[7:20pm, 3/30/2017] Hamagee: 💦 💦💦💦 💦
*LAIFIN WAYE??*
💦💦💦 💦💦💦
_Written by the Aplomb writer: *Hamagee*_
*Marriage is that relation between man and woman in which tha Independence is Equal,the Dependence mutual and tha Obligation Reciprocal".* *Best wishes for Happy Wedding Anniversary..* *May the love that you share lasts a lifetime and may you accomplish all the dreams that you have entwined together!*
*A very happy Wedding Anniversary to a wonderful couple!* *@ _sweety Billy Galadanci aka Mom Nu'aim_,Luv u loads sweethrt...* *This page goes to you* 🙌🏽
💦💦
Page 01
Wata budurwa ceh zaune kan dressing mirror tana tsara kwalliya kamar me zuwa gasar sarauniya,kyakykyawa ceh bata wasa ba,wanda kyan nata ya dace da sunanta wato *Suhana*.Suhana kyakkyawa ceh son kowa qin wanda ya rasa,nima kaina dana ganta saida na kusa tuntub'e tsabagen kyonta,gata fara tass.
Banji mamaki bama saeda ta tashi daga kan stool dinda take zaune na gaban dressing mirror d'in,doguwa ceh saedae ba can ba,batada jiki ko kad'an,saedae irin qirar coca-kolan nan ceh,to save your time,babyn ta had'u..
Bayan ta gama shirinta saeta d'au wayarta ta fito palour,inda ta tararda Mamanta zaune tana faman canza channel d'inda take kallo,ae tuni Maman ta tsaya tana qare ma y'artata kallo,kirari ta shiga mata kamar yadda ta saba yi mata a kullum "Suhana kenan,kin cancanci sunanki d'iyata,son kowa qin wanda ya rasa..Uwar mata lantarkin gida kenan,bani bada ki sae ma millionaire koma ince billionaire dan wannan kalar taki bata zaman ko'ina bace illa ta zaman palour,Suhana sarauniyar mata,kowa ya ganki dole yyi kishi,jaa zamaninki".
Koda Suhana ta gaji da wannan surutun maman nata,saeta ceh "ohh,isn't it ohk Mommy,na gaji da wannan zigarkin nikam",Maman tace "toh ae yabon gwani ya zamo dole,kin san hausawa sukan ceh 'so sone,amma son kai yafi',so kinga idan ban yabi nawa ba wazae yaba mun?"ta qare maganar tana me zurawa Suhana dake shirin qarasowa idanu..
Suhana tayi wani murmushin dake qara mata kyau,ga dimples d'innan tabarkallah,sun wani lotsa ciki,infact,her beauty is an extraordinary one.Ta kalli maman tace "gaskiyarki neh Mommy,gwanda mutum ya yabi nashi dan bbu me yabon mka shi..shiyasa nake sonki Allah",Maman tayi smiling tareda fad'in "that's my girl"..
Suhana ta karb'i remote d'in hannun Maman ta canza Sate d'in zuwaga INFINITY,inda ta shiga channel na *Joyprime*.Nan suka cigaba da kallon su cikeda jin dad'i.
Ba'a jima ba gateman nasu yyi sallama,suka ansa.Suhana ceh ta tashi taje dubawa,koda ta bud'e qofar sae yace da ita "wae ana magana dake neh a waje",Suhana ta wani b'ata rai tareda fad'in "ni kuma??",gateman d'in yace "eh,haka yace",Suhana ta d'anyi jim kad'an sae kuma tace "amma a iya sanina ba wanda yace mun zaizo guna yau,by the way ma meyasa bazae kiran ba,anya kuwa ka tabbatar ni ake nema??".
Gateman d'in ya d'aga kai alamar eh,Suhana tace "let it be,ina fitowa",nan ta koma cikin gida ta sanarda Mommynta yadda sukayi da gateman d'in sannan ta d'au gyalenta ta fita dan ganin waye..
A tsaye yake ya d'an jinginu da jikin motar shi,sae faman latsa wayarshi yake,da ganinshi ka ga d'an gidan masu shi,dan ko kayan jikinshi ya isa ya tabbatar maka da cewa d'an masu akwae neh.Ko kad'an beji isowar ta,shi dae kawae ya d'aga kai saiya ganta neh,murmushi yyi tareda fad'in "haba meh kyau,koh sallama bbu! Ai ban zaci kin iso ba",wani shegen harara Suhana ta watsa mishi tareda fad'in "what do you mean? Nazo gurin nan dan sauraron surutun ka?toh am sorry kashedi nazo maka"..
*HAMAGEE*
💦 💦💦💦 💦
*LAIFIN WAYE??*
💦💦💦 💦💦💦
_Written by the Aplomb writer: *Hamagee*_
*In devotion to Maman Saif*
💦
Page 02 💦💦
A raunane bawan Allahn nan ya soma magana " *haba Baby!! Ko sunana baki tsaya kinji ba kin hauni da fad'a,ae ba haka akeyi ba saeki tsaya na miki koda introducing kaina neh koh*"..
Suhana batace dashi qala ba,illa sauraronshi data tsaya yi.Ya dube ta kafin yace "toh Alhmdllh!! Da farko sunana Khaleed Affan,mu y'an usulun Bauchi neh,aiki ya kawo mahaifinmu nan Kaduna,inda ya had'u da mamanmu ya aura,nine first born nasu sae brother nah Khaleem wanda yanzu haka 300l yake..Na dawo daga U.k last month inda na gama masters d'ina,but still hoping to continue later.Ranan na ganki ta qarshen layin nan ina wucewa zanje gidan wani friend d'ina,nan naji kin kwanta mun a rai,toh dalilin dayasa nayi ta bincike akanki kenan,har Allah yasa na samu address naki da sunanki.Hope zan samu karb'uwa!!"..
Yana kaiwa nan Suhana ta watsa mishi wasu harara me cikeda nuna tsana qarara sannan ta jaa tsaki.A fusace take magana.
"Kai wani irin wawa neh da har zucuyar ka zata yaudare ka kan Suhana? Ance maka ni irin matannan neh da kuka saba tsayarwa? Toh wllhi tun wuri ka jaa jikinka because I'm not your class,dubeni ka gani banyi kamada kalarka ba ko kad'an",ta qare maganar tana nuna mishi kanta..
Mamaki neh ya ishe Khaleed,yama rasa ta cewa,saeda ta qare mishi cin mutunci sannan ta bar shi a wajen ta shige gida abunta..
Khaleed ya jima a tsaye yana jimamin abun kafin nan ya koma cikin motar shi ya tada ya tafi,yana tafe zuciyar shi na mishi zafii.Tunanin maganar da abokin shi Ja'afar yyi mishi ya fara..
Dama ranan daya zo unguwar harya ga Suhana,gidansu Ja'afar yazo,koda yayi wa Ja'afar kwatancen ta sae yace mishi ae yasanta amma indai zaiji shawarar shi toh karya yadda ya fara nemanta dan batada mutunci,batama san miye mutuncin ba..
Amma ina,firr Khaleed yaqi jinshi,haka Ja'afar ya sanarda shi sunanta sannan yau ya rakoshi har qofar gidansu,saedae daya rako shi saeya ceh shidae bazae zauna ya kalli kayan baqin ciki ba,saboda haka ya tafi ya bar Khaleed a wajen...
Yanzu Khaleed bema san ta inda zai fara sanarda Ja'afar kan batun ba,dan sosae ya hana shi amma yaqi hanuwa.
**************************
Suhana nah gama zazzage rashin mutuncin nan ta bar wajen,tana bud'e gate d'in ta shigo a fusace ta sake qofar ya ruhu da qarfi saeda gateman d'in ya razana,bama shiba har Mommyn ta dake can cikin gida saeda ta tsorata.
Nan ta kashe ma gateman d'in warning kan karya yarda ya sake zuwa ce mata wani yana nemanta idan ba haka ba abakin aikin shi,da jin haka ko gateman yace "insha Allahu hakan ya baro ya faru a gidannan..ayi haquri hajiya",Suhana ta wuce tabar gun ta shiga cikin gida..
Mommyn Suhana na zaune a palourn duk ta tsorita tana jiran jin abunda ya faru,ji tayi an bako qofar palourn,Suhana ta gani sae faman zage zage take,wae kowane gaja ya ganka sae yace yana so (kunji ta faa,wae gajaa bayan yafita kud'i,dan mahaifinshi babban me kud'ine a garin Kd,d'an kasuwa kuma d'an boko me jida kud'i)..
Mommyn ta tashi tsaye tana tambayar Suhana "keda waye haka beauty?",ko sauraron Mommyn Suhana batayi ba,ta wuce d'akinta tana ta faman buga qafa,binta kwae Mommyn takeyi da kallo harta shige d'akin ta banko qofa..
*HAMAGEE*
💦 💦💦💦 💦
*LAIFIN WAYE??*
💦💦💦 💦💦💦
_Written by the Aplomb writer: *Hamagee*_
*In devotion to Maman Saif*
💦
Page 03 💦💦
"Ohh yau kuwa waya tab'a beauty haka?",Mommyn Suhana ta fad'a a bayyane tareda neman gurin zama,kallon Joy prime d'inta ta cigaba dayi.
Suhana koh tana shiga d'akin ta cire d'an gyalen jikinta da takalmin ta nemi guri ta kwanta a kan gadonta,tunani iri-iri ta rinqa yi,saedae duk ba masu b'ullewa da ita hanyar gaskiya bane.Can bacci yyi gaba da ita agun.
Around 9pm kowa na zaune a palour suna kallo,saedae banda Dad nata dan shi yyi tafiya amma gobe yana hanyar dawowa.
***************************
*Waceceh Suhana*?
Suhana dai ita ceh y'a d'aya tilo wajen Haj.Faty Omar Farouk da Alhj.Omar Farouk,wannan dalilin yasa suke matuqar jida ita da sakalta ta dan komai tayi daedae neh,amma wannan ya samo asaline da irin kyaun da Allah ya bata,shiyasa take gara kan samari kai harma da manyan masu kud'in garin Kaduna.
Samarin Kaduna d'add'aya neh basu san labarin Suhana da irin kyaun ta ba,babbar matsalar iyayen kuwa itace,na farko halin maman neh tayi ta zuga Suhanan kuma ba akan turba ta gari ba,sannan duk abunda tayi daedae neh agunta.Na biyu kuma shine Baban baya kwab'an Maman,infact ma duk abunda Maman tayi a matsayin daedae yake d'aurashi saboda irin sonda yake musu shiyasa shi ko kad'an baya ganin laifin y'arshi da matarshi.
Alhj.Omar Farouk shahararren d'an kasuwa neh,yyi karatu Alhamdllh amma business keh gabanshi dan har wasu qasashen yanada shares na companies d'in designs da kuma saeda takalma na qasashe daban-daban,*koh hakan yasa Suhana girman kai da wulaqanci?? Ansar itace aa,damuwar Suhana kwae itace kyaun da Allah yyi mata dan ba qarya Suhana akwae kyau dan koh maqiyinta yasan hakan kuma bazae iya b'oyewa ba koda ya kasa furtawa*..
Maman kuwa bata aiki kwata-kwata dan bbu abunda ta nema ta rasa a rayuwarta dana y'arta,ko kad'an Baban be barin su suyi lacking wani abun.A cewarshi ma komai yakeyi dansu yake ae dan bashida uwa ko uba,wannan dalilin yasa bata aikin komai saedae tanada degrees har biyu,inda ta karanci Chemical Engineering.
Suhana kuma yanzu haka tana karatu a University of Kaduna,inda take karantar Ecology,yanzu haka tana 200l neh going to 300.Amma har yanzu bata sa asabar bama balle kuma lahadin yin aure.Ta tsaya rawar ido,kowa yazo tace bashiba kuma iyayen sun zuba mata ido tana yin yadda taso.
*Back to labari....*
Suna cikin kallo wayar Maman tayi ringing,inda tayi murmushi kafin tayi answering ganin wanda yake kira,Alhj.Omar ke kirah,bayan ta d'aga sae naji tace "wa'alaikas salam my one,yah aiki kuma?"saeya answer daga wajenshi sannan naji tace "wllh lafiyarta lau,gata can muna kallo tare",wata maganar ya sake kafinnan tayi kira ma Suhana "beauty! Kizo ga Dadynki na magana",tasowa Suhana tayi tazo ta qarb'i wayar sannan ta kara a kunnenta tareda fad'in,"hello dad",Daddyn ya answer daga can sae kuma naji tace "lafiya klou,banda wata matsala,ina gobe kace zaka dawo?",tayi tambayar cikin sakalci irin nata,daga bisani sukayi sallama ta dawo ta zauna.
Wa Maman ta bada wayar suka cigaba da hirarsu kamar saurayi da budurwa kamar yadda suka saba a kullum,dan ko yana gidanma hakan sukeyi.
Suhana kuma na zaune tana kallo bata ma san abunda sukeyi ba dan gaskiya batada sa ido,kwata-kwata bata shiga abunda be shafeta,dan zaku iya yin sirrinku ma a gabanta batama san kunayi ba dan hankalinta na kan abunda takeyi neh,bbu gulma,bbu shishigi,kuma ba munafinci,wannan halin nata neh keh burgeni da ita..
Kun san dama ance duk kyaun halinka,toh sae an samu mara kyau,haka duk munin halinka,sae an samu meh kyau a ciki,every good person has his own good side,likewise every bad person,surely has his own good side.
Ku cigaba da bin Hamagee dan jin dad'i da kuma nasihun dake cikin wannan labari
*HAMAGEE*
💦 💦💦💦 💦
*LAIFIN WAYE??*
💦💦💦 💦💦💦
_Written by the Aplomb writer: *Hamagee*_
*In devotion to Maman Saif*
💦
Page 04 💦💦
Su Mommy sun jima suna hira kafin yyi hanging call d'in.Suna cikin kallo Suhana ta kwashe da dariya,koda Mommy ta tambayeta saeta taso ta nuna mata chat d'in da sukeyi yanzu da wani,wae yace yana sonta neh shine ya tura mata pic nashi through whatsapp,yana cikin followers nata kuma a IG,infact anan ma ya samu pic nata dan numbern ta na appearing.
Mommy ma dariyar tayi kafin tace "wllh beauty bakida kyau!! Gashi kyakyawa,meye matsalarki?",Suhana ta kalli Mommyn kafin nan tayi commenting "haba Mommy,kema da ganin wannan ai kinsan ba ajina bane,wae sunanshi Yusuf Hisham",wata dariyar ta sake kwashewa dashi,haka ma Mommyn.
Sun kai qarfe goma sha d'aya na dare kafin suka je suka kwanta.Suhana bata nima da kwanciya ba tayi bacci hankalin ta kwance.
Washegari da safe bayan sunyi breakfast aka fara girke-girke na dawowar Daddyn Suhana,sunsha aiki danma sunada masu aiki har biyu,d'aya bazawara ceh me suna Talatu sae yarinya da bata wuce shekaru goma sha uku ba wato Hadiza.Tare sukayi komai sannan suka gyara ko'ina dukda dama gidan a gyare yake dan bbu yara balle ace ana b'atawa kuma dukda haka kullum sae anyi shara.
Wajen qarfe biyu Suhana da Mommyn ta suka shirya sannan suka nufi airport d'auko Dad,suna isa bada dad'ewa ba jirgin su ya sauqa,murna wajen su bbu magana,bbu koh kunya Suhana taje da Mommynta suka je suka rungume Dad a wajen,mutane da yawa na kallonsu saedae wasu burgesu sukayi,dan abun akwae sha'awa.
Bayan sun gama d'okinsu sae suka shiga motar bayan an shigarda kaya cikin boot,Suhana keh driving,Mommy kuwa da Dad suna baya suna hiran yaushe gamo kai kace shekara yake yyi,alhali befi two weeks ba.Bayan sun iso sae aka shiga da kayan sannan suka shiga ciki,inda sukayi sallah kafin sukazo yin lunch,kowannen su na cikeda nishad'i..
Suna cin abinci suna hira abunsu,can Dad ya lurada yanayin Suhana,bata cewa komai.Kowa yana magana amma banda ita,ya dubeta sannan yace "yah akayi neh my beauty?",a lokacin Suhana ta dawo daga tunaninda takeyi,tace "it's nothing dad,am just feeling a little dizzy that why",Dad yace "ayyrh...sorry koh,Allah ya sauwaqa",tace "ameen",Mommy tace "sorry my princess,koh zamu asibiti neh?",cikeda nuna kulawa tayi maganar.
Suhana tace "it's nothing much fa Mom,ba wani asibiti,I just need some rest",tashi tayi ta nufi d'akinta ta rufo qofar, kwanciya ta d'anyi dan duk jikinta a mace,abunka da malalaciya,aikinda tayi yau shiyasa mata wannan gajiyar.
Bata jimaba tayi bacci kamar wanda tayi surfen mudu 10.
Bayan tafiyar Suhana kuwa da qyar Mommy ta iya qarasa cin abinta,duk tabi ta damu kamar wanda akace mata y'ar zata mutu.Bayan sun gama sae suka tashi suka nufa d'aki suma dan hutawa,Hadiza ceh tazo ta kwashe shirgin ta kai kitchen sannan ta gyara gun.
Da daddare kuwa fita sukayi dukansu zuwa wani restaurant da suka saba cin abinci agun,anan sukayi dinner sannan suka biya different shops sukayi sayya,su icecream neh da ire-iren su,sae kuma suka siyo fruits dan na gida ya qare.Suna dawowa kuwa kowa yyi d'aki dan yau ba hira suke jinyi ba,da gani duk a gajiye suke.
*HAMAGEE*
💦 💦💦💦 💦
*LAIFIN WAYE??*
💦💦💦 💦💦💦
_Written by the Aplomb writer: *Hamagee*_
*In devotion to Maman Saif*
💦
Page 05 💦💦
Washegari da safe bayan sun gama breakfast sae Suhana ta tambayi Babanta wae ya bata kud'i zata shopping bcoz next week zata koma school,ceh mata yyi taje d'akin shi cikin wata drawern gadonshi akwae kud'i ta d'ebi yadda takeso,tayi mishi godiya sannan ta nufa d'akin.Maman kuwa na zaune a gefenshi tana jinsu amma bata ceh qala ba saima washe bakinda tayi tayi,a ganinta ma hakan da yyi daedae neh yyi neh saboda soh da qauna da yake yima y'ar.
