This site offers you with different novels series from one writer, I hope this will educate and as well as entertain you..

MAFARKIN HAMA (PART 3)

馃崄馃尶馃崄馃尶
          *MAFARKIN HAMAGEE 3*
                  馃尶馃崄馃尶馃崄

庐WISDOM OFFICIAL WRITERS 

*_In devotion to Sis Feedy_*鉂�



Page 041
  Da sauri Zeedat ta miqe tana kallon Jaheed suprisely,Jaheed ma kallonta yake yace "dama nan wajen kke zuwa kullum shine kke b'oye mun",Mud'allib neh yace "ku zauna ku fuskanci juna mana",sae a lokacin Jaheed yasan dashi a gurin dan da idonshi kamar a rufe yake baya ganin kowa sae Zeedat. Jaheed ya kalleshi cikeda mamaki sannan ya juyo ya kalli Zeedat saeya nuna Mud'allib yace "wannan kuma waye Zeedat?"Zeedat ta dubi Mud'allib tace "wannan shine Mud'allib me taimako gareni,gareka kuma ga al'ummar wannan garin,shine wanda ya fitarda ni daga cikin duhu kuma kuma yake neman fitar daku zuwaga haske dan kuwa tabbas addinin islam addinin haske neh,saboda rayuwata a yanxu ta sauya don ni kaina ina ji a jikina,a halin yanzu Me martaba,mamana da kuma Haima suna cikin addinin dan haka nake so kaima ka karb'e shi domin mu tsira tare",Jaheed daya tsaya yana ta kallon Zeedat sae yanzu ya nisa yace "amma wannan wane irin addini neh da har me martaba ya amince dashi? Lallae ya zamo dole in karb'e shi nima dan tabbas bana son yadda rayuwar mu anan garin take tafiya".
 Cikeda farin ciki Zeedat tace "Alhamdulillah",Mud'allib ma godiya yyi ga Allah sae yyi sujada Zeedat ma ta bishi sukayi tare yanda suka karanto addu'ar da ake yinta yayinda mutum ya rizqi abun farin ciki saeya yita don nuna godiya ga ubangiji.Koda Jaheed yaga sunyi sujadan,shima sae yyi yadda suka yi...


漏Hama G Muh'd
 馃崄馃尶馃崄馃尶
          *MAFARKIN HAMAGEE 3*
                  馃尶馃崄馃尶馃崄

庐WISDOM OFFICIAL WRITERS 

*_In devotion to Sis Feedy_*鉂�



Page 042
    Bayan sun d'ago sae Jaheed ya tambayi dalilin yin hakan sae Mud'allib yyi mishi bayanin komai.basu bar wajen ba saeda Jaheed ya musulunta ya karb'i dukkan cika cikan musulunci,bayan nan Zeedat ta sanarda shi hukuncin da Sarki ya yanke na cewa ita zae barma sarauta amma yanxu lallae Sarki zaeji dad'i kuma zae bar mishi karagar mulki in yaji cewa ya musulunta dan dama damuwar shi itace yadda mulkin garin zae cigaba kan koyarwa irin ta addinin Allah,addini mafi adalci,addini me koyarda mulki da yadda ake yin shi.
 Bayan sun rabuda Mud'allib wanda ya kasance cikin murna da farin ciki,sae suka nufa gida tare bawan da ya rako Jaheed na biye dasu,hira suke inda Zeedat take qara sanarda Jaheed wasu abubuwa gameda musulunci shi kuma yana jin dad'in hakan.A haka har suka isa gida,suna isa sashen baban suka nufa inda suka taradda shi kwance yana neman miqewa,da sauri Jaheed ya qarasa inda yake ya tayashi gyara zama,ya sa mishi matashi a ta kanshi sannan yace mishi sannu,Baban yace yauwa cikeda mamakin Jaheed da kuma farin cikin ganinsu tareda y'ar uwarshi,Zeedat ma ta qaraso tana mishi sannu,yaji dad'i sosae..


漏Hama G Muh'd
 馃崄馃尶馃崄馃尶
          *MAFARKIN HAMAGEE 3*
                  馃尶馃崄馃尶馃崄

庐WISDOM OFFICIAL WRITERS 

*_In devotion to Sis Feedy_*鉂�



Page 043
    Bayan duk sun gaida shi sae Zeedat take sanarda shi gameda musuluntar qaninta wato Jaheed,Sarki yyi murna qwarai da jin hakan dan haka yyi ta saka musu albarka,bayan sun gama sae Zeedat ta kira sunan baban "Baba",sarki ya ansa da "naam",sae Zeedat ta cigaba da cewa "tunda yanzu Allah yyi d'an uwana ya karb'i musulunci,to ina ganin ya kamata a matso da wannan hidima wato nad'in sarautar shi,ya kamata a sanar a fada cewa gobe za'a nad'ashi sarki kaga daga nan addinin zae fara yad'uwa har ya gama zaga garin",sarki yana jin batun Zeedat yana girgiza kai alamar abunda take fad'i gaskiya ceh,sae bayan ta gama saeya ceh "wannan gaskiya ceh,lallae kinyi tunani me kyau,Allah ya kaimu goben",sukace "ameen",Sarki yace "yanzu muyi sallah dan naga lokacin azahar tayi,bayan mun idar kuma inaso kuyi mun magana da waziri dasu galadima dan in sanarda su samun su fara shirye shirye kafin zuwa goben",suka ansa da "toh".
Jaheed neh yau kam ya taimaki baban wajen yin alwala kafin nan shima yyi nashi,Zeedat ma tayi nata sae dukansu sukayi sallah,Jaheed neh yaja su dan harya iya sallah yanzu kuma ya riqe surori har biyar a yau d'innan.Bayan sun idar sai suka fita Jaheed yaje yyi ma su waziri magana kan sarki na nemansu,bbu b'ata lokaci suka je,nayan sun gama tattaunawa sae Sarki yace da Jaheed gobe ya tabbatar Mud'allib yazo fada kafin a fara nad'in,Jaheed yace toh sannan yyi mishi sallama ya tafi..


