This site offers you with different novels series from one writer, I hope this will educate and as well as entertain you..

ALHAKI NEH! (Page 9)

🌸🦋🌸🦋🌸🦋🌸🦋🌸

*ALHAKI NEH!*

🌸🦋🌸🦋🌸🦋🌸🦋🌸🦋

® *_REAL PURE MOMENT OF LIFE WRITERS_*

_ɯɛ ɖơŋ'ŧ ơŋٳყ ɛŋŧɛřŧąıŋ ŋɖ ɛɖųĆąŧɛ, ცųŧ ɯɛ ąٳŞơ ŧơųĆɧ ŧɧɛ ɧɛąřŧ ơʄ řɛąɖɛřŞ_

By the applomb writer: *Hamagee*

Jan,2018.

# WWW.PMLWRITERS@GMAIL.COM
# IG PML WRITERS
# https://www.facebook.com/PML_-Writers-FANS-459256761123035
# http://maryamsbello.blogspot.com

Wattpad @Hama_gee

Page 09

°
Bayan wata guda hutun su ya k'are,so basu yi wasting time ba soka koma school suka cigaba daga inda suka tsaya. Kwanaki nata wucewa,soyayya da shak'uwa nata k'aruwa a tsakanin su. Kowa yasan Aminu a gidansu Amina,jira yakeyi ya kammala degree d'inshi kafin ya sanar a gida.

2yrs ltr...
Aminu ya auri Amina,suna zaune a nan Bauchi cikin kwanciyar hankali da samun nutsuwa a tsakani. Rayuwar su abin birgewa ce ga wanda ya gani. Yanzu Amina na 300 level kuma Alhamdulilah tana fahimtar karatun sosai,duk wani abinda ya shige mata duhu tana kawo ma Aminu,shi kuma sai yayi guiding d'inta.

Akwai wani hali guda na Aminu da Amina bata so ko kad'an,sai dai tayi-tayi dashi amma abin kamar yafi k'arfinta dan ya kada canzawa. Ba wani hali bane wannan illa halin rashin kulawa da iyayenshi,kwata-kwata bai damu dasu ba,baya wani zuwa dubasu while they so much need him this moment because sun fara tsufa,bayan nan basuda wani d'an bayan shi. Wannan shine babban damuwa a wajen Amina yanzu.

Yau suna zune a palour suna kallo bayan sallahr isha'i,Amina ta dubi Aminu cikeda kulawa ta kira sunanshi kamar yadda ta saba kira "hobby" ,Aminu ya amsa mata "na'am" tareda juyo kanshi gareta. Tace "yaushe zamu je gaidasu Umma kaga har mun kusada yin shekara guda da yin aure,kuma hakan bai kamata ba ace suna raye amma kwata-kwata baka kula da hidimarsu". Aminu ya maida kallon shi ga tv inda suke kallon wani Nigerian film a African magic Igbo. Saida ya d'anyi nazari kad'an kafin yace "nifa kin kasa gane mun ne kawai,amma ba wai bana son kula da hidimarsu bane,abin ne sai a hankali dan haka na taso babu wani sabo a tsakanin mu,even though ina iyaka k'ok'ari na tunda nake tare dake wajen ganin na gyara hakan".

Amina tace "to Allah ya kyauta,yanzu yaushe zamu je mu duba su?",yace "randa kike so ni yayi min amma ni bawai ina wani son zuwa bane dan bana musu kallon iyayena ma",da sauri Amina ta rufe mishi baki kafin tayi magana "haba don Allah,meyasa kake yin hakane? Iyayenka kake cewa baka musu kallon iyaye?",Aminu ya d'aga mata kai alamar eh,idon shi cikin nata babu ko k'yaftawa,ga hanunta a kan bakinshi.

Tasowa tayi daga k'asa ta dawo kan cinyarshi ta zauna tana shirin yin kuka,babu shiri ya gyara yace mata "kiyi hak'uri to me kike so inyi miki?",tace "kasa mana ranar da zamu je gaidasu Umma",cikin shagwab'a tayi maganar,shikuma da rawar jiki yace "angama,jibi zamu iya zuwa". A rayuwar shi baya son ganin b'acin ranta dan haka zai iya hak'ura da duk wani farin cikin shi dan samun nata.

Amina taji dad'in hakan sosai sannan tana rok'on Allah ya bata sa'a kan abinda take cimmawa. Tace "nagode hobby na" tareda hugging nashi,shima hugging d'inta yayi suna jiyo numfashin juna,ganin salon su na shirin saiyawa yasa na tattara takadda da biro na na waske🏃🏻‍♀️..

***
Washegari ta kama shirye-shiryen zuwa garinsu Aminu gaida iyayen shi. Ta sanar ma mahaifiyar ta,mahaifiyar tasa mata albarka tareda musu fatan alkhairi sannan tace mata ta k'ara dagewa da abinda take shirin yi dan aikin lada ne babba kuma Allah ya taimaka,daga k'arshe tace ta gaida mata Aminun kafin tayi hanging.

Aminu taji dad'i sosai tareda k'ara samun k'arfin gwiwa akan nada,sannan tayi alk'awari ma kanta na cewa duk rintsi duk wuya saita cimma burinta na had'a kan mijinta da iyayenshi,daga k'arshe take rok'on Allah ya bata nasarar yin hakan da kuma juriya da hak'urin yin hakan dan babban aiki ne..

   hghausanovelseries.blogspot.com

Share:

No comments:

Post a Comment

Popular Posts

Translate

Archive

featured post

UNIVERSITY GIRL Final episode(Chapter thirty)

Powered by Blogger.

Contact Form

Name

Email *

Message *

Blog Archive