Suhana na shiga d'akin gun side drawer nashi ta nufa,inda ta bud'e na farko,bunch bunch d'in kud'i neh cikeda drawern,batareda ta irga ba ta d'eba kwae ta watsa su cikin jakarta sannan ta fito,Baban yace "kin d'ebi inda zasu isheki ina?",Suhana tace "eh! Nagode daddy nah",yace "anything for my daughter",tayi waving nasu bye sannan ta fito,motarta ta shiga sannan ta wuce.
A wajen shopping d'in suka had'u da wani mutumi,babba neh gaskiya dan zaiyi sa'an babanta,saedae irin meh kud,innan neh so ba sosae za'a ga tsufan nashi ba,sallama yyi mata lokacin tana qoqarin ciro wata riga da tayi mata kyau,juyowanta kenan tace "waalkslm",koda ta ganshi juyawa tayi ta cigaba da abunda takeyi bayan ta answer sallamar kenan.
Shi kuma daya ga haka sae ya mayso yazo gefenta ya tsaya yana fad'in "baiwar Allah ko meneneh sunanki?",batace qala ba saema dad'a gaba da tayi,tana duba kayan,shima matsowa ya sakeyi kamar tsohon maye yaqi haqura,cewa yyi "idan bbu damuwa toh ki ban koda lambar wayarki neh inyaso idan kin samu lokaci sae nazo mayi maganar a gida ae tafi koh?",kamar da kurma yakeyi dan koh kallonshi bata sakeyi ba bayan na d'azunnan.Ganin batada niyyar magana yasa yah soma introducing mata kanshi,"da farko dae sunana Alhj.Isa Yakub,a garinnan nake da zama kuma itace mahaifata,a yanzu inada mata d'aya da yara tara,babban Kamal sae Aasim sae......",bai qarasa maganar ba ta daka mai tsawa kamar d'anta,"kai dalla malam dakata,who the hail asked you about all this? Toh maybe ma gara d'annaka wataqil in yanada aji ina iya lallab'awa dashi,amma kai kana nan tsofai tsofai da kai,ai wannan ma ragemun daraja kayi wllhi,na farko kafi sa'an babana,na biyu baka duba tsufarka da yarintata ba kazo kke mun useless talks,sannan na uku bakada kamun kai koh kad'an inba haka ba kayi magana an maka shiru instead of ka kama gabanka,aa ka tsaya kana ta zuba,excuse me please,mtsewwww",ta wani jaa dogon tsaki kafin ta bar wajen kamar meh shirin bangaje shi.
Shikuma wani farin ciki neh da annashuwa ya cika zuciyarshi saboda irin dad'in muryarta da yaji,yace a ranshi lallae za'a jeh da wannan yarinyar,zuwa yyi ya bada kud'i me yawa ma sellern yace mata idan wannan yarinyar tazo karta karb'i kud'inta gashi ya biya,matar tace toh,numbern motar Suhana yaje ya duba kafin ya tafi,a ranshi yyi tunanin kamar yasan irin wannan numbern,amma be tuna inda ya santa ba.
Suhana koh bayan ta gama siyayyarta kaman meh barin gari saeta zo biyan kud'in,matar tace mata ae wacen Alhj.ya biya mata,tsawa Suhana ta daka mata tace maza maza tayi calculating mata balance d'inta yanzunnan,bbu yadda matar ta iya haka tayi calculating,43k'500 neh kud'in,so cirowa Suhana tayi ta irga 44k ta watsasu gaban matar tareda fad'in "in kinga dama ki cinye kud'in daya baki in kinso kuma ki mayar mishi idan ya dawo because they ain't making any favour to me but maybe to you",tana kaiwa nan tayi ficewarta yaron shago na biyeda ita riqe da kayan nata..
*HAMAGEE*
💦 💦💦💦 💦
*LAIFIN WAYE??*
💦💦💦 💦💦💦
_Written by the Aplomb writer: *Hamagee*_
*In devotion to Maman Saif*
💦
*When you don't need a reason to smile, a cause to be happy, or a motive to laugh. That's when you've found the meaning of life.*
Page 06 💦💦
Maman da baban na zaune a palour Suhana ta shigo ranta a b'ace,sae faman kumbura takeyi.Baban neh yace "waye yah tab'a mun beauty haka?",cikeda shagwab'a ta qarasa inda suke zaune,ta zauna a qasa daedae qafar baban sannan ta kwantarda kanta a kan cinyarshi tana kuka,baban yah d'aura hannunshi a kafad'arta alamar rarrashi kafinnan yace "fad'a mun meye yah sameki,dan ba haka kka fita ba kinji princess",cikeda sakalci irin nah Suhana tace "Dad na rage kyau neh ko kuma na soma tsufa neh?",cikeda mamakin tambayar ta baban yace "kamar yah kin rage kyau kuma? Wani neh yah fad'i hakan,toh na tabbatar haushin rashi yakeyi,kin san ance haushin rashi kansa makaho yace ido da wari,saboda haka calm down kyaunki na nan yadda yake saema wanda yake qaruwa,kuma bbu alamar tsufa a tareda keh,kinji princess,fad'a mun keda waye?",murya qasa qasa tace "wani tsoho neh yah ganni wae yana sona,kuma wae...."saetayi shiru kuma,kamar zasuyi dariya amma sae suka matse dan sun san kalar rigimar Suhana,yanzu suna mata dariya sun tsokano wani rigimar,maman tace "kiyi haquri beauty nah,karki sake kula irinshi nan gaba balle harya fad'a miki abunda zae dameki kinji",Suhana ta d'aga kai alamun eh.
Maman tace "gud",nan sukayita lallaminta harta dawo normal kamar ba ita ba.
Washegari da rana baban ya sanar musu cewa zaeyi baqi,wani abokin shine zasuzo da d'anshi,so ayi musu abun tarba,maman tace toh.Shirye-shirye sukayi tayi dukda yawancin aikin ma basu sukayi ba.Bayan sun kammala sae aka shirya ma baqin dining,aka kai komai da komai ba sai sun iso ayita faman kai kawo ba.
Around 3:00pm suka iso,sunji dad'in ganin juna sosae dan sun jima basu gamu ba dama,Baban Suhana neh ya tambayi sunan d'an nasa,shi kuma abokin yah ansa da "Aasim kenan,yanzu yana final year d'inshi na masters",baban Suhana yace "wow,wansa kan yyi aure abunshi","Kamal ba",inji Alhj.Isa Yakub.Baban Suhana yace "Allah sarki,muje muyi lunch toh",suka tashi suka nufa kan table danyin lunch.
Wani abunda zae baku mamaki anan shine,Abokin baban Suhana daya zo d'innan shine thesame mutumin da Suhana ta gamuda shi a butique jiya,kwamacala kenan dan d'anshi Aasim ma saurayin Suhana neh though bata sanshi amma yah nace mata,shi kuma a school suka had'u,gashi d'an gaye kyakyawa amma firr Suhana taqi amince mai.
Bayan sun kammala sae Alhj.Omar wato baban Suhana yah kira matarshi suka gaisa,bayan sun gaisa sae suka d'an tab'a hira,can baban yah tunada Suhana,tambayar maman yyi Suhana nah ina neh? Tace mishi "tana d'akinta,ina jin bacci takeyi",Alhj.Isa yace "y'ar mun ceh koh?",cikeda zolaya yah fad'a,baban yace "itaceh,kuma kaga be kamata ku tafi baka ganta ba dan dama bata sanka ba tuntuni,zumunci ya fara yin wuya yanzu",Alhj.Isa yace "wllhi kuwa",baban yace da maman ta kirata,maman ta tashi taje kiranta.
Shidae Aasim hankalinshi bai wani kwanta ba,zuciyarshi tana bugawa tun shigowarsu gidan,saedae bashida ta cewa tunda baisan meya sameshi ba,baban koh sae zumud'i yakeyi a ranshi yana fad'in wataqila ma yarinyar ta burge d'anshi wato Aasim,da yaji dad'i kuwa,saboda qarin danqon zumuncine.
A kwance take tana shan baccinta,daka ganta kaga wacce damuwa tayi ma qaranci,dan ko kad'an bbu alamarshi a tareda ita,Maman ta qarsa har kan gadon amma Suhana bata san ma ta shigo ba dan daga gani baccin yyi nisa sosae,tashinta maman ta shiga yi,da qyar ta samu Suhanan ta tashi,tace da ita tazo ta gaida baqin inyaso saeta dawo tacigaba da baccinta,bbu musu Suhana ta tashi dan tasan inba taje taba toh lallae bazata samu tayi baccinta ba,an ringa damunta kenan.
Hijabinta burmeme ta sanya colourn purple yyi mata kyau,sannan tabi bayan maman zuwa inda baqin keh zaune da Daddynta sunata shan hirarsu.Da sallamarsu suka shiga bayan an answer musu,maman na gaba ita kuma Suhanan tana bin bayanta har maman ta zauna a kujerar gefen baban,tirqashi,ido hud'u sukayi da Aasim wanda mamaki yah ishe shi,ashe dama saboda ganinta ne zuciyarshi keh bugawa tun shigowarsu? Kuma nan neh dama gidansu? Ashe iyayensu abokai neh dama? Toh indae hakane shikam fad'uwa tazo daedae da zama.
Suhana kuwa tunaninta meh yazoyi gidansu,dama yazo ganin iyayenta neh? Shine aka ceh mata wae abokin babanta neh zaezo,ita har lokacin bata lura da Alhj.Isa daya zuba mata na mujiya ba,d'an nashi kwae take kallo,cikeda tsiwa tace "meya kawo kah gidanmu kai kuma? ance maka za'a mun dolene daka biyo ta bayan idona? Toh wllhi tun wuri ka janye qudirinka dan Suhana ba sa'ar yinka bace",mamaki neh yah ishi Alhj.Isa,ashe d'anshi ma na bid'arta?toh ya zamo mishi lallae yah janye dan kuwa be dace yah had'a nema da d'an cikin shi ba,saedae yanzu yaya zaiyi da Suhana,Allah yasa karta ganeshi,a ranshi yake duk waya'nnan batutuwan.
Maman Suhana da babanta ma mamaki neh yah ishe su,ashe dama sun san juna? Ko dama shine wanda ta basu labarin shi kwanaki cewa yah dameta,kullum sae yyi ta binta a makarantarsu,har baban yake cewa idan an koma makarantar zaije yyi magana da VCn kan cewa akwae wani yaronda yah damu ya'rshi,yah fita a harqanta inba haka ba zaiyi maganin shi,yanzu kam bbu wannan maganar kuma tunda fad'uwa tazo daedae da zama,da Suhana zata yarda ma da sun had'asu aure kwae dan yah yaba da hankalin yaron qwarai,itama mamar tunaninda takeyi kenan a ranta.
Suhana ceh ta juyo gun iyayen tana fad'in "Daddy! Mommy!! Wannan shine wanda nake fad'a muku yana yawan bibiyata a school,wallhi shine,daddy ka rabani dashi",ta qarasa maganar kamar zatai kuka.Sae a lokacin tayi ido biyu da Alhj.Isa,wato baban Aasim,addu'arshi dae Allah yasa bata gane shi ba,ji yyi ta ambaci sunanshi gatsau "Alhj.Isa koh?",tayi tambayar kamar meh qoqarin tuno abu,ai kuwa tana kiran sunanshi jikin shi ya d'au rawa,tabbas yarinyar ta ganeshi,wannan abun kunyar dame yyi kama,ace mutum kamar shi yana latsa yarinya kamar wannan,ae girmanshi zae fad'i a idon d'anshi,kuma ma yarinyar da d'an yake so,that's the worst part of it ma.
Kallon kowa ya dawo kan Alhj.Isa da Suhana,cikeda mamaki baban Suhana yace "Alhj.Isa ka santa neh dama?",shiru Alhj.Isa yyi dan bashida ta cewa zae zufa daya keto mishi,yah rasa yadda zaeyi dan kunyard yake ji kamar yah nitse qasa.Gashi yana ganin girmanshi,yanzu yaya kenan idan yah gano cewa ya'rshi yake nema,kuma ma yarinyarda d'anshi keh nema.Uba nayi d'a nayi..
"Lallae bakada kunya toh,ace tsofai tsofai da kai kana takara da d'an cikinka?,dama kasan gidanmu kuma kasan mahaifi na shiyasa jiyan ka tafi ba tareda tsananta bincike a kaina ba,lallae ma ka raina ma kanka hankali",inji Suhana kenan,abunka da marar tarbiyya,ita a ganinta mah batayi laifi ba,baban nata neh ya katseta da fad'in "abokina neh fa wannan Suhana,kuma besanki bama balle yah ceh zai biyo ki gida",Suhana tace "shine tsohon dana ceh muku ya tareni jiya a butique Daddy,dama wannan d'anshi neh,lallae like father like son",a fusace ta bar palourn tan qunquni,wae ita sun takura mata rayuwa,miye miye d'inta,d'akinta ta koma ta cire himar d'in kanta tayi firo dashi sannan ta kwanta a kan gadon.
A palour kuwa an bar Alhj.Isa da share zufa dukda ba wani zafin kirki ake ba kuma ma akwae air condition a palourn.Bashida ta cewa dan haka yace da Aasim su tafi,baban Suhana yace "haba dae har tafiya?",yace "iyi ai mun jima",cikeda borin kunya,baban Suhana yace "amma in bazaka damu ba ina so muyi wata magana da kai",Alhj.Isa yace "ah toh bbu matsala ai,Aasim,tashi kaje mota ka jirani koh",Aasim yace "toh Abba" sannan yah tashi yyi musu sallama yah fita zuciyarshi a dagule.
Baban Suhana neh yace "dama maganar yaran nan neh,nace meh zai hana mu had'asu tunda har yaro yah nuna yana soh,kuma itama dan sha'ani na yarinta ceh amma nasan daga baya zata amince dan na yaba da yaron",cikeda jin dad'in batun Alhj.Isa yace "danayi murna kuwa,dan naga Aasim na sonta kuma zasu dace da juna sosae,Allah yah saka kuma yah bar zumunci",Baban Suhana yace "ameen,wannan yiwa kaine ai",bayan sun gama tattaunawa sae baban Suhana yah tambayi maman koh tanada abun cewa tace mishi bbu,sae Alhj.Isa yace dasu zai tafi,har wajen mota suka raka shi sannan suka dawo.
Ita dae maman bata ji dad'in yadda baban yah amincewa Alhj.Isa ba tunda yarinya tah nuna bata so,saeda suka dawo ciki ta dubeshi tace "yanzu luv kana ganin abunda kayi daedae kenan?",ya dubeta shima kafin yace "name fah?",tace "na amince musu kan batun yarinyar nan,kana gani fah a gabanka yadda ta nuna bata so,baka tunanin ranta zai b'aci idan taji hukuncin daka yanke and without her knowledge",jikinshi yyi sanyi yace "eh kema kinyi magna,amma ni gani nayi ai zata iya amincewa idan muka gwada mata cewa yyi,by the way yaron naga ba laifi,yanda kyau,yanada qualification meh kyau gashi iyayenshi nada mutunci",ta harareshi kafin tace "hakane,mutuncin neh ai yasa yah dubi y'ar wannan yarinyar yace yana so,kuma kai a ganinka yyi daedae,dama ku maza duk halinku d'ayane ae,koh kun girma baku san kun girman ba,wataqil kaima kanada taka",ta juya mishi qeya.
With full concern yah dubeta yace "why don't you trust me today,after all the years we had spent together,I haven't cheat on you,then why today,don't you trust your husband again?",a take ta sauqo dan tasan bunda take fad'i ba haka bane,baban Suhana daban yake,yana matuqar sonta yanda itama take sonshi,ita dae kwae tayi maganar neh cikin b'acin rai,haquri ta bashi kuma yah haquran.Daga bisani yace da ita suje su tuntub'i Suhana da maganar suji koh zata amince dan yaso mata Aasim gaskiya.
Tashi sukayi suka nufa d'akin inda suka jishi a kulle,da qyar Suhana ta tashi ta bud'e musu,haquri da lallaminta suka shiga yi kamar itace uwar da uban su kuma sune yaran,Allah yah sauwaqe wannan halin..
"Wata magana muka zo miki da ita,kuma tabbas idan har kika amince zakiji dad'in yin hakan nan gaba kad'an",inji baban kenan,Suhana tace "miye maganar daddy?",Baban yace "maganar ki amince da auren Aasim,inada tabbacin yin hakan zae saka miki farin ciki meh d'orewa a rayuwarki nan gaba,kinga he's well qualified",tashi Suhana tayi daga kwanciyarta dan she can't believe what she just heard,tace "haba daddy,wannan wace irin magana ceh nake jii,ka manta neh kaika mun alqawarin bazaka sani yin abinda raina baya so ba toh yah kke neman karya alqawarin saboda wasu strangers sunyi maka dad'in baki".
*Am sorry for the late post,wllh bana jin dad'ine shiyasa,but am much better now,your Hamagee loves you much*
*HAMAGEE*
💦 💦💦💦 💦
*LAIFIN WAYE??*
💦💦💦 💦💦💦
_Written by the Aplomb writer: *Hamagee*_
*In devotion to Maman Saif*
💦
*People may hate you for being different and not living by society's standards, but deep down, they wish they had the courage to do the same*!!!
Page 07 💦💦
"Dad'in baki kuma? Nikam basuce mun komai akanki ba tun bayan tafiyarki,nine dae na hango miki hakan shiyasa nake har nake fad'i,kuma a tunanina shine idan kka zauna kkayi nazari keh da kanki zaki fahimci abunda nake fad'innan bame cutarda keh bane",Suhana ta wani b'ata rai tana fad'in "ni dae gaskiya daddy bana sonshi",maman ceh tayi caraf tace "shikenan ae,tunda tace bata so no need of arguing koh? Ka barta kwae,kwanta kiyi baccin ki beauty",ta qarasa maganar tana kallon Suhana cikeda nuna so da qauna,baban kuma cewa yyi "gaskiyarki kam,nima bana son sakata yin abunda bata sonyi,so it's ohk zan kira Alhj.Isa na fad'a cewa ba zai yiwu ba tunda daman nina fara maganar","shikenan kuwa,danni kam ban son abunda zai b'ata ran beuty nah",inji maman kenan,hugging nata Suhana tayi tana fad'in "that's why I love you much Mum and Dad,parents like no other",murmushi maman tayi,baban kuma yace "anything for my daughter",daga bisani suka tashi suka bar d'akin.