漏Hama G Muh'd
 馃崄馃尶馃崄馃尶
          *MAFARKIN HAMAGEE 3*
                  馃尶馃崄馃尶馃崄

庐WISDOM OFFICIAL WRITERS 

*_In devotion to Sis Feedy_*鉂�



Page 044
    Bayan su Waziri sun bar sashen Sarki sae suka fara gulma wae ya akayi Sarki ya sauya maganar shi a yau d'innan,su a tunanin su yarima neh yaje yyi mishi magana dan sun san tabbas Sarki na jin maganar yarima amma dukda haka sunyi mamaki da sarki ya juya lokaci guda dan su a iya saninsu idan yyi magana baya canzawa.Koda suka kai wannan labarin ma Wahiyya,taji dd'i sosae sannan ta musu alqawarin zuwa gobe bayan anyi nad'in sarautar akwae wani babban aikin da zasuyi mata saeta biyasu harda sauran na baya da bata qarasa basu ba duk zata had'a musu.Sukayi godiya sannan suka bar wajen sae Wahiyya dake ta saqa da warwara kan yadda zata cimma burinta gobe.
  Tana cikin hakan Jaheed ya shigo,ya gaida ta sae yyi shiru be sake ce mata ci kanki ba,saeda ta gaji saeta ceh "lallae yau yarima ka nuna mun cewa ni Wahiyya ni nayi naqudar ka na bi na haife ka dan ka nuna mun yanzu kana bin abinda nake fad'a maka,da badan kaje ka samu mahaifinka kan batun sarautar nan ba da yanzu wa y'aruwarka za'a bada amma yanxu ka qwacen ma kanka y'anci",tayi wani murmushin mugunta,Jaheed kuwa kallonta kwae yake a ranshi yana tunanin wanda yazo ya fad'a mata cewa shi yyi wa sarki magana.Lallae su waziri munafukai neh dan kuwa tabbas bbu wanda yaji maganar nan sae su sae kuma Zeedat,amma tabbas su sukayi mata gulmar dan kuwa ba Zeedat bace, Jaheed ya fad'a a ranshi..


漏Hama G Muh'd
 馃崄馃尶馃崄馃尶
          *MAFARKIN HAMAGEE 3*
                  馃尶馃崄馃尶馃崄

庐WISDOM OFFICIAL WRITERS 

*_In devotion to Sis Feedy_*鉂�



Page 045
    Bayan Zeedat ta bar sashen Sarki kai tsaye tayi side d'insu,tana  shiga ta gaida mamanta bayan sun idar da sallah dan lokacin data shigo suna sallahn azahar,bayan sun gaisa saeta sanarda ita duk abunda ake ciki.Maman tayi farin ciki matuqa da musuluntar yarima,ba ita kad'ae bama harda Haima tayi murna sosae.
  Lokacin la'asar nayi Zeedat,Yaayi da kuma Haima suka nufa sashen Sarki danyi mishi alwala sae suyi sallahr acan dan in ba hakan ba bbu meyi mishi kuma bazae iya da kanshi ba gwanda ma idan ruwan na kusada shi toh yana iya lallab'awa dan hannunshi na dama yana aeki,bayan sun shigo sae Zeedat ta taimaka mishi yyi alwala lokacin kuma su Yaayi suna yin nasu,bayan ta gama saeta barshi yyi sallah itama tayo alwalan,bayan ta idar saeta ceh ita kam zataje ta d'an huta dan ta gaji,sukayi sallama sannan ta fita,Yaayi kuwa ta jima suna hira da Sarki daga baya har Haima ta tafi ta barsu.
 Ba wata hira bace kuma illa ta duniya.
Lokacin magrib nayi Zeedat da Haima suka dawo sukayi sallah tare kafin nan sukayi mishi sallama suka tafi,kafin yayi bacci ko yyi isha.
Jaheed ma dake shi kad'ae neh a sashen sa yyi sallolin shi hankali kwance.
Dukkanin su da tunanin gobe sukayi barci..



漏Hama G Muh'd

馃崄馃尶馃崄馃尶
          *MAFARKIN HAMAGEE 3*
                  馃尶馃崄馃尶馃崄

庐WISDOM OFFICIAL WRITERS 

*_In devotion to Sis Feedy_*鉂�



Page 046
   Niyad da Ja'i na hango a tsakar gidansu suna ta zuba drama,wae Ja'i ya siyo musu ragon suna neh dan yanzu haihuwar tazo kusa sosae dan yana iya zuwa yau koh gobe,shine Niyad take wannan shegen rigimar wae a dole saeya siya musu saniya koh raqumi dan ba zae yiwu ace shekara da shekaru basu tab'a haihuwa ba sae yanxu kuma ace ya sayi rago kad'ae,Ja'i yace "haba Niyad kowa ba daedae qarfinsa yake abu ba? Yanxu keh kanki shaida ceh a garin nan ba kowa yake ka da rago a suna ba,mafiya yawansu akuya ceh ko taure",a fusace Niyad tace "dakata Ja'i ban tambayeka abunda mutan gari sukeyi ba,kwae ina magana akan abunda ya dace muyi neh dan nuna banbancin mu dasu dan kuwa akwae,abunda yasa nace babanci kuwa shine su masu yanka akuya ko tauren ai kowacce shekara d'aya ko bibbiyu suke haihuwa,mu fa? Inace yanxu kimanin shekarun mu talatin da biyar kenan bamu samu haihuwar ba sae yanxu kuma ka cemun wae ga yadda y'an gari sukeyi",ta wani ja ta tsuke fuska,Ja'i yace "ba wae ina nufin semun yi yadda ya'n gari sukeyi ba,ina nuna miki cewa koda ragon muka yanka bbu meh ganin kashinmu neh"Niyad tace "Ja'i! Baka da wata magana da zaka mun fa tunda duk shekarun nan da muka d'iba bamu tab'a siyan koda kazar suna ba, toh lallae dole mu yanka sa ko raqumi dan yanzu yaci ace ka tanadin kud'in saboda baka tab'a haihuwa ba,idan kayi lissafin kud'in sayan akuyoyi na kowane bayan shekaru biyu tun auren mu ai yafi kud'in siyen raqumi ma",shidae Ja'i daya rasa yadda zaiyi da ita saeya bar gidan abunshi..



