yi da mamaki,maganar da Zainab tayi ne ya dawo da hankalinta. Har k'asa Zainab ta tsuguna tareda fad'in "ina yini Umma Zuwaira". Zuwaira ta d'anyi murmushi kafin tace "lafiya lau 'yata,haka kika girma ai na jima ban ganki ba". Zainab tayi dariya tareda fad'in "ai Umma tace min kina tambayata in kinzo lokacinda nake makaranta". Zuwaira tace "yanzu kam anyi candy ai". Zainab tace "eh". Bayan sun gama Zainab ta tashi zata fita sai maman ta tace ta d'an k'arasa tuk'a mata tuwo a kan wuta daga nan saita kwashe,babu b'ata rai ko tura baki ko wani gunaguni dai tace "toh Umma" saita fice zuwa yin abinda uwar ta sata.

Ko kun san dalilin daya saka Zainab rusuna jin ance Zuwaira ceh? Ko me yasa ta rawar jiki? Ko miyasa da maman tasa ta wani aikin batayi hancini ba? Muje zuwa shafin gaba dan warware muku k'ullin...

     hghausanovelseries.blogspot.com

Share:

No comments:

Post a Comment

Popular Posts

Translate

Archive

featured post

UNIVERSITY GIRL Final episode(Chapter thirty)

Powered by Blogger.

Contact Form

Name

Email *

Message *

Blog Archive