Kwanciya Suhana tayi bayan fitarsu tana tunanin abunda yah faru d'azu,amma fah Aasim yah had'u gashi yah iya wanka ba qarya,ga good qualification,komai yyi saedae tana buqatar wanda yah fishi a komai,dan ita a ganinta tafi kowace budurwa meh jin kanta kyau da aji,so dolene prince nata ma ya zama the most handsome,classy and rich one.Tunaninta kenan a kullum shiyasa har yanzu take ganin bata samu wanda yyi mata ba.Da waya'nnan tunanin tayi bacci..
Bayan fitarsu su daga d'akin Suhana d'akin baban suka koma inda baban yah kira Alhj.Isa yah bashi haquri kan abun bazae yiwu ba bcoz yarinya taqi,shiko Alhj.Isah cewa yyi ba komai sun gode da karamcin da yah nuna musu,bayan sun gama sae yyi hanging call d'in,yah dubi maman Suhana yace "dear kin san gobe zan tafi Uganda koh?",ta wani b'ata rai kafin tayi magana "yaushe kah dawo da har zaka sake yin wata tafiyar? Nikam ban yarda ba",ta wani juya kanta gefe,cikeda nuna kulawa da lallami kamar yadda ya saba yi mata yace "haba mine kamar yau na fara tafiyar nan,aiki zani kuma it's very urgent you know,shiyasa kwae amma da bazanyi tafiyar ba nima".
Cewa tayi "kuma yaushe zaka dawo?",yace "gaskiya zan kai one month koh three weeks five days haka dan aikin da yawa",tace "a month dae??,gaskiya yyi yawa nikam saedae muje tare",yah dubeta yace "toh ai kuma Suhana nada makarnta kinga bazamu tafi tabar makarantar ba,kuma ai bazamu tafi mu barta ita kad'ae ba koh?",tace "saedae kuwa mu tafi mu barta,baga gidan Umma ba nasan zata so zuwa can amma gaskiya ni saedae muje tare",yace "toh shikenan anjima mayi maganar da daddare",tace "Allah yah kaimu",suma kwanciyar sukayi kafin a kira sallahr la'asar.
Da daddare bayan dinner sae baban yah kira Suhana,"Suhana! Suhana!!","na'am Daddy nah ina zuwa",daga d'akinta ta fito sanye da rigar bacci wae har zata kwanta,wani himar da d'aura akan rigar amma himar d'in be kai qasa ba yah dae fi rigar tsayi,ta qaraso tazo ta zauna tace "gani nan",yace "uhumm dama zan fad'a miki cewa gobe in Allah yah kaimu zamu Uganda da mommynki,inada wani urgent aiki neh,kuma zamu kai one month koh muyi three weeks haka".
Da sauri Suhana ta d'ago kai ta kalleshi "tafiya ku barni kuma daddy?",baban yah d'aga kai alamar eh sannan yace "kina son zuwa gidan Umma ina? Acan zaki zauna tunda kinada school koh kuwa?",Suhana tace "wallahi bazan yarda ba Daddy,saedae nima na biku inyaso",maman neh tace "haba beauty keda zaki koma school,kiyi haquri mana in kun samu hutu saeki jeh kema",da sauri Suhana tace "wallah nidae ban yarda ba,qafata qafar Mommy,haka kwae zaku tafi ku barni ni kad'ae,ni bana son zuwa gidan Umman ma,koh mu tafi tare koh kuma mu zauna da Mommy",ta wani jaa ta matse bayan ta qare zancen nata.
Baban yama rasa tah cewa,qoqarin rarrashinta yah soma yi ita kuwa sae dad'a botsewa takeyi.Ita ata firr saedae ayi tafiyar nan da ita,bbu yadda suka iya kuwa qarshe maman neh ta haqura da zuwa amma taso binshi,koh kad'an bata son irin yanayin tafiyarshin nan,ace namiji yayi tafiya wata qasa yah barka harna tsawon wana biyu? Gaskiya ita bata so.
Ga fitinanniyar yarinya da sukeda ita,kwata-kwata bata damu da farin cikinsu ba,ita dae kwae abunda zae sata farin ciki take bid'ar yi tunda haka aka koya mata tun tana qarama,wannan shine babban *LAIFIN* iyayen na farko,basu tsawatar mata so bata jin shakkar kowannensu,kuma duk abunda tace koh tayi shine daedae saboda ita meh kyau ceh bata yin ba daedae ba,Allah yasa mu dace..
Da qyar maman ta iya bacci ranan,duk tunanin tafiyar yaqi barinta.
Washegari tunda asuba bayan anyi sallahr asubahi suka raka baban airport,Suhana harda kukanta baban da maman suna rarrashinta,daga qarshe dae jirginsu yah d'aga su kuma suka koma cikin mota lokacin 6:30am harta yi,bayan sun dawo gida sae sukayi breakfast sannan maman tace ma Suhana anjima zasu gidan wata friend nata,Suhana ta answer da "toh Mommy",sannan ta koma d'akinta ta kwanta dan bacci take ji sosae.
Around qarfe 10 ta tashi tayi wanka ta shirya sannan ta nufi d'akin maman inda ta tararda itama har tayi wanka shiryawa takeyi yanzun,zama tayi tana jiranta ta gama shirin.Bayan ta gama sae suka tafi gidan qawar maman.
Suna isa gidan aka bud'e musu gate suka shigo,suna shiga suka samu haj.Aisha wato matar gidan kenan a palour suna kallo da y'arta wato Abida,Abida yarinya ceh y'ar kimanin shekaru ashirin daedae,ajinsu d'aya da Suhana kuma thesame course,ta tsani Suhana sakamakon saurayinta daya ga Suhanar yace yana sonta,bata qaunarta kona second d'aya dan gani takeyi kamar akwae abunda Suhanan takeyi dan jan hankalin maza,bata santa ba sae a school,tana yawan bama mamanta labarin Suhana,maman kuma cewa kawae takeyi karta na shiga sabgarta gaba d'aya,maganar saurayi kuma in lokacinda Allah yyi zatayi aure toh duk *rintsi* zatayi,saboda haka ta barta da Allah inma wani abun take yi ma mazan,can mata.
Da sallamarsu suka shiga yayinda su Hjy.Aisha da Abida suka answer musu,suna shiga Hajy.Aisha ta miqe tana musu sannu da zuwa ganin hajy.Faty ceh,har lokacin idon Abida na kan tvn da suke kallo,saeda suka qaraso suka zauna sannan ta d'aga ido ta gaida maman Suhana,ta juya kenan tayi ido hud'u da Suhana wacce take kallon wayarta bayan ta gaida maman Abidan.
Wani irin tashi tayi kamar wacce taga kura tana nuna Suhana da yatsarta "Ammee wannan ceh yarinyar da nake baki labari kullum,wacce take zuba zashin mutunci a school d'innan",jin ance rashin mutunci yasa Suhana d'ago kanta tana kallon Abida up and down kafin tace "keh kama kanki daalla,wace ceh mara mutuncin",hankalin iyayen duk ya dawo kansu,Suhana ceh ta miqe tana fad'in "yah kamata ki koyi hankali dan naga kamar bai ishe ki ba",a fusace Abida tace "dakata mara mutunci,keh har kin isa kizo gidanmu kina fad'a mun magana son ranki?toh wallahi kinyi kad'an,ashawooo!!",ran Suhana yah qara b'aci bata san lokacinda ta qaraso inda Abida keh tsaye tana tsiwa ba,marinta tayi tasss kamar y'arta.
Saeda Abida taso fad'uwa,ta d'aga hannu zata rama kenan maman ta tace "keh Abida!bakida hankali neh daga zuwan baquwa zaki soma fad'a da ita?toh koh da wasa bana son rashin hankali","Ammee itace wacce nake fad'a miki fah,wallahi baki san kalan rashin mutuncin taba",inji Abida kenan,maman tace "enough of that nace miki bana son hauka,can't you behave good to a visitor",Abida bata sake cewa komai ba ganin yadda Ammeen nata ta bata rai kuma bata son hakan.
Suhana kuwa ranta yah gama b'aci,wae ta yaya za'ayi wata taci mata mutuncin haka,ba'a haifeta ba kuwa.A fusace ta bankad'o kafad'ar Abida tana fad'in "kinyi kad'an ki ci mun mutunci in fad'a miki,baki kai wannan matsayin ba,in akan wannan kucakin saurayin nakine kema kin san niba ajinshi bace,keh wanda yah fishi mah banyi dashi ba balle kuma shi,dama keh d'ince daedae shi amma ni ba sa'ar shi bace,sannan let me warn you idan kka sake mun irin wannan to be frank with you zakiyi nadama bcoz ba'a taqalata a kwana lafiya.In kunne yah ji.."bata qarasa ba dan a zatonta Abida ta fahimceta.
Abida bata ceh mata komai ba kwae saeta bar wajen saboda ganin yadda Ammeenta keh harararta,d'aki ta koma ranta a dagule,tunanin yadda zatayi maganin Suhana kwae takeyi.
Suhana kuwa fita tayi daga palourn tana huci,mota ta bud'e ta shiga tana jiran maman ta fito su tafi.Ta bud'e wayarta ta kunna data sannan ta hau IG inda ta kalli pics,fita tayi ta hau whatsapp ta duba messages,tayi reply nah wasu,wasu kuma batayi ba,sanda ta gaji sannan ta sauqa ta rufe data...
Bata jima sosae ba Mommyn ta fito,bayan sunyi sallama saeta shiga motar suka tafi,Mommyn ta lura da yadda yanayin Suhana yah sauya ba kamar lokacinda suka zo ba,tace "meh yah sameki beauty?",Suhana ta juyo ta kalleta kafin tace "bakiga yadda yarinyar nan taci mun mutunci bane? Wallahi bazan barta ba,saena yi maganinta yadda nan gaba koh an roqeta tamun ba zatayi koh attempting ba,ki jira ki gani",Mommyn tace "ki barta kwae beauty,kiyi haquri ki rabuda ita kinji?",Suhana tace "wae yah kke cewa nayi haquri neh Mommy,bayan komai a gabanki akayi?",Mommyn tace "ba haka bane,naga komai amma keba sa'ar yinta bace,be kamata ki biye mata ba tunda ita kanta ma tasan kin wuce kula kalan samarinta","hakane amma ya dace na tunasarda ita hakan",inji Suhana kenan,Mommyn tace "toh Allah yah kyauta",Suhana tace "ameen".
Har suka isa gida bbu wanda yah sake cewa qala,bayan sun shiga kai tsaye Suhana ta wuce d'akinta,Mommyn ma d'akinta ta wuce.
*HAMAGEE*
💦 💦💦💦 💦
*LAIFIN WAYE??*
💦💦💦 💦💦💦
_Written by the Aplomb writer: *Hamagee*_
*In devotion to Maman Saif*
💦
*Smile, because you're beautiful. Laugh, because you're living life to the fullest. Stand strong, because haters can't bring you down..* ☺
Page 08 💦💦
Suhana ta kwanta kenan wayanta ta fara ringing,ganin sunan dake appearing kan screen d'in wayar yasa tayi picking "hello daddy!",ta fad'a cikeda salalci,bayan sun gaisa sai take mishi complain d'in tana da buqatar kud'i,yace karta damu zae mata sending anjima.Bayan sun gama wayar saeta kwanta,bada jimawa ba bacci yyi gaba da ita.Da yamma kuwa yah yi mata transferring 50k,bayan taji alert na shigowar kud'in saeta kira shi tayi mishi godiya.
*Some days later...*
Da yuri Suhana ta tashi yau dan zata school, bata tsaya ta wani yi breakfast di'n kirki ba saboda karta b'ata lokaci.Ta d'au keyn motarta ta fice bayan tayi ma Mommyn sallama,tana isha makarantar ta soma hidimar yin registeration,a wajen biyan kud'i a bank tayi wani new catch,wani d'an saurayi neh,yanada tsayi amma ba sosae ba,qibarshi dan daedae,chocolate in completion dan ba'a ceh mishi fari ba,ba kuma baqi ba.Yanada kyaunshi daedae gwargwado gashi d'an gaye dashi,Motarshi qirar CorollaS ceh,blue in colour,sabuwa ceh gata tsaftsaf tasha wanki,shima fess yake,Fahyim kenan.Tunda yaga Suhana yaji yah yaba,ta kwanta mishi a rai,kuma da aure yake sonta dan shima d'in yanzu he's ready tunda yah kammala karatunshi kuma yana aiki,shi Lawyer neh yanzu haka.
Daedae lokacinda tazo bank d'in yah fara kallonta,motarshi na bayan nata dan a tare suka iso wajen sukayi parking,yana kallonta lokacinda ta fito daga motar,ana neh yah qarema kyaunta kallo,gaskiya wannan akwae halitta,yah fad'a a ranshi tareda komawa cikin motar dan da fitowa zaiyi,a rayuwarshi zae iya cewa bai tab'a kallon meh irin kyaunta kuma karku manta shima fah ba tayan baya bane wajen kyaun,daedae gwaegwado sunada kyau y'an familynsu.Bayan ta fito daga motar saeta sanya mata lock kafinnan ta tsallaka titi zuwa cikin bank d'in,duk idonshi na kanta,bayan yah fito shikuma saeda yah duba numbern motarta kafinnan yah bi bayanta,rab'ewa yah tsaya yi dan be samu yyi abunda yah kaishi ba dan karta kub'ce mishi.
Yana biyeda ita harta kammala abunda zatayi sannan ta dawo motar zata tafi kenan,biyota yyi sannan yah qaraso inda take tareda yin sallama "assalamu alaikum",ba tareda tayi mishi kallon kirki ba ta answer "wasalam",kallo yah bita dashi a ranshi yana mamakin yadda ta answer sallamar wae wasalam.Matsewa yyi yah farada "inba matsala ina sonyin magana dake,dan Allah ki bani numbernki koh ki mun kwatancen gidanku sae inzo muyi maganar",juyowa mutuniyar tayi ta qare mishi kallo up and down tana fad'in "kai kuma a suwa da zaka zo gidanmu.Kazo ma kaimun meneh? Koh ance maka ina neman meh tayani hira neh,escuse me!!",ta wani bud'e motarta ta shige ta kunnata,figar motar tayi inda ta bud'e Fahyim dake tsaye da qurar wajen.Shi kuwa girgiza kanshi kwae yyi dan yasan gigin kyaun da take dashi keh d'ibarta,amma meh na wulaqanci haka? By the way meh yyi lacking? Shima ai meh kyaun neh.
Yah jima agun yana tunanin wulaqancin da Suhana tayi mishi daga qarshe ya koma cikin bank d'in duk jikinshi bbu qarfi dan Fahyim yah washi wulaqanci da meh yinshi a rayuwarshi,ji yyi dama tun farko be kulata ba ae da hakan be faru ba,bayan yah kammala abunda yah kaishi saeya fito yah dawo motarshi,yah tada sannan yah tafi abunshi.
Suhana kuwa school campus ta koma,inda ta qarasa bubuwanda zatayi sannan ta koma gida,still akwae abubuwanda yah rage batayi ba amma dole sae zuwa gobe ta qarasa.Lokacin qarfe d'aya mah ta wuce,gida tah wuce kai tsaye dan a gajiye take.Tana isa kuwa taci abinci dan dama gajiyar harda yunwa tunda bata wani karya ba d'azun,nan tayi tah bama Mommyn nata labarin abubuwan da suka auku a yau d'in,tun daga fitart har zuwa dawowanta.Instead of maman taga cewa tayi laifi kan yadda tayi treatening Fahyim,bata gani ba saema qara mata qarfin gwiwa ta tayi,wae meyasa maza basu ajiye kansu yadda Allah yah ajiyesu neh,harda ceh mata ai wani gajan yah sake mata magana ta zage ta nuna mishi babancinsu,ita koh Suhana dama akan turbar take,cewa toh tayi tana jin dad'in yadda maman keh zuga ta da yi mata kirari.
Bayan sun kammala sae Suhana ta koma d'akinta inda tayi sallahn azahar kafin tah kwanta,wayarta ta d'auka ta fara game daga bisani tayi bacci dan a gajiye take,sae bayan la'asar ta tashi inda tayi sallahr kafin ta koma ta kwanta,da magrib ma yyi haka,ta tashi tayi sallahn sannan ta fito palour yanzu kuma,tv ta kunna tayi kallo kafin aka kira sallahr isha'i,shima ta tashi taje tayi kafin ta dawo ta cigaba da kallo,around 8:30pm Mommyn ta fito sukayi dinner sannan suka d'an tab'a hira around 10:00pm Suhana taje ta kwanta dan gobe ma da wuri take son tafiya school d'in.
Tana shiga d'aki tayi wanka sannan ta fito ta sanya sleeping gown sannan ta kashe wutar d'akin ta kwanta bacci,tah kwanta kenan aka d'auke wutar nepa dan haka ta taso tazo ta cire wayarta dake jikin socket tana charge,ta kunna hasken wayar sannan ta dawo tazo ta kwanta kafin ta kashe touch d'in,bata jima ba tayi bacci.
Bayan nepa sun d'auke wuta lokacin Mommy na palour,da qyar ta laluma wayarta ta kunna touch d'in kafin ta kashe socket na tvn da wutar palourn baki d'aya sannan ta koma d'akinta,ta canza kaya sannn ta kwanta bacci itama,saeda tayi addu'a kafinnan ta kashe wutar wayan nata sannan ta koma ta kwanta,itama bata jima ba tayi baccin.
Washegari da wuri ta tashi tayi shirye-shiryenta kafin ta tafi school,tana zuwa kuwa bata wani jima ba ta kammala duk abubuwanda yah kamata tayi,around 10:30am ta gama komai ta bar makarantar,saeda ta biya ta sayi kayan qwalma a wani shop kafin ta tafi gida,ta samu akwae wuta dan haka a palour tayi branch,inda tayi ta kallonta tana ciye-ciyen su chocolate d'inta,lokacin Mommyn nata bata gida sae masu aikinsu,dama kafin ta fita Mommyn ta fad'a mata cewa zataje gidan Umma njima.
****************************
*Some days back....*
Ranar da Suhana da Mommynta suka ziyarci gidan Hajy.Aisha kenan.