漏Hama G Muh'd
 馃崄馃尶馃崄馃尶
          *MAFARKIN HAMAGEE 3*
                  馃尶馃崄馃尶馃崄

庐WISDOM OFFICIAL WRITERS 

*_In devotion to Sis Feedy_*鉂�



Page 047
    Ja'i be dawo gidan ba saeda yasan yadda yyi ya samo saniya,aro yaje yyi? Siya yyi? Ko kuwa satowa yyi,ohoo ko Niyad batada wad'annan amsoshin tambayoyin ita dae kwae tayi murna da yin hakan.
  Da dare yyi Ja'i yaje ya nemo musu abunda zasu ci na daren,bayan ya dawo sukaci kafin nan suka kwanta bacci.
  Washegari tunda sassafe Niyad take jin ciwon mara,daga ji kuma tasan haihuwa ceh tazo mata saeta sanar da Ja'i.Shikuma Ja'in saeya je ya kira likitar garin wato matarda take karb'ar haihuwa,koda ta zo saeta sa Ja'i ya kawo mata duk abubuwan da zasu buqata daman sun kammala siyayyarsu tun cikin nada watanni shida.
  Suna zaune can sae naquda tazo ma Niyad gadan gadan,ko magana Niyad bata iyayi ta koma abun tausayi,koda likitar taga haka saeta maida Niyad d'aki da taimakon ta Niyad ta haihu,d'anta Namiji ta haifo gashi qato fari kyakyawa,Likitan tayi qoqarin gyarasu duka sannan ta gyara d'akin,Ja'i na shigowa kai tsaye ya nufa wajen Niyad da jaririnsa,murna wajen shi bbu magana,nan ya sallami likitar da kud'i me yawa saedae kullum zata ringa zuwa tanayi ma me jego da jariri wanka dan bbu meyi musu,tayi godiya tayi musu sallama ta tafi bayan ta sanarda su yadda zasuyi komai kafin zuwa gobe ta dawo..


漏Hama G Muh'd
 馃崄馃尶馃崄馃尶
          *MAFARKIN HAMAGEE 3*
                  馃尶馃崄馃尶馃崄

庐WISDOM OFFICIAL WRITERS 

*_In devotion to Sis Feedy_*鉂�



Page 048
    Bayan likitar ta tafi sae Ja'i ya tafasa ruwan zafi yasa a abun riqe zafi wanda Niyad zata ringa tsarki dashi kenan har zuwa goben,bayan ya gama saeya fita zuwa kasuwa,koda ya dawo da gashin nama ya shigo da yawa,ya kawo ya ajiye ma Niyad.
 Niyad taci gashin nan kamar bazata bar saura ba amma bbu yadda ta iya sada ta rage dan naman nada yawa sosae.Da dare yyi suka kwanta sukasa jaririn su a tsakiyar su suna wasa dashi har bacci ya d'auke su.
Washegari da sassafe Ja'i yaje ya hura wutan ruwan wanka Niyad da jaririnsu kamar yadda Likita tace,can likitan tazo tayi musu wankan ta gyarasu sannan ta duba lafiyarsu taga ba wani abu da yake damunsu saeta tafi abinta.
鈥︹€︹€︹€︹€︹€︹€︹€︹€︹€︹€︹€︹€︹€︹€︹€�
Haka suka cigaba dayi kullum saeta zo ta musu wanka har ranar suna.Yau da wuri tazo ta shirya su sae aka kwantar da babyn yana bacci,su kuma suka cigaba da shirye shiryen su.
  Rana tayi har an rad'a ma yaro suna *YUZRAN*,mutane y'an suna har sun fara cika a gida,kowa yana mamakin irin wannan suna dan basu tab'a ganin sunanda aka yanka Saniya guda ba irin wannan,ga abinci ishashe.
  Niyad ceh ta shiga d'aki domin d'auko jariri wa y'an suna su ganshi,koda ta d'aga shi sae taji jikin shi a sake,saeta kai kunnenta wajen hancin shi,ina shiru kke ji,ta d'aura tafin hanninta kan qirjin shi amma ina bbu rai,wani ihun data kurma neh yasa jama'a tururuwa a d'akin...