Bayan tafiyarsu hajy.Aisha tayi kiran Abida,"Abida! Abidaa!!"."Na'am Ammee",inji Abida kenan,ta hanzarinta ta fito tana fad'in "gani Ammee",Ammeen ta dubeta sannan tace "qaraso kizo ki zauna",cikeda ladabi ta qaraso ta zauna a gefenta,Ammee ta dubeta kafin tace "kan maganar wannan yarinyar ceh,Abida nasan keh yarinya ceh me jin magana ta,bake bama har sauran yayyunkin basa bijirewa umrnina,saboda haka kema qaramarsu hakan yah kamata kiyi koyi dashi,kar in yadda inji wani abun yah had'aki da ita,kota neme ki da magana toh keh karki biye mata sae a zauna lafiya kinga mamanta qawata ceh,tare mukayi secondary school harma jami'a,saedae ni bayan mun kammala first degree na fara aiki,ita kuma cigaba tayi inda har yanzu bata fara aikin ba.Saboda haka ina gargad'inki karki sake inji wani abun kinji koh",Abida tace "toh Ammee nah! Amma wallahi Ammee sabida darajarki kice dana gwada mata nima ba'a tab'ani a wanye lfya".
Ammee ta dubeta qwarae tasan halin Abida,kamar yadda ta fad'a daba don maganar da tayi mata da bazasu wanye lafiya ba dan Abida bata shiga harqar mutane koh kad'an amma idan wani yah nemi yah shiga nata toh bazae dad'inyi da ita ba dan Abida akwae bala'i,wanda hakan yasa bata mu'amala da mutane da yawa hasalima qawarta d'aya meh suna Fa'iza,tare suke tun primary school,secondary sannan yanzu suke university d'aya kuma course d'aya aji ma d'aya.Ammeen tace "na sani amma kiyi haquri",Abida ta dubi Ammeenta kafin tace "no need ki bani haquri ae,just as you said",Ammee tayi murmushi tareda fad'in "Allah yyi miki albarka",Abida tace "ameen".
Yaran hjy.Aisha uku a duniya,d'anta na fari shine yaya Fahyim,sae second child Adda Faty,sae Abida yar auta.Yaya Fahyim d'in yanada shekaru 27 yanzu,yah karanci Law yanzu aure kwae yah rage mishi.Sae Adda Faty wacce ta qare degree nata itama amma tayi aure shekaru uku da suka wuce wanda sae bayan auren ta qarasa karatun nata,shekarunta 24 yanzu,tanada y'arta d'aya meh suna Ihsaan.
Bayan wasu kwanaki,
Abida ta ga Suhana a wajen registration amma tayi kamar bata ganta ba,ita kuwa Suhana da alamu bata ganta ba ma dan da tayi making drama a wajen,tana kallonta harta zo ta gama abunda zatayi ta tafi,batace mata komai ba saboda maganar da Ammeenta tayi mata.Bayan ta kammala gida ta koma washegari ma ta dawo,tayi three days kafin ta gama.
Fahyim na zaune da Ammeen su a palour suna hira sae idonshi yah kai kan wayarta,kamar wanda aka zabura yace "Ammee muga profile pic d'innan,hoton waye?",murmushi Ammee tayi tareda miqa mishi,yana gani ya tuno da kamannin Suhana,"Sunanta Suhana,tayi maka neh?",inji Ammee cikeda zolaya,Fahyim yace "Ammee kenan ae wannan wulaqancin ta bazai barta ta samu miji ba",Ammee tace "kah santa kenan?"cikeda tuhuma.
Fahyim yace "qwarai,shekaranjiya mun had'u da ita a bank,danayi mata magana kuma saeta nemi ta ci mun mutunci,shiyasa na haqura",murmushi Ammee tayi kafin tace "Suhana kenan,wannan kyawun nata na rud'inta da yawa,amma to be frank with you inhar kana sonta karka samu damuwa insha Allah zaka samu",Fahyim yace "Ammee kenan,in zan sameta ina so mana,amma wulaqanci neh ni bana so kin sani kuma,tukunna ma a ina kka santa?",Ammee tace "she's my friend's daughter,ranan ma sunzo gidannan da ita,mamanta is a good friend of mine,tare mukayi secondary school da university da ita,saedae ita bata aiki har yau,inhar kana soh zan iya samun mamanta nasan yadda za'ayi,karka damu kaji",cikeda jin dad'i Fahyim yace "yauwa Ammee nah,shiyasa nake sonki,wllh yarinyar ta kwanta mun a rai tun randa na fara ganinta,ni dae kwae wulaqanci neh na wasa".
Ammee tace "ae wulaqancin saboda bbu soyayya neh,inda kawae soyayya da bazatayi maka ba,by the way ae d'anna wa ma kyakykyawa neh,son kowa qin wanda yah rasa,yah za ayi ace taqishi",cikeda zolaya tayi maganar.
Fahyim yace "kai Ammee,kema ziga zakiyi mun?",tace "ba zancen zuga,haka maganar take,yanzu dae ka kwantar da hankalinka,na karb'i wuqa da naman zanyi komai,just sit back and watch",yace "toh godiya nake",haka sukayi ta tad'insu abun sha'awa har Abida ta dawo,da sallamarta ta shigo bayan sun answer,duk a gajiye take da qyar ma take magana kamar meh azumi.
*HAMAGEE*
💦 💦💦💦 💦
*LAIFIN WAYE??*
💦💦💦 💦💦💦
_Written by the Aplomb writer: *Hamagee*_
*This page is yours my Faty aka y'ar mitsila 😘..... Happy Anniversary and May your marriage be Blessed with love, joy And companionship For all the years of your lives! Hoping that the love you shared years ago Is still as strong today as it was then Bringing you much joy , love and happiness To celebrate again.Happy anniversary dear* 💋❤
💦
*Three things in life you can never get back: 1) The rock after its thrown. 2) The word after its said. 3) The moment after its passed.*
Page 09 💦💦
Bayan ta gaidasu kai tsaye kitchen ta wuce,ta d'ibo abinci jollof rice ceh da salad sae kunun aya data d'auka a fridge.
Ta d'au spoon da cup sannan ta koma palourn inda ta ajiyesu kafinnan ta koma d'akinta,himar ta cire sannan ta shiga toilet tayi fitsari.
Bayan ta wanke hannunta saeta fito tasa wayarta a charge sannan ta nufi palourn.
Wani irin juyawa kanta keyi tsabar yunwa da gajiya,hakan yasa bata ceh masu Ammee komai ba,hasalima bata san meh suke fad'i ba.
Saeda ta gama cin abincin ta kafinnan ta tashi ta kai plates d'in kitchen sannan ta dawo ta zauna,wani annashuwa take ji don d'azu ba qaramin jin yunwa take ba.
Ta dubesu kafin tace "waeni Ammee meye naga kunata farin ciki neh ko dae yaya yah samo mana mata neh?",
da zolaya ta fad'i hakan,,
Fahyim yace "yah akayi kkayi guessing correctly?".
Abida tayi dariya kafin tace "dama nasan za'a rina wae an saci zanin mahaukaciya.Meh sunanta kuma a ina take,aina mah kuka had'u??".
"Irin wad'annan tambayoyi haka? Bbu koh kad'an jinkiri"
Fahyim neh yyi maganar,dariya sukayi dukansu.
Abida tace "toh ae abun neh yah bani supprise,ace yau kaine da budurwa,kaida koh kallo yan'matan nasu isheka dashi ba.
Amma it's a great news indeed,sae a shafa mun labarinta nima naji",ta qarasa fad'i tana gyara zama alamun sauraron shi take.
Fahyim yace "Ammee zaki tambaya full detail akanta donta tabbatarmun da cewa y'ar good friend nata ceh,nidae jiya muka had'u da ita a bank,kuma da nayi mata magana batayi responding,shine na qyaleta,yau kuma a dpn mamanta naga pic nata a wayar Ammee shiyasa ma har nayi maganar amma da na fasa da ita ma",
Dariya Abida tayi dan tasan halin yayan nata kamar yadda yace ya fasa d'innan toh kad'anne daga aikinshi.Saedae koh wacece wannan yarinya me sa'a haka?
Tace "muganta Ammee",Ammee dake ta latsa wayar tace "ina zuwa",duba numbern Maman Suhana tayi tareda shiga kan pic d'in tayi saving nashi to gallery daman batayi ba.
Saeta fita daga whatsapp d'in dama ta gama abunda zatayi,ta rufe datar tareda shiga gallery tayi searching pic d'in,ta shiga sannan ta miqo ma Abida daketa alla alla ta ga budurwar yayanta.
Da hanzari ta karb'i wayar tana washe baki,Fahyim kuwa kallonta kwae yake yana jiran comment nata dan yasan dole ta yaba itama.Ammee kuwa kallon da take mata na jiran jin me zatace neh dan sarai tasan da jiqaqqiya a tsakaninsu.
Da mamakin Abida saeta ga hoton Suhana a kan screen d'in wayar,bakin data washe shi d'azu yanzu tsuke shi tayi tareda jan tsaki.
"dama wannan ceh budurwar taka yaya? Ka rasa wacce zaka gani kace kana so kaf garinnan sae ita?toh wallah shawara zan baka gwanda tun kafin kayi nisa ka sake tunani akanta".
Da mamaki Fahyim yace "keh kuma ina kka santa da har kka san batada kirki? Koh kina kishi neh?".Yana kaiwa nan shima yah tsuke fuska.
Abida tace "Allah yah kiyaye mun yin kishi da wannan ballagazar wllhi,koba komai na fita mutunci,Ammee kema kin amince mishi da ita kenan?bayan kinsan halinta".Ta qarasa maganar tana kallon Ammeen nasu.
Ammee tace "Abida kenan,dan kun samu misundersting da ita does'nt mean batada kirki fa,kuma maganar bata son kula samari ba abun mamaki bane kiga ta kula yayanki dan shima abun bari bane,ta yiyu waya'ncan di'n duk basuyi mata bane koh basu dace da ita ba,amma yayanki ai batace be mata ba koh!".
Fahyim yace "fad'a mata dae Ammee,kuma ma ni ta burgen dan hakan yah nuna cewa tana da aji,kuma ni bana son mace mara aji dama,Ammee dama abokiyar fad'an ta ceh?",ya fad'a yana kallon Ammeen.
Ammee tace "eh sun tab'a samun matsala da ita,dan ranan ma dana ceh maka sunzo da mamarta saeda sukayi,amma yanzu komai yah wuce a tsakaninsu tunda nayi mata magana".
Fahyim yace "toh daya fi dan dolenki kiyi shiri da my furture wife insha Allah".Abida ta tab'e baki tana kallonsu.
Tace "Allah yah kyauta,ma wannan kke cema future wife din'ka? Nidae koh ka aureta ba sonta zanyi ba bbu ruwana da rayuwarta,ballema bata da mutunci bata ajiye kanta nan kusa ba zaiyi wuya ta amince maka".Tana kaewa nan ta juya kanta tana kallon tv da tashar mbc 2 keh aiki.
Ammee ceh tace "bana son haka Abida,dan kunada rashin jituwa tsakaninku be dace kina aibantata a idonshi ba,ai saeki kashe mishi qarfin gwiwa,by the way idan bazaki fad'i alkhairi a kanta ba saekiyi shiru bata son qananan magana,kuma dole ki ajiye shegen kishinkin nan dan insha Allahu aurensu za'ayi,anjima ma zani gidansu".
Abida dae batace qala ba illa tashi da tayi ta barsu a palourn zaune,d'akinta ta koma inda ta kunna fan ta kwanta abunda,bata jima ba tayi bacci dama a gajiye take.
Bayan barinta palourn kuwa Ammee da Fahyim cigaba da hirarsu sukayi.Fahyim yace da Ammee karta je gidan tukunna ta bari sae sunyi magana da maman nata a waya,kwae dae ta bari ba yau ba sae yah sake tunani a kai.
Tace toh "toh ba komai Allah yah kaimu lokacin yah kuma zab'ar da mafi alkhairi".
Fahyim yace "ameen Ammee".Daga nan suka tashi suka bar palourn dukansu.Ammee ta kashe socket din tvn.
Ta shiga d'akinta Fahyim kuma yahyi side d'inshi yanata tunanin yadda zai b'ullo wa lamarin,dan abun yah dameshi ace yarinyar dayake soh qanwarshi bata sonta,gaskiya akwae sakel.
**************************
Wani chocolate meh suna coucous ta d'auka tana bud'ewa,hankalinta kwance tanayi tana kallon tashar mbc bollywood.Suhana kenan,sarauniyar kyawawa.
Can wajen azahar dan har an fara kiran sallahr ma ta tashi ta tattara shirgin kayan ciye-ciyenta ta koma d'akinta dasu,a kan drawern gadon ta ajiye su kafin ta koma palourn inda ta d'au wayarta da gyalenda ta ajiye shi nan kan kujera ta mayar d'aki,wayarta ta jona yana charge.
Bayan nan saeta shiga toilet,bata fito ba saeda tayi wanka tayi alwala sannan tazo ta shirya.Bayan ta sauya outfit d'inta saita yi sallah.
Bayan ta idar da sallahn saeta kira Hadiza meh aiki,ba tareda jimawa ba Hadiza tazo dan jin kiran da tayi mata,Hadiza yarinya ceh meh jin magana da girmama na gaba da ita.
Tana isowa tace "gani anty",Suhana tace "shigo ki d'ebi kayana dana cire ki wanke mun kafin a d'auke wutar".
Hadiza tace "toh"sannan ta shiga d'akin ta d'ebi kayan sannan ta fita dasu zuwa wajen da suke wanki,ta zuba kayan,ta saka omo da sabulun wanki tareda zuba ruwa sannan ta kunna washing machine d'in,bayan yah gama yinsa saeta cere ta d'auraye tayi spinning kafin ta d'an shanya.
After five minutes taje ta kwashe su a shanyar tazo ta goge dan tasan sarae Suhana bata son barin kayanta a shanya a cewarta yana kud'arda kaya,shiyasa in zata mata wanki sae tayi spinning saboda yyi saurin bushewa.
************************** Suhana kuwa baccinta ta kwanta yi,bata jima ba baccin yah d'auketa,cikeda kwanciyar hankalin ta gama da registration,dan yanzu attending lecture neh kwae yah rage mata,kuma sae bayan 2weeks,result kuwa yyi kyau dan duk iyashege da sakalcin tannan tana mugun jaa.
Both maman ta da babanta suna da ilimi,tayi gado gabada baya kenan.
Wajen qarfe uku da rabi maman Suhana ta dawo gida,koda ta shigo saeta tambayi Hadiza cewa Suhana ta dawo kuwa.
Hadiza tace "eh,ai tun safe ta dawo dan kina fita befi da minti talatin ba itama ta dawo".
Maman tace "ohk",saeta nufa d'akin Suhanan inda ta tarar tana bacci dan haka batace mata qala ba saeta futo,gudun karta tashe ta ma a hankali take tafiyar,harta fita ta rufo qofar kuwa bata tashi ba.
D'akinta ta koma inda ta ajiye shirginta itama tayi alwala dan an kira sallahn la'asar lokacin.Bayan tayi sallahn saeta d'an kishingid'a da jikin gadon tana latsa wayarta cikeda kwanciyar hankali.
Bayan fitar Maman daga d'akin Suhana wayarta tayi qara alamar shigowar message,qaran neh yah tashe ta daga baccin da takeyi.
Ta d'an jima a kwance kafin ta tashi ta zauna,nanma saeda ta d'au lokaci kafin ta tashi daga kan gadon,wayarta taje ta duba dake charging,yana 75% neh yanzu dan haka bata cire ba,ta duba time taga to four neh yanzu.
Toilet ta shiga tayo alwala tazo tayi sallah sannan ta fita daga d'akin,fridge tace ta sha ruwa tareda d'aukan wani sauran cake ta kira Hadiza tace ta d'an mata warming nashi,Hadiza ta karb'a taje warming d'inshi.
Ganin qofar maman kamar a bud'e yasa Suhana nufan wajen,inda ta bud'e ta shiga,a qasa ta samu maman tana latse-latsen waya kamar yadda ta saba.
Ta shiga tana tambayar ta "yaushe kka dawo Mommy?".maman ta d'ago kai tana kallonta kafin ta answer.
"ban jima ba,na shiga d'akinki ae na samu kina bacci shine ban tasheki ba".
Suhana ta qarsa ta zauna,cewa tayi "ae wllh tsaban gajiyan da nayi neh koh jinki banyi ba,dan tun qarfe shabiyu da rabi ina jin na kwant,yanzun ma qaran waya neh yah tashen".
Maman tace "ae kuna fama,ina dae yanzu kam kin kusa gamawa?".Suhana tace "ae nikam ma na gama,karki ga layi kuwa".
"hmm,kice kinyi a sa'a kekam"inji maman,Suhana tace "iyi wllh".Haka suka cigaba da hirarsu harda dariya.
Can Suhana taji bud'e qofar d'akinta,tasan be wuce Hadiza bace ta kawo mata cake d'inda tasa ta warming ba,dan haka ta tashe tana fad'in.
"barin karb'o cake wuri Hadiza naji kamar ta kai mun d'aki",Mommyn tace "ohk,kawo mana nima zan d'an ci tunda da zafi",Suhana tace "toh",tareda barin d'akin.
D'akinta ta nufa inda ta tararda Hadiza riqeda plate d'in cake d'in.Ta karb'a tareda cewa "tnks",sannan ta d'an yanka mata ta bata.
Hadiza tace "nagode anti",cikeda jin dad'i,Suhana batace komai ba sae barin d'akin da tayi Hadiza na biyeda ita.
*HAMAGEE*
[7:25pm, 3/30/2017] Hamagee: garbahama69@gmail.com
💦 💦💦💦 💦
*LAIFIN WAYE??*
💦💦💦 💦💦💦
_Written by the Aplomb writer: *Hamagee*_
*In devotion to Maman Saif*
💦
*Sometimes that mountain you've been climbing is just a grain of sand. What you've been out there searching for forever is in your hands.*
http://www.hamageenovelsseries.com/facebookpage
Page 10 💦💦
D'akin Mommy ta shiga kai tsaye,inda ta kai musu cake d'in suka ci tare,Suhana ta tashi tareda fad'in "ina zuwa Mommy",maman tace "tow",Suhana ta fita taje ta d'auko musu hollandia milk drink ta kawo da cup.
Ta zuba tasha sannan ta sake zubawa ta ajiye wa maman,haka suka d'anyi chilling that very moment together.
***************************
Tunda Fahyim yah shiga d'akinshi yake tunanin amincewa da batun Suhana,yana sonta matuqa saedae ba zae so ace bada son Abida zaiyi neman ba dan ta jima tana d'okin irin wannan ranar.
Ranarda zaeyi mata albishir na yah samu macen da tayi mishi,har addu'a take mishi na Allah yah bashi mata ta gari,yanzu kuma ace hakan ta faru!
Saedae kuma baya jin zae iya rabuwada Suhana,dan yasan ko ba dad'e koh ba jima zasu sasanta kansu,da wannan maganar yah tsaida shawarar shi.
Washegari da yamma suna zaune da Ammee yake ceh mata ya gama shawarar shi akan Suhana,yace "Ammee duk sanda kka samu lokaci kiyi ma mamanta maganar,Abida kuma nasan yadda zanyi da ita".
Ammee taji dad'in batun nashi dan haka tace mishi "karka damu insha Allahu komai zaiyi kyau,zamuyi maganar da ita kafin kaje gidan nasu".
Yace "nagode Ammee",tace "ba komai ai hakki neh a kaina in samar muku farin ciki dukkanku,gobe Abbanku zae dawo daga Saudi,ka sani koh?".
Yace "eh munyi waya d'azunnan ae",tace "toh yyi kyau,Allah yah kaimu goben da rai",yace "ameen".
★★★★★★★★★★★★★★★★
Washegari da wuri Ammee da Abida suka fara gyaran gida,though ba wae datti gidan yyi amma saeda suka gyarashi,aka gyara side d'in Abban.
Girke girke sukayi kala-kala,around hud'u na yamma yah iso,Fahyim neh yaje yah d'auko shi,tareda Abida suka tafi.
Bayan sun d'auko shi gida suka dawo kai tsaye kowannensu na murnar dawowarshi.Shima Abban murnar yakeyi da d'okin gida.
Yah tambayi Abida "yah school mamana?",dama haka yake kiranta dan meh sunan mamanshi ceh.tace
"lfya klou Abba har na gama registration jiya",yace "that's great,Allah yah bada sa'a",tace "ameen".
Bayan sun isa basu tsaya cire kayan nashi ba suka shiga gidan tsaban d'oki,Ammee ma tayi murna sosae ganin dawowarshi lafiya.
Bayan sunyi murnar su sun gama saeya shiga d'akinshi Ammee nah biyeda shi,su Fahyim kuma waje suka koma inda suka d'auko duk wani ilahirin kayanshi dake motar suka shigo mishi dasu.
Bayan Abba yah gama wanka yasa kaya sae suka fito inda suka had'u gaba d'aya full house d'in in banda Adda Fati da tayi aure.
Saeda suka gama cin abincin su kafinnn kowa yah dawo palour yah zauna inda suka soma hirar yaushe gamo kamar basu tab'a yin magana ba tunda yah tafi.
Around 5:30 Adda Fati da mijinta sukayi sallama a gidan,inda kowannen su yah answer kafin suka shigo,gaisawa suka yi dukkansu.
Sukayi ma Abban sannu da dawowa,shikuma wasa yah shiya yiwa Ihsaan wacce harta fara iya magana saedae baiyi qwari ba dan tana cikin shekaru biyu kenan yanzu.
"Anya zan iya da wannan amaryar kuwa? Bbu baki ba qafa har yanzu saema wani kunyata da takeji!",inji Abba kenan,yana yima Ihsaan wasan kaka.
Dariya sukayi dukkansu Ihsaan kuwa ta tsura mishi ido kamar tv,bayan mamanta taje da gudu tasa kuka dan ba qaramin qiwa takeda shi ba daman.Koh kyakyawan kallon da be gamsheta ba akayi mata toh kuka takeyi,balle kuma mutum yyi mata magana.
Dariya suka sakeyi Ammee na fad'in "lallae naci gari,tunda kaida amaryar taka kun b'ata daga zuwanta".
Abba yyi dariya kafin yace "ae wannan amaryar kam baqauyiya ceh,ace daga ango yyi magana sae kuka?".
Fahyim yace "uhm uhm fah Abba karta tafi kazo kana daka sani,dan yanzu kaga a gaban Ammee kke,saeka bar nan kazo kana damuwa,gara ka lallab'ata kwae".
Ammee tace "ba wanin nan amaryar da take tsoronshi harda kuka meh zaiyi da ita".Dariya sukayi duk tasu.
Abida tace "keh dae Ammee na ganeki,kishi neh kwae keh damun ki ba wani bun ba".
Haka sukayi ta raha a tsakaninsu suna dariya,daga bisani su Adda Fati sukayi musu sallama kafin su tafi,Fahyim da Abida neh sukayi musu rakiya dama mijin Adda Fatin abokinshi neh sosae.
Bayan sun musu rakiyar har saeda suka bar haraban gidan kafin suka dawo ciki.
Da daddare Ammee da Abba suna zaune a palourn shi sae Ammee take ceh mishi daman akwae maganar da take so suyi.
Abba yace "tah me kenan?",Ammee tace "akan yaronnan neh Fahyim,yaga wata yarinya yace yana soh,kuma abun dad'in shine y'ar close friend d'ina ceh,ina Haj.Fati wacce mukayi secondary school da university tare?".
Abba yace "qwarae kuwa na ganeta!",Ammee tace "toh her very daughter,kasan daman y'arta d'aya ceh ba?",yace "haka".
Tace "toh ita",Abba yaji dad'in batunnan sosae.Yah dubi Ammee kafin yace "toh bbu abunda zance sae Alhmdulillah,dukkanin godiya yah tabbata ga Allah mad'aukakin sarki daya kawomu zuwaga wannan lokacin,tabbas na jima ina jiran zuwan wannan rana,dan na matsu daya fidda mata yyi aure kasancewar yanzu yah mallaki hanklin kanshi kuma yah kai matakin yin iyali,dama ina son yin maganar daga nah dawo sae kuma Allah yasa zaki riga tara ta da maganar",
Ammee ta d'an nisa kafin tace "toh ae mun gode Allah,yanzu neman mishi izinin fara nemanta yake soh ayi dama,shine nace saeka dawo".
Abba yace "hakan yyi kyau,kuma insha Allahu zuwa gobe zamu ga yadda za'a yi akai,kuma zan samu abokin nah wanda muka riga mukayi magana dashi kan zamu had'a yaranmu aure,na tabbatar zae fahimta dama akan complain danayi mishi neh kan yaron baya son yin aure har yanzu yaqi fiddo mata,sae yake cemun wllhi shima babbar matsalarda take damunshi kenan,wae har yanzu basu samu wanda yah dace da y'arsun ba amma sae soh mu had'asu aure".
Ammee tace "amma ba zae ji dad'i ba gaskiya",Abba yace "iy toh yah za'ayi? Nasan zae fahimta ae ba wani abun zuwa goben insha Allahu zamuyi maganar dashi danma baya qasar neh yanzu yah tafi kasuwanci amman da mun had'u dashi mun tattauna by face zai fi".
Ammee tace "hakane,Allah yah shige mana gaba toh",Abba yace "ameen ameen,yanzu na gaji barinje in kwanta koh zan samu hutu".
Ammee tace "wallahi kuwa,barinje in kawo maka shayi naji weathern da d'an sanyi zaka fi jin dad'in baccin".
Yace "yauwa Indo tah dakin kyauta wallahi,kamar kin san nayi missing irin tea d'inki,wallahi harna dawo ban tab'a shan irin tea d'inki ba,keta daban ceh".
Ammee data tsaya tana kallonshi cikeda fara'a a fuskarta tace "Allah saki,nasan zakayi missing shiyasa nace barin kawo maka koh ka samu hutu meh dad'i".
Yace "toh godiya nake",tace "my pleasure",tashi tayi ta barshi a palourn ta nufi kitchen inda ta daura ruwan tea d'in kafin ta zuba kayan kamshi dasu ganyen shayin.
Abba kuwa bayan ta fita tashi yyi yah nufa d'akinshi inda yyi shirin bacci,yyi alwala yyi shafa'i da wutiri,bayan yah idar saeya hau kan gadon yana jiran shigowarta.
Be jima da kwanciyar ba tayi sallama yah answer kafin ta shigo riqe da flask d'in shayin da cup na sha,akan side drawer ta ajiye sannan ta fita palourn shi ta d'auko kwalin sugar inda ta sa mishi cubes uku a cikin cup d'in.
Bayan tasaka saeta zuba tea d'in a ciki,saeda tayi starring nashi ta tabbatar sugarn yyi melting kafin nan ta miqo mishi yana kwance yana kallon ta.
"Here you go" ta fad'a sanda ta miqa,shi kuma tashi yyi yah karb'a kafin yace "tanks my Indo",dariya ma yah bata daya ceh Indo,duk da cewa hakan yake kiranta koh da yaushe amma wannan karon dariya yah bata.
Yace "au yau kuma dariya na baki?",tace "sosae ma",nan suka cigaba da shan hirarsu yana yi yana shan shayinshi harya gama,Ammee ta tashi ta fitarda cup d'in sannan ta kawo wani koh anjima zaisha.
Ba kad'an ba Abba yaji dad'in shayin nan dan har santi yyi tayi,be d'au lokaci ba yyi bacci.Ammee ma baccin tayi bayan ta gama abunda zatayi.
B'angaren Fahyim kuwa alla alla yakeyi gobe tayi samun yyi wa Abba albishir kan yah samu matar aure,dan sarai ya san yadda yah matsa mishi kan maganar dukda cewa ba wani girma yyi ba amma kuma ya samu abunyi da wuri yanda zae iya riqe iyali ba tareda neman wani tallafi ba.
Abunda yasa yau kuma be sanarda shi ba saboda ganin yau yah dawo kuma yanada buqatar hutu shiyasa yah yanke shawarar gobe kafin Ammee ta riga sanar mishi shi zai fara fad'a mishi.
Kuma yasan Abba zaiyi murna da hakan qwarai.Da wannan tunanin yyi bacci ba tareda yasan lokacinda baccin zae d'aukeshi ba.
****************************
Washegari da asuba Abba yah tashi,alwala yyi kafin yazo yah tashi Ammee.
Saeda yah tabbatar tah tashi dan harta shiga toilet kafin yah fita.Yana fita kuwa kai tsaye ya nufa side d'in Fahyim.
"Kai Fahyim ka tashi kuwa? Lokacin sallah yyi fa!",Fahyim da already yah tashi har ya shiga yin alwala yace "na tashi Abba,yanzu alwala nakeyi",dake qofar toilet d'in a bud'e yah bari,shiyasa Abba yah ji shi.
Cewa yyi "toh yyi kyau"sannan yah tafi abunshi,shi kuma haka yake indae yana gida toh sae yah tabbatar iyalanshi sun shaida cewa lokacin sallah tayi musanman ta asuba.
Bayan yyi alwalan saeya fito ya nufi masallacin shima.
Ammee kuwa bayan ta fito daga yin alwalan,d'akin Abida ta nufa,tana shiga ta tasheta,Abida batada wuyan tashi ba kaman lokacinda Adda Fati take nan ba,ita da har sae an watsa mata ruwa sometimes kafin take tashi.
Abida kuwa magana kwae na iya tashinta barinma da asuba tana saurin tashi.
Bayan Ammee ta tasheta saeta bar d'akin,d'akinta ta nufa tayi sallah.
Abida kuwa tana tashi ta shiga tayi alwala tazo tayi sallah.
Tare su Abba suka dawo daga masallaci suna hirarsu,suna shigowa lokacin kuma Abida ta fito daga d'akin Ammee,gaisheta taje tayi kamar yadda ta saba,bama ita kad'ae ba haka ta taso taga yayyunta nayi.
Nan take ta tsuguna har qasa sannan tace "ina kwana Abba",Abba yah answer cikeda fara'a
"Morning mamana,kin tashi lafiya?",tace "lafiya klou",kafinnan ta tashi ta gaida Fahyim ma "ina kwana yaya Fahyim",Fahyim yah answer "lafiya klou,kin tashi klou koh?",tace "lafiya lou".
Bayannan saeta koma d'akinta inda tabi tsawon gado dan bacci be isheta ba.
Abba ma d'akinshi yah nufa yah kwanta,haka Fahyim mah baccin shi yaje yah koma.
*HAMAGEE*
garbahama69@gmail.com
💦 💦💦💦 💦
*LAIFIN WAYE??*
💦💦💦 💦💦💦
_Written by the Aplomb writer: *Hamagee*_
*This page is yours ANEELURV,you're just sweet and dear some,#ILYSM* 😘
💦
*Somewhere someone is thinking of you. Someone is calling you an angel. This person is using celestial colors to paint your image. Someone is making you into a vision so beautiful that it can only live in the mind. How your eyes close and your jaw tightens with concentration as you give pleasure a home. These thoughts are saving a life somewhere right now.Someone is calling out to you silently and you are answering without even being there. So crystalline. So pure. Such life saving power when you smile. You will never know how you have cauterized my wounds. So sad that we will never get to see each others,but maybe some days. How it hurts me to know that I will never be able to give you everything I have.You people are making my day,I never known that I'm having such loving and caring fans untill when I met you people@my facebook fans#ILYSSM*
http://www.hamageenovelsseries.com/facebookpage
Page 11 💦💦
Bayan sunyi breakfast Abba da Ammee na zaune a palourn Abba suna kallon news,Fahyim neh yyi sallama sannan yah shiga bayan sun answer.
"Sannunku da hutawa",inji shi su kuma suka ceh "yauwa".Abba yah dubeshi yace "akwae magana a bakin kannan,fad'i meye damuwarka?".
Fahyim yah d'an sosa qeya kafin yace "Abba dama nazo roqonka abune",Abba yace "name neh? Fad'a mun koma miye zan baka in inada shi".
Fahyim yace "dama ranan neh naga wata yarinya kuma Ammee tace mun y'ar qawarta ceh,shine shin..nshine nake so ka nema mun.n"sae kuma yyi shiru.
Dariya Abba da Ammee sukayi,Abba yah qarasa mishi "aurenta right?",Fahyim da idonshi keh kallon qasa yah d'ago yana kallon Abba kafin yah answer da "eh",cikeda jin kunya kamar wani mace.
Abba yace "shine kke inda inda? Ae wannan great news neh dan haka karka samu damuwa yau d'innan za'a jeh nema maka aurenta,har nayi magana dasu baffanunku dan jiya Ammenku ta sanarda ni komai".
Fahyim yah ji dad'in maganar Abba sosae,ashe har Ammee ta fad'a mishi! Ashe ma da maganar yah kwana tunda har yah sanarda su Babbafa.
Yah dubi Abba yace "nagode Abba",Abba yace "you don't need to son,Allah yyi maka albarka",Fahyim yace "ameen Abba".
Ammee ta dubi Fahyim kafin tace "yanzu hankalin ka yah kwanta koh?",kunyar maganar yaji shiyasa bece komai ba saeya tashi yace "barinje in shirya zani office".
Abba yace "toh saeka fito",Fahyim yah fita zuwa d'akinshi ranshi fari tass.
Bayan yah shirya saeda yazo yyi musu sallama suka sa mishi albarka kafin yah tafi,Abida dake zaune a palour tana kallon *Joyprime* inda ake maimaichin *JODA AKBAR*.
Ganin zae fita yasa tace mishi "a dawo lafiya yaya!",Fahyim yace "yauwa Abida,Allah yasa",tace "ameen,yaya in ka samu season 25 & 26 na KING OF HEARTS dan Allah ka sayo mana ance mun yah fito".
Fahyim yace "ohk insha Allah zan duba,amma anjima ki kirani ki mun tuni karna manta",tace "toh".Yah fita.
Tare suke kallo dama dan shima mayen Indian film neh shiyasa yake sayo musu daga yaji wani meh dad'in yah fito.
***************************
Suhana nah kwance a kan sofa tana latsa wayarta cikeda kwanciyar hankali.
Tana cikin haka Mommynta ta shigo palourn da annashuwa a fuskarta,tazo ta zauna a gefenta kafin tace "Duba ki gani"ta miqa mata wayar dake hannunta.
Suhana ta tashi kafin ta karb'i wayar,Mommyn tace "cikin su ki zab'i set biyu wa'inda sukayi miki Daddynki neh yah turo mun su yanzu wae yana shagon neh so mu zab'a kafin yah saya".
Shagon saeda gold Daddyn yaje shine yah d'au hoton wasu yah tura mata akan ta zab'i wanda yyi mata saeta bama Suhana ma ta zab'a nata dukkansu kala bibbiyu zasu zab'a,shine yanzu tazo nuna ma Suhanan ita already ta zab'i nata harta tura mishi.
Suhana cikeda murna ta shiga duba hotunan tana rawar ido,kowanne ta gani tace yyi mata kyau.
Can tazo kan wanda maman ta zab'a already tace yyi mata sannan ta nuna wani,Mommyn tace "na rigaki wannan ai,ki zab'i wani kalan kwae".
Suhana tace "nidae shi nakeso"cikeda shagwab'a kamar meh shirin yin kuka,ita atapirr wannan design d'in take so.
Ganin ta nace yasa Mommyn haqura ta zab'i wani daban sannan ta tura mishi,bayan yah gama saya saeya sake d'aukansu a waya yah tura mata dan ta dad'a tabbatarwa sune wa'inda suka zab'a.
Mommy ta tabbatar mishi da cewa sune kafin nan yah biya yah bar shagon.
Murna wajensu ba'a magana musanman ma Suhana tafi murna dan designs d'inda ta zab'a sun had'u gasu they're so unique.
*_Sorry with the short page,I'm having a serious backache that's why I can't type much..#ILYALL_*
*HAMAGEE*
garbahama69@gmail.com
💦 💦💦💦 💦
*LAIFIN WAYE??*
💦💦💦 💦💦💦
_Written by the Aplomb writer: *Hamagee*_
*In devotion to Maman Saif*
💦
*Build your own dreams, or someone else will hire you to build theirs.The only thing that stands between you and your dream is the will to try and the belief that it is actually possible.*
http://www.hamageenovelsseries.com/facebookpage
Page 12 💦💦
Around qarfe goma sha d'aya da rabi ba na safe su Baffa Saeed da Baffa Aminu tareda wani best friend na Abba wato Alhj.Kamal suka d'auki hanyarsu ta zuwa gidansu Suhana dan yin tambaya da gaisuwa.
Mommy na kwance tana latsa wayarta lokacinda Hadiza tayi sallama,ansawa tayi tareda bata umarnin shigowa.
Koda Hadiza tah shigo saeta dubi mommy kafin tace "hajiya anyi baqi neh shine nazo sanarda keh".