漏Hama G Muh'd
 馃崄馃尶馃崄馃尶
          *MAFARKIN HAMAGEE 3*
                  馃尶馃崄馃尶馃崄

庐WISDOM OFFICIAL WRITERS 

*_In devotion to Sis Feedy_*鉂�



Page 049
    *_Gidan Sarki_* 鈥⑩€⑩€⑩€⑩€⑩€⑩€⑩€⑩€�
Washegari da safe Jaheed ya nemi Zeedat suka je wajenda Zeedat suke had'uwa da Mud'allib,basu wani jima ba Mud'allib yazo dan dama sunyi akan yazo goben da wuri,bayan ya iso sae suka gaisa sannan suka nufa gida tare.
   Sarki na kwance sukayi sallama ya ansa sae suka shigo bayan ya basu umarnin shiga.Ko wannan su ya nemu guri ya zauna,Sarki neh ya fara magana "godiya da dukkan wani yabo ya tabbata ga ubangiji Allah,ina miqa mishi godiyata daya kawo mu wannan lokaci,kuma ya sauya mana rayuwa acikin qanqanin lokaci,kaima kuma ina maka godiya daka shiga rayuwar y'ata harya zamanto mun gano hanyar gaskiya kuma mun bita duk ta sanadiyyar ka,keh kuma Zeedat bbu abunda zance dake da kuma d'an uwanki sae Allah yyi muku albarka"dukansu suka ceh "ameen".Sarki ya cigaba "dalilin da yasa na taraku anan shine,na farko yau za'a rad'a sabon sarki a garinnan saboda haka nake kira gareka yarima,daka kwatanta gaskiya da adalci a mulkin ka,kuma ka tsara komai a hanya mafi gaskiya da dacewa dan haka nake so ka nad'a Mud'allib wazirin ka kuma limamin garin nan sannan ko bayan raina ban yadda ka bijirewa umarnin sa ba dan kuwa tabbas nasan ba zae saka a turba ta banza ba,na biyu kuma inaso ana gama nad'in nan a d'aura auren Mud'allib da Zeedat,aure kuma na har abada,idan kka sab'a umarnin mijinki Zeedat toh ki tabbatar da cewa ban yafe miki ba,na uku kuma gareka neh Mud'allib,na baka amanar y'ayana biyun nan da Allah ya mallaka mun idan,ka sani idan kaci amana toh lallae amana bazata barka ba.Daga qarshe nake cewa Allah ya had'a kanku baki d'aya ya kuma baku zuri'a ta gari sannan yasa kuci nasara wajen ceto rayuwar al'ummar garinnan",suka ceh "ameen",kowannen su ya d'au mishi alqawarin cika dukkanin abunda yace suyi,daga qarshe suka mishi sallama suka bar d'akin.



漏Hama G Muh'd
 馃崄馃尶馃崄馃尶
          *MAFARKIN HAMAGEE 3*
                  馃尶馃崄馃尶馃崄

庐WISDOM OFFICIAL WRITERS 

*_In devotion to Sis Feedy_*鉂�



Page 050
    Bayan sallahr azahar aka d'aura yarima kan karagar mulki,bayan an gama hidindimu sae Mud'allib ya koma garinsu akan gobe zae dawo da y'an uwanshi sae a d'aura musu aure da Zeedat.
Bayan an gama komai sai Waziri da galadima suka je sashen Wahiyya dama tace anjima suzo tana neman su,suna zuwa ta fito ta samesu.Wasu y'an maganganu sukayi kafin nan ta sallame su suka tafi cikin murna dan ba kad'an ba ta basu abun arziqi kuma tace zata qara musu.
___________________________________
Ana yin sallahr isha'i Sarki yyi bacci dan a gajiye yake sae dae yana murnar burin shi ya cika tunda ya shaida magajin shi saura auren y'arsa wato Zeedat wanda ake sa ran d'aura shi gobe in Allah ya kaimu.
  Kamar a mafarki yaji mutane a kansa dan haka yyi saurin tashi dan ganin abunda yake faruwa,da bud'e idon shi sae yyi ido hud'u da Waziri da galadima sae sarkin fada kowan nensu bbu idon rahama a fuskar shi.Waziri neh riqe da adda ya sa a wuyan Sarki tareda mishi kashedin idan ya sake yyi musu ihu saeya fille mishi kai kafin lokacin yin hakan yyi,"Gimbiya Wahiyya wato amaryar ka,ta aiko mu nan dan mu qarasa ka dama ita ta nakasa ka idan baka manta,toh shine muke so muji ko kanada saqon da zaka isar mata kafin mu aika da kai" inji Waziri,Sarki dake ta b'ari yana addu'oi yace "bbu komai saedae ina roqon ku daku bani wata dama"Waziri yace "hanzarta damar miye?" Sarki yace "ina so ku bani takarda dan yin wata y'ar wasiyya ga y'ay'ana kuma inaso ku basu hannu hannu kar ku bama wani ko wata idan basu bane"Sarkin fada yace "an gama amma ka tabbatar baka rubuta musu wani abu da zae gane muna da hannu akan wannan kisa ba",Sarki yace yyi alqawarin hakan dan haka suka kawo mishi takarda,alqalami da kuma tawada a cikin wata roba qarama,suka taimaka mishi ya tashi ya zauna sannan suka damqa mishi kayan rubutun,saeya fara rubutu kamar haka:



漏Hama G Muh'd

馃崄馃尶馃崄馃尶
          *MAFARKIN HAMAGEE 3*
                  馃尶馃崄馃尶馃崄

庐WISDOM OFFICIAL WRITERS 

*_In devotion to Sis Feedy_*鉂�



Page 051
    *_Assalamu alaikum,daga farko dae ina me baku haquri kan mummunan labari da zaku iske amma ina so kuyi haquri kuma kuyi ta mun addu'a ko zan samu rabauta a ranar gobe kiyama.Bayan nan ina so na muku magana kan riqo da addininku sannan kada ku bijire mishi koda na qanqanin lokacin.Kai yarima ko ince Sarki inaso kayi mulkinka bisa addinin musulunci,kuma duk wani hukuncin da zaka zantar ya kasance haka addini ya tanadar,kayi mulkin ka bisa amana da jin qai kuma ka tabbatar dukkan al'ummar mu sun karb'i wannan addini.Keh kuma Zeedat,ina so ki zauna da mijin ki lafiya,yi nayi bari na bari shine kad'ae hanyar samun aljannar ki,Allah yasa mu dace ya kuma baku ikon riqo da gaskiya._*
            _Bissalam_
Bayan ya gama saeya nad'e ya ajiye a inda yasan zasu gani,su waziri dake jira ya gama suka ceh ya gama yace eh,a take a wajen ya fille mishi kai,shi kuwa Sarkin banda kalmatush shahada bbu abunda yake yi har yaji kanshi ya bar jikin shi dan sunkuyar da kanshi yyi a lokacin,koda suka gama aikinsu sae sukayi sauri suka bar d'akin kowannen su ya koma makwancin shi.Sarki kuwa jikin shi duk jini neh inda gangar jikin sa yake gefe haka kanshi ma gefe guda yake,jini duk ya rufe fuskar shi.(Allah ya jiqan shi nace sannan na bar d'akin)..



漏Hama G Muh'd
 馃崄馃尶馃崄馃尶
          *MAFARKIN HAMAGEE 3*
                  馃尶馃崄馃尶馃崄

庐WISDOM OFFICIAL WRITERS 

*_In devotion to Sis Feedy_*鉂�



Page 052
    Washegari da safe Jaheed da Zeedat suka fara shirye shiryen d'aurin auren,bbu wanda yasan da auren sae su sae maman Zeedat da Haima,suna cikin haka suka ji ana shela cikin fada wae an kashe Sarki a d'akinshi cikin dare kuma bbu wanda ya san su waye neh.
   A hanzarce suka nufa wajen,suka taradda gawar Sarki kwance a gaban bayin shi sunata rusar kuka,Jaheed yyi qarfin hali yace dasu su daena mishi kuka ba'a kuka haka wa mamaci sae dae ayita mishi addu'a,dukkan su saeda sukayi mamakin maganganun yarima na cewa wae suyi mishi addu'a dan su basu san wannan ba (Allah mun gode maka kuma ka raba mu da jahilci a duniya da lahira).
 Zeedat kam gabaki d'aya ta rasa na cewa,jikinta duk yyi sanyi a ranta tana tunanin wanda ya aikata wa ubansu wannan aika aikan.Da qyar suka bar gawar baban bayan sunyi mishi addu'oi.
 Har an d'auki gawar za'a a birne bayan matan shi duk sun ganshi,kwatsam saega Mud'allib sun shigo da y'an uwan shi,yace a dakata sae anyi mishi wanka an sallace shi,kowa ya tsaya yana mamakin abunda ya fad'a.Saeda aka mishi wanka sukayi sallahn gawa da taimakon y'an uwan Mud'allib d'in sannan suka kai shi makwancin shi,bayan sun sae Jaheed yace za'a iya d'aura auren yanxu sannan bayan an d'aura za'a bashi Waziri da kuma limamin gari sannan sae a fara aikin yad'a muaulunci a garin,amma kafin nan sae an gano wanene silar mutuwar Sarki,Waziri,galadima da kuma sarkin fada duk idonsu saeda ya raina fata,Mud'allib yace "da zaka bar maganar d'aurin aure da nad'innan sae zuwa nanda kwana biyu zuwa uku daya fi saboda a gano wanda yyi wannan kisar kuma a yanke mishi hukunci daedae da abunda ya aikata",Jaheed da jin hakan saeya ceh "ai duk yadda kace daedae neh,toh sae a bari sae bayan kwana ukun sannan daga yau za'a fara bincike",Mud'allin da y'an uwan shi duk suka goyi bayan hakan akan bayan kwana uku zasu dawo..


漏Hama G Muh'd
 馃崄馃尶馃崄馃尶
          *MAFARKIN HAMAGEE 3*
                  馃尶馃崄馃尶馃崄

庐WISDOM OFFICIAL WRITERS 

*_In devotion to Sis Feedy_*鉂�



Page 053
  Bayan nan sae Jaheed da Zeedat sukayi musu rakiya suka tafi.Zeedat da Jaheed bayan sun dawo kai tsaye sukayi sashen Sarki,masu aikin suka yima tambayoyi kan waye na qarshen shiga d'akin sukace tunda suka bar d'akin bbu wanda ya sake shiga kuma basu ji motsin kowa ba da daddare,ran Jaheed yyi mugun baci dan a ganinshi sakacin su neh yyi yawa da suka zauna bacci basu san wanda ya shiga ba,Zeedat ceh tace "lallae shigowa akayi aka kashe shi,kun zauna kuna barci baku ma san wanda suka shigo ba,an san baku isa ku hana a kashe shiba amma ae da kuna lura da abunda keh wakana da kun gano wanda yyi wannan kisan",haquri suka soma basu su kuma suka wuce suka barsu a wajen,d'akin Baban suka nufa inda sukayi ta dube duben su ko Allah zaisa su gano wani abun,suna cikin haka Zeedat taci karo da wata takarda a tsakankanun shimfid'ar Baban,ta zaro takardar sannan tayi ma Jaheed magana "zo ka gani Jaheed",Jaheed yyi maza ya qaraso inda take yana fad'in "meh kka samu?",nan ta ware musu takardar suka bi suka karanta,kowannen su saeda yyi kuka saboda tsananin tausayin Baban,Zeedat tace "amma wannan wane irin azzalumi neh,harya jirashi yayi wannan rubutun kuma ya kashe shi,kai mutanen mu basuda imani",Jaheed yace "insha Allahu wanda yyi wannan abun saeya shiga hanu kuma bbu makawa hukunci saeta hau kanshi koma waye shi"..