"Baqi kuma? Wasu irin baqi?"Mommy ceh tayi tambayar tareda d'agowa daga jinginon da tayi a jikin gatonta na alfarma.
Hadiza tace "eh baqi,kuma maza neh,su uku inaganin alhaji suka zo nema,amma bance musu baya nan ba kawae nace barin zo in fad'a muku neh".
Mommy ta d'anyi shiru na lokacin kad'an tana tunanin suwaye baqinnan,a iya tunaninta batayi zaton kowa ba tunda Daddyn Suhana ba wasu abokai yakeda su ba,kuma in yana dasu ai yah kamata ace sun san da tafiyar shi.
Ta dubi Hadiza kafin tace "kice su shiga palourn Daddyn Suhana saeki kai musu snacks da drinks ina zuwa".
Hadiza ta answer da "toh" kafin ta nemi hanya ta fita,umarninta taje ta cika bbu wani mishkila a ciki sannan ta koma kitchen inda take taya Mama Talatu da wasu aikace-aikace a kitchen.
****************************
Bayan d'an wani lokaci Mommy tah fito sanyeda gyale a jikinta dan kayan jikinta irin Arabian gowns d'innan neh kuma marasa shape.
Palourn da baqin keh zaune ta nufa,kafin ta shiga tayi sallama suka answer,bayan ta shiga saeta nemi guri ta zauna sannan suka gaggaisa,ita dae har a lokacin kallon rashin sani take musu dan bata gane koda d'aya daga cikinsu ba.
Murmushi ta d'anyi kafin tace "kunzo neman meh gidan koh? Gashi ban ganeku ba".
Baffa Aminu neh yace "gaskiya neh bazaki sanmu ba,munzo wajen meh gidan neh da kuma keh,daga gidan Hajy.Aisha qawarki muke".
Cikeda nuna kulawa tace "Allah sarki ai ban shaida ku ba? Lafiya dae koh?",Baffa Saeed yace "lafiya qlou,nidae qanin meh gidanta neh,haka ma wannan",saiya nuna Baffa Aminu.
"wannan kuma aminin shine",tareda nuna Alhj.Kamal.Mommy tace "Allah sarki,gidan duk qlou ae?",sukace "lafiya,Alhmdullh",tace "toh madalla,sannunku da zuwa!!".
Sunji dad'in yadda ta qarb'esu matuqa dan har godiya sukayi tace ba komai.
Alhj.Kamal neh yah gyara murya kafin yace "toh! Yanzu dae babban maqasudin zuwanmu nan shine dan nemawa d'anmu wato d'an gidan Alhj.Sadeeq auren y'ar wajenku saedae kuma Mahaifinta baya nan".
Mommy tace "tohh",saeta d'anyi shiru kafin ta sake cewa "karku damu,whether yana nan koh baya nan it would'nt change anything don na tabbatar shima zaiso had'a alaqa da duk wani d'anda yah zo ta wajen hjy.Aisha".
"saboda haka karku samu wata matsala san sanarda shi duk yadda mukayi,shi kuma yaro ku sanarda shi cewa zai iya zuwa duk lokacinda yaso,fatana shine Allah yah zab'a mana mafi alkhairi".
Sukace "ameen".Duk tasu sunji dad'in yadda tayi na'am da buqatarsu,daga bisani sukayi mata godiya tareda yin sallama sannan suka tafi.
Taji dad'in al'amarin sosae dan duk wanda yah san haj.Aisha toh dole yaso had'a alaqa da ita dan mutuniyar arziqi ceh danma yanzu da girma yazo musu basu cika yin zumunci a tsakaninsu ba.
Duk abunnan da akayi Suhana na bacci bata ma san anyi wasu baqi ba balle tasan koh dame suka zo.
Duk tunanin Mommy ta yaya zatayi Suhana ta amince da batun nata dan sarae tasan halin Suhana zaiyi wuya ta yarda dashi.
Saedae ta sha alwashin bazata bar wannan damar ta wuce ta ba dan wannan babban dama ceh tazo musu kuma in suka cigaba da biyewa Suhana toh haka zata zauna batayi aure ba dan har yanzu bata san abunda yah dace da ita ba koh kad'an.
Da wannan tunanin Mommy ta koma d'akinta ta kwanta.
••••¶¶•••••¶¶¶•••••¶¶¶•••••¶¶••••
Bayan tafiyarsu Baffa zuwa gidansu Suhana,Abba yah kira abokin shi da sukayi magana kan had'a ya'ya'nsu dan yah bashi haquri kan abunda yah faru.
Ringing d'aya,ana biyu yah d'aga wayar,bayan sun gaisa kamar yadda suka saba sae yake ceh mishi "wllh na kiraka kan batun maganar yarannan neh".
Abokin yace "toohh Allah sa dae ba wani abun bane yah faru?".Abba yace "eh toh! It's nothing much,kawae maganar had'a su da mukayi magana a baya neh bazae yiwu ba.Unfortunately jiya bayan na dawo daga tafiya sae ake sanardani cewa yah ga wata yace yana soh,yanzu dae maganar da mukeyi d'innan harna tura aje ayi tambaya dan gaskiya naga yana son abun sosae".
Abokin yace "Allahu akbar,ae haka ake soh dama,rashin nuna abokin zaman neh dama yasa zamuyi had'in,toh yanzu kuma ai sae mu gode ma Allah daya kawo mana abun da sauqi.Nidae fatana kwae shine d'iyata ta samu wanda zae dace da ita".
Abba yace "insha Allahu zata samu,kuma na gode daka fahimci matufata,Allah yah qara zumunci da qauna".
Abokin yace "ameen.Allah yasa mu gama da duniya lfiya".Abba yace "ameen".Sallama sukayi kafin Abba yah yi hanging call d'in cikeda jin dad'i.
Koda yah sanarda Ammee yadda sukayi,tayi murna da kasancewar yah gane manufar Abba ba tareda jin haushi koh wani abun ba.
Like I told you yesterday,I'm having a serious backache,just need your prayers for my healing..# One luv for you all #Team LW
*HAMAGEE*
garbahama69@gmail.com
💦 💦💦💦 💦
*LAIFIN WAYE??*
💦💦💦 💦💦💦
_Written by the Aplomb writer: *Hamagee*_
*In devotion to Maman Saif*
💦
*Love what you have. Need what you want. Accept what you receive. Give what you can. Always remember, what goes around, comes around..*
http://www.hamageenovelsseries.com/facebookpage
Page 13 💦💦
Mommy nah kwance wayarta tayi ringing,batareda b'ata lokaci ba tayi picking,gaisuwa na mutunci da abota sukayi.Hajya.Aisha ceh ta kirata.
Ammee tace "kinga baqi rana tsaka koh?",Mommy ta d'anyi dariya kafin tace "wallahi ba komai,naji dad'in zuwansu.Allah dae yah bar zumunci".
Ammee taji dad'in maganganun Mommy sosae,tace "Ameen.Wallahi naji dad'in abunnan,nidae banida abunda zance sae nagode kuma Allah yah had'a kansu".
Mommy tace "ameen ameen,karki damu insha Allahu bazaku samu wata matsala damu ba,shi kuma yaron duk sanda yah samu time zae iya zuwa".
Ammee tace "toh madallah,Allah yah bamu tsawon kwana muga aurensu".
Mommy tace "ameen",bayan sun gama tattaunawa sae sukayi sallama kafin nan Ammee tayi hanging call d'in.
Bayan sun qare wayar sae Mommy ta kira numbern Daddyn Suhana,ringing nah farko yah d'aga yana fad'in "hello wife!".
Mommy tace "hy,ina gajiya?",yace "ba gajiya",bayan sun gama gaisuwarsu na yah gida yah Suhana yah aiki?.
Sae Mommy tace "wata magana nake son fad'a maka".Yace "tah miye fah?".
Mommy tace "Allah yah kawo ma Suhana mijin aure,d'azunnan aka zo neman ma yaron izinin fara nemanta,kasan d'an waye?".
Daddyn Suhana da yah d'anji wani iri saeya ceh "aa d'an waye?"yah mayar ma irin zaiji ta ambato sunan wani meh kud'i neh tace d'anshi,sae yaji tace
"D'an haj.Aisha qawatan nan,ka tuno ta koh?"yah d'anyi ajiyar zuciya kafin yace "tabbas na tuno ta,ai tanada kirki sosae".
Mommy tace "ai ka bari kwae,ba ita kad'ae ba har mijinta nada kirki shiyasa ma kaga banyi sanya ba wajen amince musu,na farko qawata ceh na biyu kuma sunada kirki sosae.Duk iyayen kirki bazasu qi su had'a jini dasu ba,shiyasa na amince a take,hope banyi laifi ba?".
Daddyn Suhana yace "wallahi bakiyi komai ba,inma zance kinyi wani abun saedae nace kin kyauta amma banda kinyi laifi dan gaskiya nima na yaba na halin haj.Aisha dukda cewa ban san mijin nata ba amma ita tanada kirki,saedae ince Allah yah wuce mana gaba".
Mommy cikeda jin dad'i tace "ameen mine! Saedae wani hanzari ba gudu ba!".
Yace "name kenan?",tace ban sanarda Suhana ba kuma kasan halinta sarai,fatana dae Allah yasa karta ceh bata sonshi kasan ta".
Daddy yah nisa kafin yace "kinyi magana,amma karki damu koma miye zata amince dan gaskiya bazamu sake barin wannan damar ta wuce mu ba tunda yaron nada hankali nasan zae kula da ita,kome kka gani?".
Mommy tace "gaskiya neh,gashi yaron na aikinshi,lawyer neh fa!".Yace "toh kin gani! Karma kiyi mata maganar ki bari saeya zo inyaso sa sasanta kansu".
Mommy tace "gaskiyar ka,sae yah zo d'in kwae".Bayan sun gama maganar sae suka canza chapter sukasha hirarsu kafin Mommy tayi hanging call d'in,hakanma dan taji kiran sallah neh.
Bayan tayi alwalan saeta jeh d'akin Suhana dake bacci kamar kasa bata ma san ana kiran sallah ba,ta tasheta kafin taje tayi sallahn nata.
Bayan Suhana ta tashi toilet ta shiga tayi alwala sannan ta fito tayi sallah itama,saeda tayi isha kafin ta fito palour.
Bayan sunyi dinner saeda suka sha hirarsu kafin kowannensu yaje yah kwanta.Kamar Mommy zata fad'a ma Suhana abunda yake faruwa sae kuma ta fasa dan sanin halinta.
°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°
Around 5:30 na yamma Fahyim yyi sallama a d'akin Ammee,bayan ta answer saeta ceh yah shigo,shigowan yyi fuskarshi da annuri.
A gefen gadon Ammee yah zauna ita kuma tana wani gefen,saedae dukansu suna facing juna neh,yah gaisheta ta answer.
Ammee ta dube shi tace "yah akayi? Yanzu hankalinka yah kwanta ina?".
Fahyim yace "bbu komai Ammee,kwae ganin abun nakeyi kamar mafarki,ban zaci gidansu za suyi saurin amincewa ba".
Ammee ta d'anyi murmushi kafin tace "dama nah fad'a maka ka kwantarda hankalinka ai,nasan haj.Fati bazata qi had'a zuri'a dani ba,dan ba qaramin aminci neh a tsakaninmu ba danma yanzu muyi sanyi".
Fahyim yace "toh godiya ta tabbata ga Allah,amma wani hanzari ba gudu ba!".
Ammee ta qura mishi ido tareda fad'in "name fah?",Fahyim yace "irin yadda naga Suhana tayi treatening d'ina ranan,baki ganin zata ceh bata amince dani ba? Kuma kin ceh iyayen basu mata dole!".
Ammee ta d'an saki ajiyar zuciya kafin tace "indae wannan neh toh kada ka damu kanka,tunda maman ta amince kuma ta nuna tana soh koma miye zata san yanda zatyi ta tausasa yarinyar harta amince.D'azu ma munyi waya da ita take cemun nah fad'a maka zaka iya zuwa a ko wane lokaci kke son zuwa".
Fahyim yaji dad'i sosae,yace "zuwa gobe da yamma insha Allahu zanje gidan toh",Ammee tace "Allah yah kaimu goben toh,it's good to take your time".
Yace "ameen Ammee",bayan sun gama tattaunawa sai ya bar d'akin yah koma palour inda yah tararda Abida zaune tana kallon KING OF HEARTS season 26.
Zaunawa yyi shima yana tambayarta abunda yah faru a wajenda baya nan,nan tayi mishi bayani kafin suka cigaba da kallon su cikeda jin dad'i.
°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°
Washegari da yamma around 4:30pm Fahyim yah shirya cikin jamfarshi ash colour,yasha aikin hanu wanda aikin yazo colour d'aya da hularshi wato dark ash.
Kayan yyi matuqar yi mishi kyau.Bayan yah gama shirinsa saeya fesa turare sannan yah d'au keyn mota da wayarshi sannan yah fiton.
Lokacin Ammee da Abba na palour suna hira,yyi sallama suka answer sannan yah shigo yah gaidasu kafin yah musu sallama ya fice.
Daga ganinshi bbu tambaya sun san inda zaeje.Sun ji dad'i ganin yadda d'an nasu yah fara zama responsible yanzu dukda cewa daa d'inma ba wae mutumin banza bane.
****************************
Suhana nah kitchen tana pudding dan yunwa take ji lokacin,anyi jollof rice neh ita kuma bata soh shiyasa.
Bayan ta gama saeta juye shi cikin mug tasa sugar da spoon sannan tah d'auka ta fito palour dashi.
Hankalinta kwance take sha,ta kunna tv tareda canza channel zuwa Zee Aflam.Wani film meh suna Kriish akeyi,tana son film d'in sosae.
Hakan yasa bata canza channel d'inba,a haka harta gama shan pudding d'inta,bayan nan saeta tashi ta nufa d'akinta.
Toilet ta shiga tayi alwala sannan ta fito tayi sallahn la'asar,bayan ta idar saeta koma toilet d'in tayi wanka sannan tazo ta sa kaya bayan ta gama shafe-shafenta.
Light makeup ta d'anyi sannan ta d'au wayarta ta shiga yin selfie,tayi kyau sosae,she's looking take away.Bayan nan saeta je d'akin Mommy.
A kwance kan rug ta sameta alamun dae yanzu ta idar da sallah shine ta kwanta.
Sallama tayi,Mommy ta answer kafin nan ta shiga,Mommy kuwa tashi tayi ganin Suhana,saeda ta qare mata kallo sannan tace
"The beauty is inside you my daughter! You're always looking gorgeous and pretty,you look so beautiful my dear!".
Suhana tace "kaaii Mommy",Mommy tace "Allah you look nice,kinyi kyau".
Suhana taji kanta yah qara huruwa,tace "thank you,yanzu nazo kimun pic neh zanyi posting a IG".
Mommy tace "sure! Zo in miki".Suhana tazo ta miqa mata wayarta inda Mommy ta shiga d'aukanta hoto ita kuma tana canza different styles.
Bayan sun gama yi a d'akin be ishesu ba saeda suka koma palour sukayi wasu,suka jeh waje ma sukayi.
Bayan sun shigo gida sae suka wuce d'akin Mommy inda Suhana ta shiga posting pics d'in a Instagram.
Bayan nan saetayi editing wani tasa a profile pic nata na whatsapp,tayi status again.
Around 5:00pm Hadiza tayi sallama suka answer kafin ta shigo,tana shigowa tace dasu "anyi baqo neh yana waje!".
Mommy sarai tasan dawan garin dan d'azu Ammeen su Fahyim ta kirata take sanarda ita cewa Fahyim yana zuwa yau d'innan.
Tah dubi Hadiza take "shikenan kije",Hadiza tah juya ta fita ba tareda tace komai ba.
Mommy ta juyo tana kallon Suhana kafin tace "jeh ki duba waye beauty!".
Suhana koh zuciyarta d'aya tace "ohk" tareda tashi ta nufa qofar fita,d'akinta ta koma ta sanya gyale dark ash colour dan doguwar rigar jikin light ash ceh sae d'an stones masu dark ash color.
Ta d'au takalmanta ta sanya sannan ta fito ta nufa qofar fita hankali kwance.
A harabar gidan taga motarshi glass a rufe,kuma tinted neh.Murmushi yyi ganin tana zuwa inda yake.
A tunaninshi ma tasan da zuwanshi neh ganin yadda tayi shiganta tayi kyau.
Ita kuwa tunanin inda tasan motar ta fara yi.Kamar ta tab'a ganin motar kwanannan amma bata tuna ko a ina ta ganta ba.
Cikeda takunta nah qasaeta ta isa wajen tana sauraron a bud'e motar taga koh waye.
Ganin ta qaraso inda yake yasa yah bud'e qofar motar yah fito fuskarshi da annuri,yana smiling wanda yake qara mishi kyau,ga dimples d'innan sun bayyana a kumatun shi.Tabarkallah dan badae kyau ba saedae wani abun.
Yana fitowa sukayi ido hud'u dashi,tsayawa kallonshi tayi tana tuno a inda ta tab'a ganinshi,can yah fad'o mata a rai.
Shi kuwa wani irin kyau ta qarayi mishi,komai nata burgeshi yake,godiya ya shiga yi wa Rabbi daya had'ashi da wannan baiwar Allahn,tareda roqon Allah yasa yah samu karb'uwa a wajenta dukda yadda yaga alamun masifa cike a fuskarta.
°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°
Bayan fitar Suhana tashi Mommy tayi taje ta samu Hadiza,tace mata ta shirya kan table da fruits,drinks da kuma snacks,dake kullum basu rabuwa da wa'innan abubuwan a gidan dama.
Hadiza ta ansa tareda zuwa cika umarnin Mommy.tsaf ta shirya komai kan table saura shigowan baqo yah rage.
Bayan Mommy ta sanarda ita kuwa d'aki ta koma inda ta kira Daddy,a ringing nah farko yah answer.
"Hello mine!",inji Mommy kenan,Daddy kuma yah answer da "yah akayi?",tace "yazo yanzunnan,Suhana ta fita,yanzu ban san yadda za'a qare ba!".
Daddy yace "karki damu kanki,ki aika kice su shigo palour yanzu saeku gaisa kafinnan ki basu waje".
Mommy tace "toh shikenan barin aika Hadiza yanzu!",yace "ohk",sae tayi hanging call d'in.
Tashi tayi ta nufa d'akin Hadiza ta sameta,ta qira sunanta kafin tace "kije waje kice masu Suhana su shigo palour yanzun nan".
Hadiza ta answer da "toh",sannan ta tashi tasanya himar d'inta tasa takalma kafin ta nufa waje.
*HAMAGEE*
garbahama69@gmail.com
💦 💦💦💦 💦
*LAIFIN WAYE??*
💦💦💦 💦💦💦
_Written by the Aplomb writer: *Hamagee*_
*In devotion to Maman Saif*
💦
*We learn something from everyone who passes through our lives.. Some lessons are painful, some are painless.. but, all are priceless...*
http://www.hamageenovelsseries.com/facebookpage
Page 14 💦💦
Cikeda tsiwa Suhana tace "kaaii!! Meya kawo ka gidanmu?",shi kuwa Fahyim be damu da abunda tace ba,dariya ma yyi kafin yah answer.
"Haka ake karb'an baqo? Ko danma ba damuwa tunda kin damu dani,don da baki damu dani ba da bazaki ganeni daga had'uwa d'aya ba".
Wani takaici neh yah kamata tace "da ance maka jaka ceh ni da bazan iya recalling face naka ba,banma san kanayi ba ballantana na damu da kai only that nasan naga face naka kuma be jimaba so I can recall it easily".
Dariya Fahyim yyi sannan yace "it's ohk my wife! Yanzu kinyi maraba da zuwana?".
Kafin Suhana ta bashi answer saega Hadiza ta qaraso gurin da sallamarta.
"Assalamu alaikum",Fahyim neh yah answer dan Suhana koh magana bata iyawa tsabagen takaici,na farko yazo har gidansu ba tareda izininta.
Sannan yazo yana fad'a mata maganar banza,waye shi haka? Dame yake taqama da zae gaya mata ba dad'i haka?.
Duk tambayoyin nan a ranta take yinsu.Bata ankara ba taji muryan Hadiza na fad'in "hajiya tace wae ku shigo ciki!".
Fahyim yace "toh muna zuwa,kice muna shigowa",Hadiza tace "tohh" kafin nan ta juya ta nufa cikin gidan,Fahyim kuwa maida kallonshi kan Suhana yyi yana fad'in "muje kou!!".
Suhana ta zamo speechless,dan batada ta cewa,ita dae tana tunanin Mommy ta sanshi neh da zata ceh su shigo bata san wanda yazo ba?.
Samun kanta tayi tana binshi har suka shiga cikin gidan,ita tayi musu jagora zuwa palourn.
Bayan sun shiga zama sukayi kowa a kujera daban,bbu wanda yah tofa komai sae muryan Mommy da suka jiyo tana magana da Hadiza daga alamu kuma palourn zata shigo.
Sallama tayi suka answer sannan ta shigo,har qasa Fahyim yah tsuguna yah gaisheta "ina wuni",tace "lafiya klou,yah gida yah aiki?".
Yace "Alhamdulillah,yah jama'a?",tace "lafiya klou,gidan naku klou koh? Yah Ammeenku",yace "duk lafiya tace in gaisheki".
Mommy tace "tohh ina ansawa",bayan sun qare gaisuwar sai ta fita tabar musu palourn.Suhana koh kallo ta bisu dashi tana son magana ta rasa meya hanata yi.
Tashi tayi tace mishi "zaka iya zuwa gidanmu kuma a karb'e ka amma ni baka kai na karb'eka ba dan haka yafi maka sauqi ka tashi ka kama gabanka dan Suhana is'nt your mate".
Dariya ma ta bashi dan a ganin shi duk abunda take fad'innan na d'an lokaci neh kuma nan bada jimawa ba inta fara sonshi zata daina.
Yace mata "did you really mean your words?",ta harareshi kafin tace "ofcourse yes!!".
Yace "it's ohk then,karki damu zan dawo another day because it seems you're stressed today!".
Yah gama maganar kenan saega Mommy ta shigo,tace "yah dai naganki a tsaye".
Fahyim neh yyi caraf yace "tafiya zanyi!",Mommy tace "tafiya kuma? Yaushe kazo?".Juyawa tayi ta kalli suhana data dake a wajen tana jiran qiris ta tofa na bakinta.
Mommy tasan halinta dan yanzu saeta zubar da ita a gaban shi dan haka batace komai ba saima juyawa da tayi dan karta yi wata maganar.
Tace ma Fahyim "kuma koh ruwa baka sha ba! Da alla da d'an sha koda ruwa neh tukun".
Beyi mata musu ba yah koma ya zauna.Suhana kuwa da ranta yah gama b'aci tajaa tsaki ta tafi ta barsu a wajen.
Bin bayanta Mommy tayi,shikuma ruwa kad'ae yasha hakanma ba don yaso bane dan kwae baya son yi mata musu neh.
Bayan yasha saeya fita yah tafi bayan yyi mata sallama.Bayan fitarshi kuma d'akin Suhana Mommy ta nufa.
**************************
Mamaki neh yah ishe Fahyim wae ace yarinya kamar Suhana ta zauna tana rashin mutunci wa mutane kuma a gaban mamanta? Kuma maman na jin nauyin yi mata magana kamar itace uwar.
Kai anya zai iya da ita kuwa!! Yarinya bbu kwab'a haka! Dubi d'azu fa har tsaki tayi kuma a gaban maman,sannan maman bata jii komai ba sabida ta saba.
Shikam yana ganin kawae zai haqura da ita neh.Duk a zuciyarshi yake maganganun nan.
Da wannan tunanin yah koma gida,jikinshi duk yyi sanyi.
**************************
Bayan tafiyarshi saeta shiga d'akin Suhana inda ta tararda ita sae faman cika take tana batsewa kamar akayi ma pampon iska.
Ta nufa inda take tareda kiran sunanta "Suhana!!",Suhana bata koh juya ba balle ta kalleta tace "uhmm".
"Meyasa baki saurari yaron nan ba? Koh kin san d'an haj.Aisha neh!!".Juyowa Suhana tayi kamar an tab'o mata inda yake mata qaiqayi tace "ohh really? Ae ban sani bane,wato farin ciki d'an qawarki yafi miki nawa koh? Why this sudden change mom?".
"You didn't get me right! Ba haka nake nufi ba,keh kanki kinsan cewa nafi kowa san farin cikin ki kuma ina iya qoqarinah wajen ganin na mallaka miki farin cikin amma ban san yadda kka d'auki abun ba! I'm telling you Suhana this man will surely bring happiness to your life,I promise you this!!".
"This's unbelievable Mom!! Did you really think this is my type? I guess you're mistaken.Karki manta keh kka ce mun I'm not an ordinary girl like others,I'm different and yes I'll marry the man I wish to,toh yet banga wanda ya dace dani ba,why can't you understand and get the point?",Inji Suhana.
Kallo kwae Mommy ke binta dashi,maganganun Suhana hakane dan kyau tanada kyau kuma duk wasu qualities da namiji zaiso agun mace Suhana nada su.
Saedae har yanzu bata fahimceta ba,bata sanma ta inda zata mata maganar harta gane ba.She's just helpless now.
Tace "uptill now you did'nt reach the main point dear,ina gwada miki hanyar da zata b'ulle miki neh nan gaba,kin san dae dole kiyi aure koh?".
Da sauri Suhana tace "for sure na sani amma meyasa kke behaving as if kin gaji dani inba haka ba meyasa zaki had'ani da wannan? Is'nt he so local to me? I think he is'nt my type!!".
Mommy ta rasa yadda zatayi da Suhana daga qarahe dae barin ta tayi akan daga baya sayi maganar in tana good mood amma yanzu isn't the right time da zatayi mata maganar dan be kamata aceh suna sa'insa da ita ba.
Fita tayi ta barta a d'akin,Suhana kuwa koh a jikinta,koh irin ta d'anji bbu dad'i ganin yadda maman taji haushi,koh ajikinta dan bata ma san tana yi ba.
***************************
Bayan Fahyim yah koma gida d'akin Ammee yah wuce straight dan bbu kowa a palourn.
Sallama yyi ta answer sannan yah shiga,Ammee tana mishi kallo d'aya tasan akwae abunda yake damunshi.
Shida yah kamata ace yah dawo cikin farin ciki amma gashi nan bbu annashuwa a tareda shi,koh meyasa? A ranta tayi tambayar.
Ganin ta jira yyi mata magana kuma beyi ba saeta ceh "yah akayi?".
Kamar wanda yake jiranta ta tambayeshi,yace "Ammee nikam na fasa,bazan iya da yarinyar ba ko kad'an bata ganin darajar mutum".
Ammee tace "subhanallah,meya faru kuma?",nan ya sanarda ita yadda sukayi tunda ga zuwanshi har zuwa dawowan shi.
Ammee tace "karka damu indae dan wannan neh,kaidae kwae kayi qoqarin koya mata sonka shikenan,nina fad'a maka wannan indae ta fara sonka toh duk wannan abun baza tayi su ba,kai ba namiji bane? Ai an san namiji da haquri da juriya kan mace,saboda haka karka ceh ka fasa,be kamata kayi giving up tun yanzu ba".
Haka tayi ta kwantar mishi da hankali harya gamsu da maganganun nata,kuma yyi mata alqawarin jure duk wani abunda zaiji koh zai gane daga gareta.
Daga bisani tasa mishi albarka sannan yah tashi yah fita dan har an fara kiran sallahn magrib.Alwala yaje yyi yah tafi masallaci.
**************************
Bayan Mommy ta bar d'akin Suhana nata d'akin ta nufa,daddyn Suhana ta kira,yana d'agawa maganar da yah fara yi itace "yah kuka qare?".
Tace "humm",yace "yah dae?".Tace "wllh bata kulashi ba,infact ma gajiya yyi yah tafi.Na rasa meye damuwar Suhana,when I tried to convince her kuma she turned into deaf ear to me".
Daddyn yace "just let it be,I'll call her later yanzu ina aiki neh,karki damu kanki please I'll talk to her kinji?".
Mommy tace "shikenan,nima zanje inyi sallah yanzu kam,sae zuwa anjima koh".
Yace "ohk,Allah yah kaimu",tace "ameen",sukayi sallama kafin tayi hanging call d'in.
Tashi tayi ta shiga toilet tayi alwala sannan ta fito tayi sallahn magrib d'in.Bayan isha sukayi dinner kafin suka kwanta.
**************************
*Days later...*
Da wuri Suhana ta tashi yau dan tanada lectures kuma akwae meh 8-10,bayan tayi sallah saeta yi wanka ta shirya.
Bata wani yi breakfast d'in kirki ba ta tashi tayi ma Mommynta sallama kafin nan ta tafi.
Tana isa lokacin qarfe 7:40 neh so batayi latti ba,zama tayi a wani d'an corridor tana danna wayarta kafin lokaci yyi,lecturern da zai shiga musu baya yin late shiyasa kowa yazo da wuri.
Sannan idan yah shiga bbu meh shiga kuma,saedae mutum yyi missing class d'in,shi kuma dokar shi kenan.
Ana cikin haka yah shigo school d'in lokacin 7:55 tayi already.Daedae lokacin kuma Suhana ta tashi kenan taje siyan notebook dan ta gama mantawa bata zo da littafi ba.
Be biya ko'ina ba straight hall d'in yah nufa,kowa sae sauri yake yah shiga,kafin kace meh kowa yah shiga kafin yah iso dama ana ganin shi ake guje-gujen shiga.
Bayan yah shiga gaisuwa suka fara yi tareda tambayar yah hutu,bayan nan sae lecture yah fara.
Daedae lokacin Suhana ta iso wajen da saurinta.Tsayawa tayi ganin harya shiga,ga mamakin kowa saiya ceh "shigo mana!!"
*HAMAGEE*
garbahama69@gmail.com
💦 💦💦💦 💦
*LAIFIN WAYE??*
💦💦💦 💦💦💦
_Written by the Aplomb writer: *Hamagee*_
*This page goes to each and every amazing person in my group..you people made our day yesterday,tnks for the birthday wishes for those who cares to wish,others that didn't are thanked as well,we ain't offended at all,we loves you all with one heart* ❤
💦
*Difficulties In Your Life Don't Come To Destroy You, But To Help You Realize Your Hidden Potential..*
http://www.hamageenovelsseries.com/facebookpage
Page 15 💦💦
Ba ita ba kowama saeda yasha mamakin shi,"come in now!!",yah maimaita ganin ta tsaya kallon shi.
Cikeda takunta nah ishasshiyr mace meh qasaita ta shiga hall d'in as if ba alfarma akayi mata ta shiga ba.Shi kuwa bece mata komai ba saema juyawa da yyi yah soma rubutu a kan board kafinnan yah juyo ga y'an aji yana musu bayani.
Ido hud'u Suhana tayi da Abida,wani harara ta watsa mata kafin ta nemi seat ta zauna.
Ana cikin lecture saega wani d'an class d'inne shima yazo,da kaman malamin ba zai barshi yah shiga ba dan shikam ma harya fidda rai dan yasan ba shiga zaiyi ba.
Ganin yadda kowa yah tsura ma malaminnan ido yasa yace mishi yah shigo.
Dad'i yah kama mutumin nan,shiga yyi yana fad'in "thank you sir!",shiko lecturern bece komai ba saeya cigaba da koyarwan shi.
**************************
Bayan sun fito daga lecturen sae Suhana da wata qawarta meh suna Suwaiba kala suka nufa office d'in lecturern nan,Suwaiba kala budurwa ceh meh tashen ya'mmatanci,tana jida kanta matuqa,wannan dalilin yasa qawancen nasu yazo d'aya da Suhana.
Sallama sukayi yah answer sannan suka shiga kowaccen su naji da kanta."Gamu mallam kace mu sameka a office".Suby kala ceh tayi wannan maganar.
Suhana da ita yake kiranma bata ceh komai ba sae Suby dake ta zabga mishi rawar kai.
Yah dubeta sannan yace "no qawarki nayi kira bake ba,I don't have any case with you,ohk!".Nan take ran Suby yah b'aci saedae bbu yadda ta iya dan idan tayi qiris tana iya gani a result d'inta dan ba qaramin mara mutunci bane mutumin.
Yace "you can leave or wait outside for her!".Fita Suby tayi ta basu waje ranta a b'ace.
Yah juyo ga Suhana tareda fad'in "yanmata yah gajiya?",tace "ba gajiya",tajaa ta fuske,ita alla alla take yah sallameta ta tafi gida dan a gajiye take kuma tana son yin bacci kafin ta dawo na yamma.
Ta gashi da shirun nashi dan haka tace "mallam gida zani fah baka sanardani abunda kayi mun kira danshi ba!!".
Murmushi yyi kafin yace "sunanki nake son jin daga farko".Suhana ta galla mishi harara tareda fad'in "and for what reason? Yau mukayi resuming ballantana kace ka bamu test koh wani assignment maybe kana so kayi confirming sunana".
Yace "calm down ya'nmata I don't mean to hurt you kwae buqata nake da ita a gareki,kuma ina fatan Allah zaisa ki qarb'eta hannu biyubiyu".
Kan Suhana yah d'aure tace mishi "wace irin buqata kuma?".Yyi dariya kafin yace "ahh common!! Yah zakiyi pretending as if baki gane ba,kamarki a shekarunki da kuma level d'in karatunki kice baki san meh nake nufi ba".
Suhana tace "am sorry!! I have to leave right now".Tashi yyi tsaye yah nufa inda take tsaye tareda sanya fuakar rashin wasa a tareda shi.
Yace mata "sonki nakeyi,tun lokacin dana fara kallonki naji ina sonki kuma wllhi soneh nah gaskiya,ina fatan zaki karb'eni hannu biyu!".
Daskarewa Suhana tayi a wajen a ranta tana mamakin meh hali irinnashi yah dubi idon student yace yana soh,lallai abun yah kai maqura dan ita saboda sanin shi yasa tun farko bata kawo wannan tunanin a ranta ba.
Amma abun akwae mamaki dan bata tab'a jin ya nuna balle yace yana son wata student ba hasalima shi daban yake shiyasa yan'mata keh mugun kama kansu dan yana iya disgracing d'inki a cikin mutane.
Jin shirun Suhana yyi yawa yasa yace "koh sae kinyi tunani neh?",da sauri ta d'aga kai alamun eh,yace "it's good kiyi tunanin,dan gaggawa aikin shid'an neh,shikenan you can go saedae ina buqatar ki bani numbern wayarki dan inji feedback naki in kin gama tunanin!".
Da sauri kamar meh jin tsoro Suhana ta karb'a wayar hannunshi da yake miqa mata ta sanya mishi numbern nata sannan ta miqa mishi.
Yadda Suhana keh abu kamar ba itace Suhanan da kuka sani ba,yarinya meh aji da jida kanta,yarinya meh isa da mulki ga duk wanda taso.Yarinya mai wulaqanta duk wanda taso koda yah fita neh.Abun yah matuqar bani mamaki kuma nasan hakane a wajenku!!
Bayan fitar Suhana daga office d'in murmushi malamin yyi tareda duba wayar hannunshi,nan yyi saving numbern da *Beauty*..
***************************
A waje kuwa har Suby ta gaji da jiranta dan harta yanke shawarar tafiya abunta.Ganin fitowarta yasa ta dakata.
Suby taji mamakin ganin mood d'in Suhana yanda ta sauya gaba d'aya tayi wani iri kamar ba ita ba.Suby bata kawo maganar soyayya a tsakanin su ba saboda sanin koh shi wanene.
Ta mayar koh ya ci mata mutunci neh,tambayar Suhana tayi ita kuma tace mata bbu komai kwae ta gaji neh shiyasa.
Haka suka nufa motar Suhana suka shiga,bayan ta ajiye Suby a gida saeta wuce abunta.Hankalinta duk baya jikinta,jinta take kamar an sake yinta neh kamar ba ita bace.
Tana isa ta samu Mommy a palour tana kallon maimaicin *Joda Akbar* na jiya.
Da fara'a Mommy tace "you're warmly welcum my princess".Suhana tayi smiling tareda fad'in "tnks Mom".
Mommy ta lura da yanayin Suhana sarai amma saita share dan a tunaninta gajiya ceh dama haka ta saba dawowa tasan zuwa anjima zata ware.
D'aki Suhana ta wuce tareda cire mayafin jikinta ta ajiye shirgin data shigo dasu.Zubewa tayi akan lallausan gadon ta tareda rufe ido tana tuna al'amarin da yah auku yau.