漏Hama G Muh'd
 馃崄馃尶馃崄馃尶
          *MAFARKIN HAMAGEE 3*
                  馃尶馃崄馃尶馃崄

庐WISDOM OFFICIAL WRITERS 

*_In devotion to Sis Feedy_*鉂�



Page 054
   Bayan sun d'anyi jim na wani d'an lokaci,sae suka cigaba da binciken su,can Jaheed yaci karo da wani zobe,ya d'auko ya nuna ma Zeedat suka qare mishi kallo,Zeedat tace "bbu makawa wannan zoben sarauta ceh,ya zamo cewa a cikin fadawan gidannan neh wani ya shigo d'akin nan,kuma ga jini a jiki,tabbas sae mun nemo meh wannan zoben saboda a cikin gidan yake",Jaheed yace "wannan haka yake,kuma da gani na babban bafade neh dan su kad'ae ake mallakawa irin wannan abubuwan".Bayan sun gama tattaunawa sae suka yanke hukunci anjima a fada za'a tara dukkan fadawan gidan sae a tabbatar da zoben waye,a haka suka rabu Jaheed yyi sashen shi ita kuma tayi nasu sashen inda ta sanarda Maman ta komai,Maman tace "Allah ya tona asirin wanda yyi kisan",Zeedat da Haima sukace "ameen".Bayan sun gama jimamin suka tashi sukayi alwala sukayi sallahr azahar.Jaheed ma sallahr yyi a sashen shi.
   Bayan tafiyan su Mud'allib sae su Waziri suka jeh suka samu Wahiyya suka sanarda ita abunda ake ciki,Wahiyya tayi musu alqawarin zata hana Jaheed yin binciken dan idan harya gano toh lallae kashin su ya bushe,sae sannan su Waziri suka d'an ji sanyi a ransu saedae maganar da Jaheed yyi na cewa za'a nad'a Mud'allib Waziri yana damun Wazirin,amma ya bar maganar tukunna sae an kashe wancen maganar kafinnan ya d'ago wannan..


漏Hama G Muh'd
 馃崄馃尶馃崄馃尶
          *MAFARKIN HAMAGEE 3*
                  馃尶馃崄馃尶馃崄

庐WISDOM OFFICIAL WRITERS 

*_In devotion to Sis Feedy_*鉂�



Page 055
    Wahiyya ta rasa ta yadda zata fara tunkarar Jaheed da batun ya janye bincike akan wanda ya kashe ubanshi,saedae bbu yadda ta ita dole ta san duk hanyar da zata bi dan hanashi aiwatar da binciken,dan haka ta tashi kai tsaye ta nufa sashen Jaheed d'in.
 Jaheed ya idar da sallah kenan bayan yyi addu'oi yana tunanin me zoben nan saeya ji muryar mamanshi dan haka yyi saurin miqewa ya nufa qofar d'akin ya bud'e mata ta shigo,tana kallon shi taji nikinta yyi wani irin sanyi ta rasa ta inda zata fara mishi magana,Jaheed ya lura da yanayim da ta shiga ciki dan haka ya tambayeta "ya dae na ganki haka?kinada wata matsala neh?",jin ya fad'i hakan yasa Wahiyya tayi amfani da wannan lokacin tace "bbu Jaheed kwae tunanin mahaifin ka nakeyi,ina tausaya mishi kan irin wannan kisa da akayi mishi",Jaheed yace "ki daena damuwa mama,insha Allah zae samu rahamar ubangiji",Wahiyya da bata fahimci abunda ya fad'i ba tace "ban fahimce ka ba",Jaheed yace "ba wani abu",Wahiyya tace "shi kenan,amma kasan miye?",yace "a'a",tace "ina ganin ya kamata ka janye maganar bincike da kke sonyi na mutuwar babanka,muji kwae da rashin da mukayi,bana so garin binciko wani abun a janyo wata babbar matsalar saboda haka yadda muka haqura kaima ya kamata ka haqura kwae dan ba gano komai za'a yi ba",ta wani sunkuyar da kai qasa alamar kuka yaci qarfinta,Jaheed ya matso kusada ita ya d'an kwantar da kanta a jikin shi yana lallashin ta sekace y'ar shekara 5..


漏Hama G Muh'd

馃崄馃尶馃崄馃尶
          *MAFARKIN HAMAGEE 3*
                  馃尶馃崄馃尶馃崄

庐WISDOM OFFICIAL WRITERS 

*_In devotion to Sis Feedy_*鉂�



Page 056
    A ranshi yana mamakin yadda akayi taji wannan maganar tunda bata wajen akayi kuma a iya tunanin shi bbu wanda zae fad'a mata a wajen,yace lallae akwae wani abu dake gudana wanda bamu san dashi ba,yyi gyaran murya bayan ya gama tunanin da yake sae yace "karki damu daga yanxu ma na daina",wani dariyar da Wahiyya ta sakar neh yyi mugun d'aure mishi kai,wae ace a kashe mijinta amma bata damu da sanin wanda ya aikata kisan ba saima so da takeyi a rufe maganar kuma har murna takeyi dan yace ya janye,lallae akwae wata maganar a qasa saedae ya barwa kanshi sanin hukuncin da ya yanke a kan hakan.Yyi murmushi shima yace "ina shikenan,hankalinki ya kwanta?",tace "eh,haqiqa ka nuna mun cewa inada iko akanka kuma zaka bi maganata akoda yaushe",yace "hakane mama",ta tashi ta miqe ta tafi tana me murna.Koda ta koma sashenta saeta saka aka kira mata su Waziri sannan ta sanarda su yadda sukayi da Jaheed d'in,suma sun d'an samu relief saedae har yanzu waziri na cikeda damuwar maganar Jaheed ta cewa za'a nad'a sabon Waziri,ya d'an nisa yace "ni dae har yanxu hankali nah ba'a kwance yake ba na cewa za'a nad'a sabon waziri",Wahiyya tace "damuwarka kenan? Toh bakada damuwa ana maka wannan maganar kai kana wata,ae indae muka samu wannan magana ta ruhu toh munyi meh wuyar daga baya ayi maganar nad'in,sannan kasan a yanzu idan na mishi maganar nad'in toh dole yyi tunanin wani abu a tsakanin mu",dukkansu sunaji suna girgiza kai alamar gamsuwa,daga bisani sukayi mata sallama suka tafi.Farin ciki gun Wahiyya ba'a magana.
  Bayan fitar Wahiyya Jaheed yyi ta jin mamakinta,meyasa bata son a gano wanda ya kashe baba? Meyasa daga jin nace na fasa ta fara murna jikinta na rawa?,duk wannan tambayoyin a zuci Jaheed yyi su,yyi maza yyi nafila raka'a biyu saeya roqi Allah ya gafarta mishi qaryar da yyi ma mamanshi,dan bazae iya yin yadda takeso ba,dole ya gano wanda ya kashe mishi baba.Bayan ya idar ya kwanta a haka har yyi bacci..


漏Hama G Muh'd
 馃崄馃尶馃崄馃尶
          *MAFARKIN HAMAGEE 3*
                  馃尶馃崄馃尶馃崄

庐WISDOM OFFICIAL WRITERS 

*_In devotion to Sis Feedy_*鉂�



Page 057
    *Gidan Niyad*
Mutane suka cika a d'akin kowa na tambayar ta lfya,bata iya basu ansar tambayarsu saedae kukan da ta cigaba dayi,ganin babyn kwance yasa wata ta tsuguna ta d'auko shi,a kid'ime take fad'in "yah mutu,wayyo d'an yah mutu",nan da nan gidan suna ya koma na makoki,masu farin ciki da masu taya murna suka koma baqin ciki da tausaya wa Niyad,lallaminta sukayi tayi masu kuka kuma nayi.Bayan Ja'i ya dawo aka sanarda shi,yyi baqin ciki kwarae da gaske,shi yanzu ma babban damuwar shi shine yadda ya karb'o bashin saniyar suna gashi baida kud'in biya,kuma gashi har an yanka yanzu ya zamo asara kenan,wani irin takaicin Niyad yaji saboda ita ta tursasa shi ya karb'o.
   *Gidan Sarki..*
Washegari Sarki (wato Jaheed)ya tara dukkan fadawan gidan dan qarasa binciken da yakeyi,nan ya gano cewa wannan zoben na Waziri neh,Jaheed be nuna cewa ya gane komai ba kan kisar baban shi saedae a ranshi yana tunanin yadda zaeyi ya tunkari waziri da batun ko yanada wata masaniya kan batun.Bayan an watse da yamma Jaheed da Zeedat suka yanke shawarar tunkarar waziri tare dan dama Jaheed ya sanarda ita duk yanda akayi d'azu,bayan sun gama tattaunawa sae suka nufi wajenda waziri ke zama suka samesu tareda Galadima da sarkin fada kuma daga gani suna tattaunawa neh kan wani abu me muhimmanci ganin yadda fuskarsu ta nuna.Suka qarasa suka mishi magana,gefe suka jashi kafinnan suka fara mishi tambayoyi kan ta yaya akayi zoben shi yaje d'akin sarki,nan da nan jikin shi ya soma rawa ya qago wasu qarerayin shi ya fad'a musu.Sukayi sukayi dashi cikin hikima ya fad'a musu yadda akayi amma firr waziri yaqi kuma daga maganganun shi sun gano cewa sarae yanada masaniya kan kisan shiyasa suka qi barin shi.
  Saeda waziri yaga fushin jaheed sosae tukunna ya yarda ya fad'i gaskiya tunda ga kan nakasan sarki da mutuwar Aina har zuwa mutuwar sarki,tas ya kwashe ya fad'a musu dan sun mishi barazanar mutuwa sunce indae be fad'i gaskiya ba toh lallae zasu kashe shi..


漏Hama G Muh'd
 馃崄馃尶馃崄馃尶
          *MAFARKIN HAMAGEE 3*
                  馃尶馃崄馃尶馃崄

庐WISDOM OFFICIAL WRITERS 

*_In devotion to Sis Feedy_*鉂�



Page 58
   Sun shiga cikin tashin hankali ba kad'an ba barin ma Jaheed da ya kasance mahaifiyar shi ceh tayi komai.Waziri kuwa yyi nadama sosae saedae *it's too late to cry...*
   Bayan kwana biyu,kwanaki uku sun cika cif,Mud'allib suka dawo shida y'an uwanshi,anyi musu tarba da kyau daga bisani aka d'aura auren su da Zeedat daman duka b'angare biyun a shirye suke.Bayan an kammala komai aka nad'a Mudallib Waziri tareda niyyar neman way'anda suka cancanta sae a basu galadima da kuma sarkin fada,bayan an gama hidindimu sae y'an uwan Mud'allib suka tafi da niyyar shikuma zae je daga baya tareda Zeedat d'in.
  Koda aka sanarda Mud'allib rabarin da waziri ya bayar saeya ceh hukuncin daurin rai da rai neh akansu,saboda haka Sarki yasa aka zo mishi dasu waziri dama tun ranan yasa aka kullesu saboda karma su fad'a wa mamanshi abunda ake ciki,koda suka zo sae Mud'allib yyi qoqarin musuluntar dasu,amma fir suka qi,dan haka bbu bata lokaci akayi musu hukunci daedae da laifinda suka aikata.
  Wahiyya dajin wannan labari tayi hauka,haka aka d'aukota aka kaita gidan yari amma sashen mahaukata.Jaheed yyi baqin cikin abunda ta aikata ba kad'an ba saedae kuma bbu yadda ya iya kuma hukunci dolene akanta dukda cewa itace ta haife shi,bbu yadda ya iya haka yyi tawakkali ya dogara ga Allah sannan idan ya tuna yanada Zeedat da kuma Mud'allib,sae yaji damuwar shi ta ragu dan Mud'allib ya zamo mishi kamar jini yanzu,bama shi kad'ae ba har ita Zeedat d'in shiysa take qara sonshi koda yaushe...


漏Hama G Muh'd
 馃崄馃尶馃崄馃尶
          *MAFARKIN HAMAGEE 3*
                  馃尶馃崄馃尶馃崄

庐WISDOM OFFICIAL WRITERS 

*_In devotion to Sis Feedy_*鉂�



Page 059
    Bayan wasu y'an kwanaki,Allah yyi wa Wahiyya rasuwa,Jaheed yaji baqin ciki mara misaltuwa daya kasance ta mutu ba'a musulma ba saedae bbu yadda ya iya da ikon Allah,Zeedat,Mud'allib da kuma Yaayi da Haima sune sukayi ta lallamin shi suma sun tausaya mishi sosae da sosae.
  Bada jimawa ba suka fara aikin yad'a addinin musulci ma jama'a,saedae abun haushi bbu dayan su daya kula hasalima cewa sukeyi sarki na neman ruguza rayuwarsu da suka samo shi tun kakanu da iyaye,sunyi sunyi har sun gaji dasu,saedae sun d'au niyyar cika wannan alqawari da sukayi wa kansu na yad'a addinin.
  Bayan kwana biyu,Mud'allib ya d'auki Zeedat suka tafi garinsu da niyyar zasuyi kwana d'aya sae su dawo,zae kaita ganin dangin shine.
 Bayan tafiyarsu Jaheed baya jin dad'i kwata kwata,Yaayi ceh kad'ae me d'ebe mishi kewa dan yanxu ya riqeta kamar mahaifiya harma yana jin da ita ceh ta haife shi tun farko.
Washegari da safe,Jaheed na zaune a fada suna tattaunawa da Yaayi kan yadda zasu fuskanci al'amarin,sae wani bafade ya shigo yace dashi yyi baqi,Jaheed yace ace dashi ya shigo..


漏Hama G Muh'd
 馃崄馃尶馃崄馃尶
          *MAFARKIN HAMAGEE 3*
                  馃尶馃崄馃尶馃崄

庐WISDOM OFFICIAL WRITERS 

*_In devotion to Sis Feedy_*鉂�



Page 060
    Bafadennan ya fita yace da baqin su shiga sarki yace su shigo,koda suka shigo sae suka gaida shi cikin girmamawa kamar yadda akeyi wa sarki,Sarki yace "meke tafe daku?",d'aya daga cikinsu ya fara da cewa "haqiqa munyi nazari munyi tunani kan maganar da kai mana ranan,kuma mungano cewa addinin nan naku abun bi ne saboda da muka duba irin rayuwar da akeyi da a gidannan da kuma wacce ake yinta yanzu ba d'aya suke ba,da ana mulkin zalunci da son kai amma yanzu bbu wannan kuma da duk abunda sarki yaga dama ayi yinshi akeyi koda be dace ba amma yanzu gashi nan addini kke so ka koyarda mu amma baka tilasta mana ba,sae ma neman zab'inmu da kayi,saboda haka nida wanban d'an uwan nawa mun yarda munaso mu shigo cikin addinin koda kuwa zamu qarar da dukkan dukiyoyin mu neh",wani farin cikine ya ziyarci zuciyar Jaheed da Yaayi wanda basu tab'a shiga cikin shi ba,Jaheed yace "lallae naji dad'in wannan magana taku amma ku sani cewa ba'a biyan komai kafin a shiga cikin wannan addinin",nanda nan Jaheed ya musuluntar dasu.
  Bayan nan sae mutanen suka sanarda su cewa ae basu kad'ae bane akwae wasu a waje,yawansu yafi qarfin su shigo a tare shiyasa suka jira a waje yanzu suma sae aje a musuluntar dasu.Jaheed sunji dd'i sosae dan haka bada jimawa ba suka nufa waje inda suka ga mutane bila adadin,nanda nan suka karb'i musulunci suma,fadawan gidanma duka suka shiga,ranan dae tare sukayi sallahr azahar.
  Bayan sallahr suka zauna Jaheed yyi ta ilimantar dasu way'ansu abubuwan da ya kamata su sani as *muslims*, suna cikin haka su Mud'allib suka dawo,suma sunyi murnar taran wannan labari me dad'i.Haka rayuwarsu taci gaba kullum a jam'i sukeyin sallah matan kuma a gidajensu sukeyi,a kwana a tashi kuwa dukka y'an garin suka musulunta illa su waziri wanda har yanzu suke gidan yari.
  Rayuwar Niyad kuwa tuni ta sauya dan yanzu ta daena duk abunuwan da takeyi,suma sun kama addini bbu sanya...


Anan na kawo qarshen wannan littafi me taken suna *MAFARKINA*,sae mun sake had'uwa a littafina na gaba wato *UNIVERSITY GIRLS* wanda already na fara rubuta shi,saqon gaisuwata ga dukkanin masoyana na fili dana b'oye,wanda na sani da wanda ban sani ba,Allah ya had'a mu a darussalam..Assalamu alaikum!!


漏Hama G Muh'd
Share:

No comments:

Post a Comment

Popular Posts

Translate

Archive

featured post

UNIVERSITY GIRL Final episode(Chapter thirty)

Powered by Blogger.

Contact Form

Name

Email *

Message *

Blog Archive