A gaskiya she's lucky to have prof.Sadeeq Manu dan yah had'u iya had'uwa.Gashi yarone badae sosae ba amma kuma ba babba bane dan be wuce 34years ba.Irin masu gama karatu da wurinnan neh.
Ga ilimi agunshi,gashi kyakyawa ga iya wanka,ga aji dan dayawan ya'namatan campus d'innan nah bibiyarshi saedae basu samu fuska bane shiyasa.
Yana mugun jan girmanshi,Lecturen GNS d'insu neh shi,be cika dariya da kowa ba kuma baya b'ata rai,sannan bashi da zafi amma dukda haka maza da mata tsoronshi sukeyi,ga kud'i daidae gwargwado,ga gaa gaaa,yah dae had'u kawae..
Babban farin cikin Suhana shine inta amince dashi toh bbu qarya zatayi suna a cikin camp dan kowa saeya ji a jikinshi.Ita kuma babban abunda take so kenan tayi tarayya da wanda zae saya mata mutunci yah janyo mata girma kuma,duk a idon mutane.
Toh gashi Allah yah kawo mata a bati.Tace "I've to use this opportunity before it pass,ya zamo dolene na amince mishi,for the first time da zan fara accepting masoyi,how popular I'll be,huhh".
Wani irin dad'i da shauqi Suhana keh ji a yanzun nan.Kamar a sama taji wayarta nah ringing.
Tana dubawa kuma saita ga number bbu suna,jikinta yah fad'a mata cewa prof d'inta neh yyi kira dan haka ta daedaeta murya tareda saeta kanta kafin ta answer dan na farkon harya yanke sake kiran akeyi.
Daddad'an muryarshi da inta tuna yake sata farin ciki neh yace "assalamu alaikum!",cikeda jan aji da yanga irin nata ta answer da "wa'alaikum salam",cikin zaqin muryarta.
Yace "hope kin d'au muryar!!" tace "kamar dae hakan".Yace "toh you've to be sure,it's prof.Sadeeq Manu speaking",wani dad'i neh yah baibayeta,yanda yah kira sunan yyi mata dad'i sosae.
Tace "na gane!".Yace "dama soh nake naji koh kin isa gida lfya",tace "lfya klou,tnks"yace "no need to mention,kafin na barki ki huta ina soh inji sunan naki".
Saeda ta d'an jaa ajinta na fama kafin tace "sunana Suhana Omar Farouq".Yace "what a nice name!! Kice banyi kuskuren yin saving sunanki da beauty ba dan kin amshi sunan naki.Uhmm kar in cika ki da much noise na barki lafiya".
Tace "ohk",yace mata "bye"tace "bye" as well,hanging call d'in yyi.Tsurawa wayar ido Suhana tayi ta ma rasa yadda zata fassara irin farin cikin da take ciki yanzu.
Tayi kissing jikin screen d'in wayar kafinnan tayi saving numbern bayan ta gama tunanin sunan da zata sanya mishi.'CHOCOLATE' tayi saving sunan dan a rayuwarta bbu abunda take soh kamar shi.
Dan koh rai aka b'ata mata daka bata chocolate toh zata haqura,tana mugun soh.
Tashi tayi tayo alwala tayi sallahn azahar kafin ta koma kan gado tayi kwanciyarta,da qyar tunanin prof nata ya barta tayi bacci.
Around 3:05pm ta tashi a baccin nata,wanka ta shiga tayo sannan ta had'a da alwala.Palour ta fito inda ta nufa dining ta d'ebi abinci taci tasha ruwa sannan ta dawo ta kurkure bakinta saetayi sallahn la'asar sannan tayi shirin tafiya.
Kamar karta jeh take ji amma bata soh kuma tayi missing,bayan ta gama shirinta saeta jeh d'akin Mommy tayi mata sallama sannan ta fito.
D'akin Hadiza ta nufa tayi knocking,babi jimawa Hadiza ta taso ta bud'e,Suhana ta umarce ta da ta wanke mata toilet ta gyara d'akin kafin ta dawo.
Hadiza ta answer da "toh saekin dawo".Suhana tace "yauwa" sannn ta fita ta tafi.
Saeda ta biya ta d'auki Suby sannan suka wuce school d'in.Suby tayi ta shan cikinta koh zata jii abunda prof yah fad'a mata amma firr Suhana taqi sanar mata komai.A cewarta in yyi tsami kowa ma yaa jii.
Bayan sun gama ma haka tare suka dawo.Suhana dae kwata*2 ta sauya a d'an qanqanin lokaci wanda hakan yah damu Suby kala.
**************************
Mommy nah kwance tana jiran dawowan Suhana dan akwae maganar da take son yi da ita.Saedae kuma magrib yah kusa kuma bata dawo ba.
Hakan yasa ta bari sae zuwa dare kafin nan ta huta.Koda Suhana ta dawo gida lokacin ana shirin kiran sallah neh.
*HAMAGEE*
garbahama69@gmail.com
💦 💦💦💦 💦
*LAIFIN WAYE??*
💦💦💦 💦💦💦
_Written by the Aplomb writer: *Hamagee*_
*In devotion to Maman Saif*
💦
*One of the most important keys to Success is having the discipline to do what you know you should do, even when you dont feel like doing it...*
http://www.hamageenovelsseries.com/facebookpage
Page 16 💦💦
Bayan sallahr isha Mommy da Suhana na zaune suna cin tuwon dare,Suhana dae cii kwae takeyi amma hankalinta baya wajen koh kad'an.
Tunanin prof d'inta take tayi,Mommy tana kula da yanayin ta,taga duk ta sauya,kamar meh tunani while tasan Suhanan ta bata saka damuwar komai a ranta,bata ma da damuwar balle ta damu.
Toh ko meh ya faru yau d'in? Sae Allah.Bayan sun gama cin tuwon Suhana kanma bata wani ci ba ta tashi,Hadiza ceh tazo ta kwashe shirgin ta kai kitchen.
"Wae ni meya samu beauty neh yau d'innan?".Inji Mommy kenan.
Suhana tace "meh kka gani? Bbu komai".
Mommy tace "anya kuwa?"doubtedly.Suhana tace "Allah bbu komai".
Mommy dae tasan akwae wani abun amma saita share kwae,tace
"magana nake son muyi dake!".
Suhana tace"maganar meh kenan Mom?",Mommy tace
"magana akan Fahyim!"
Suhana ta juyo tana kallon Mommy kafin tace "toh meh same shi? Wae ni Mommy bazaki bar maganar mutuminnan bane?"
Mommy tace "eh toh! Abunda nah hango miki yasa nah kasa daina yi miki maganar shin dan a gaskiya Suhana zaki samu ingantacciyar rayuwa a tareda shi,yaron bashida hayaniya kuma yana matuqar sonki,Koh jiya saeda yah kirani yah gaishen,bayan mun gama wayar kuma Ammensu ta kirani take fad'a mun irin rashin sukunin da yake ciki na qin amincewa da kikayi dashi.Why Suhana? Why can't you understand,why can't you figure anything good in him?".
Suhana ta rasa miye damuwar Mommy akan shi.Tace "well! Kina sonshi while bana sonshi,which one is more important here,my love or yours?,I see no reason da zaisa kiyi ta insisting kan maganar nan Mom coz ni zan zauna dashi kuma nace banayi,why can"t you understand the situation?".
Mommy tace "you're right,but a mother always ensures her child's happiness in any case and she can't bear to see his weakness no matter what and how.And yes she always tries to make his dream comes true!!".
Kaman Suhana zatayi kuka tace "Mooommm!!!!,dan Allah ki bar maganar nan haka,it's the matter of me loving him and I ain't interested in him so why can't you let it be".
Mommy tace "toh shikenan,amma dae kiyi tunani a kai".
Suhana bata qara cewa komai ba,ranta ma b'aci yyi,wae akan wani banza Mommy take neman takura ma rayuwarta.
Tashi tayi tah koma d'akinta inda ta d'au wayarta da niyyar yin chatting sae taga 2missed calls.
Koh da ta duba saetaga 'Chocolate' neh yyi kiran.Kamar zata kira shi sae kuma d'agun class d'inta yah tashi.
D'auka tayi tazo ta zauna ta kunna data,ta kunna kenan sae wayar ta fara ringing.
Chocolate neh keh kira saboda haka saeda ta gama jan ajinta kafin tayi picking,
"waalaikas salam"ta answer,yace
"yah kke?"tace"lfya lou"yace "na kira ki bakiyi picking call d'inba,kin sa inata damuwa",Suhana tayi dariya kafin tace "am sorry wllh muna magana da Mom neh a palour".
Yace "ohk ba matsala,amma da saikiyi calling back tunda kin gani koh".
Suhana tace "eh! Yanzu na gani nima",yace "toh ba komai,yah Mom d'in?"
Tace "lafiyarta lou",yace "toh Alhamdulillah,yanzu ina so inji matsayin da kka bani a zuciyarki neh,answer nake son ki bani,am I accepted or not".
Wani fad'uwa gabanta yyi,tama rasa ta cewa dan a gaskiya tana sonshi dan so amma she can't just tell him.
Ta qirqiro murmushin qarya kafin tace "ae ban gama shawarar ba,ba yau mukayi magana ba?".
Yace "hakane! Amma ai kin san ance love at first sight is the most true love,and it's always the best".
Tace "hakane! But saenayi tunani,zaka ji feedback inna gama tunanin".
Yace "toh bbu matsala,Allah yasa inji alkhairi",tace "ameen".Haka sukayita hirarsu daga bisani yyi hanging.
***************************
*WEEKS LATER....*
Yau ta kama ranar Saturday kuma yyi daedae da ranarda Daddy zai dawo daga Uganda.
Shirye-shirye suke tayi kamar masu tarban governor,sae dare yah isa gidan.Kowa murnar dawowar shi yake.
A ranan gidan yah koma complete,kowannen su daa yana ganin kamar ranan bazata zo ba,sae gashi Allah yah kawo mu ranan sae san barka.
Washegari,
Da safe bayan sallahn asuba,Mommy nah d'akin daddy suna kwance yake tambayarta.
"Nikam yah maganar yaran nan neh?",Mommy ta juyo tana facing nashi tace "suwa kenan?".
Daddy yace "Suhana da yaron qawarki baa"."Hmm ka bari kwae,abu yaqi yyi dad'i wllh,na rasa yadda zan fahimtar da Suhana kan wannan maganar".Inji Mom
Daddy yace "lallae kuwa,yanzu har yanzun basu daedaeta ba? Meyasa Suhana bata fahimtar mu neh?".
Mommy tace "sae Allah! Nikam ma na rasa ta yadda zan b'ullo mata ma wllhi".Daddy yace "what will happen shine indae kinada full interest akan yaron kuma kin tabbatar bashida wata matsala saeki fad'a mun yanzu".
Mommy tace "wallahi i'm fully interested in him,and he's also financially good.With him,our Suhana will be happy forever I assure you this".
Yace "great!! Then yau d'innan inaso ingana da mahaifanshi,ki kira haj.Aishan ki sanar mata cewa ina son ganawa da baban yaron".
Mommy tajii dad'i qwarai tace "insha Allahu,anjima kad'an in gari yah d'anyi haske ma zan kirata sae na shaida matan".
Daddy yace "Allah yah kaimu!",tace "ameen".
Bayan gari yah gama wayewa around 8:30am Mommy ta kira wayar Ammee dan sanarda ita maganarsu ta d'azu da Daddy.
Ringing d'aya ana biyu tayi answering tareda yin sallamarta "assalamu alaikum!",Mommy ta answer da "ameen,waalaikumus salam,haj. an tashi lafiya?".
Ammee tace "lafiya qlou,yah gidan naki?",tace "lafiya lou,yah naki iyalan?",Ammee tace "kowa lafiyan shi klou".
Mommy tace "toh madallah,dama akan maganar yaran nan neh na kiraki sassafen nan",dariya Ammee tayi tace "wae sassafe,Allah yasa dae alkhairi neh".
Mommy tace "eh mana,daman baban yarinyar nan neh yace nayi miki magana yanason suyi magana da me gidan naki kan batun yaran dan duk abunda ake yinnan yanada labarinshi,so jiya yah dawo kuma daga tafiyar dana ceh miki yyi".
Ammee tace "Allah sarki!! Yah dawo lafiya ae?",Mommy tace "lafiya lou wallahi".
Ammee tace "toh Alhamdulillah,kuma insha Allahu zan sanarda shi".Mommy tace "yauwa, nagode".Ammee tace "nice da godiya ae".
Mommy tace "yah masifaffiyar y'ata?",tana dariya,Ammee ma dariyar takeyi tace "Abida baa,iyayen f'ada,lafiyarta qlou".
"Toh a gaida mun ita! Kuma yaushe zaku zo?"injii Mommy kenan.Ammee tace "zatajii insha Allahu! Eh toh inna saka rana zan sanarda keh!".
Mommy tace "Allah yah kaimu toh",Ammee tace "ameen".Saeda suka gama shan hirarsu tukunna Mommy tayi hanging call d'in.
Suhana na cikin baccinta meh dad'i wayarta ta soma ringing,ita ta tasheta ma,saedae ganin chocolate keh kira yasa ta maida masifar da tayi niyyar zubawa.
Dan yanzu ya zamo d'anlelenta,autan maza.Bayan tayi answering saeta ceh "hi" cikin muryar bacci.
Yace "am so sorry my beauty! Na tasheki a bacci".Suhana tace "it's ohk tunda kai ka tashen ba komai,amma daa harna shirya bala'in da zanyi".
Dariya Sadeeq yyi sosae kafin yace "wllh kin fiye fad'a,kuma ba'a san kyawawa da fad'a ba,kema ki daina".Tace "zanyi qoqari tunda kace".
Yace "yauwa".Suhana tace "daddy dae yah dawo jiya!",Sadeeq yace "really!",tace "sure!".
Yace "am happy wallahi! Kinga yanzu sai nazo gida a sanni koh",Suhana ta wani canza face tareda fad'in "so soon?",Sadeeq yace "ehen,baki so nazo gidanku?".
Suhana tace "nidae ba yanzu ba,ka bari sae mun dad'a sabawa tukunna".Wani farin ciki Sadeeq yaji dama yah fad'i hakan neh saboda taga kamar cewa da gaske yakeyi.
A fili kuma yace "yace hakane,Allah yah cika mana burinmu",tace "ameen".
Bayan sun gama hiran sae yyi hanging up,tashi Suhana tayi ta shiga toilet inda tayi brush sannan ta fito ta nufi palour dan tun suna waya taji anyi mata knocking qofa,kuma tasan breakfast neh yyi shiyasa.
Tana fita a palour ta samu su Mom,ta gaidasu sannan ta zauna ta fara breakfast,cikin kwanciyar hankali suke abunsu har suka gama.
Bayan sun gama suna zaune a palour Daddy yah d'auko jewelries da yah saya musu yah kawo,kowa ta d'au nata,sunyi murna sosae.
Harda wasu kaya yah kawo musu,harda nah Hadiza da anty talatu wannan kan,suma da aka basu sunyi murna tareda godiya.
*HAMAGEE*
Hamagee: garbahama69@gmail.com
💦 💦💦💦 💦
*LAIFIN WAYE??*
💦💦💦 💦💦💦
_Written by the Aplomb writer: *Hamagee*_
*In devotion to Maman Saif*
💦
*If Yesterday Did Not End Up The Way You Wanted, Just Remember God Created Today For You To Start A New. God Gives The Best To Those Who Leave The Choice To Him....*
http://www.hamageenovelsseries.com/facebookpage
Page 17 💦💦
Abbaa nah zaune a palourn shi yana kallon *Channels tv* kasancewar yau Lahadi bbu aiki.Ammee tayi sallama yah answer sannan tazo ta zauna a gefen shi.
Ta dubeshi tace "d'azu munyi waya da haj.Fati take ce mun wae meh gidan nata yah dawo har sunyi maganar yaran kuma yace yana so ku had'u".
Abba yah gyara zama tareda cewa "toh Alhamdulillah,yau kenan?".Ammee "da son samu ba",yace "toh ba komai saemu je anjima dake".
Ammee tace "toh shikenan",a take ta kira Mommy ta sanarda ita zasu zo,Mommy taji dad'i sosae,ta fad'a ma Daddy ma yace Allah yah kaimu.
Shirye-shirye aka koma yi,Suhana dai bata san meh ake ciki ba,kuma bata damuda tayi tambaya akai ba dan bata shiga hidimar da ba'a saka ta ba daman.
Around 11:00am suka iso gidan,tarba Mommy tayi musu sosae kafin taje ta kira Daddy ma yazo palourn,nan fa *kallo yah koma sama*.
Daddy yace "iyy,Alh. Sadeeq neh!".Abbaa yah miqe tsaye yana fad'in "Alhj.Omar! Dama gidan daka dawo kenan? Kace Suhana y'ar tamu ceh!"yah qarasa yana bashi hannu.
Musabaha sukayi tareda neman guri suka zauna,su dae Mommy da Ammee kallon su kawae suka tsaya yi cikeda al'ajabi dan basu tab'a sanin mazajen nasu sun san juna ba.
Daddy yace "ae ban san d'anka bane yaron da tuni nace an bashi",dariya suka kwashe da ita.Su mommy da Ammee sunsan mazajen saedae ba su san mazajen nasu bane.
Mommy bata san mijin Ammee ba kenan,tama Ammeen bata san mijin Mommy ba kenan,Abba neh yah juyo yah kalli Ammee yace mata "shine abokin nawa da nake fad'a miki ranan".
Ammee tace "ayyrh ae na gane shi ma,kaga bakuyi disappointing juna ba kenan!".
Abba yace "wallahi kuwa,bamu san already yaran sunga juna bama,shiyasa nayi mishi wancen bayanin".
Daddy yace "kaga zamuyi abun da kyakkyawan niyya kenan,tunda abunda muka zab'an ma yaran namu shi yake shirin faruwa".
Dukkansu sukayi hamdala,Mommy ta tashi tace zata kira Suhana ta gaishe su.
Tana kwance tayi shame-shame a kan gadonta lokacinda Mommy tayi knocking,bata iya tashi koh magana ba dan baccinda keh idonta.
Ganin Suhana tana bacci yasa Mommy bud'e qofar d'akin tayi shigewarta.Tashin Suhana ta shiga yi,koda Suhana ta tashi saeta ceh "haba Mommyyyy!!,meh zan miki haka neh? Ina baccina meh dad'in nan zaki zo ki d'aga nih,gaskiya bana soh nikam"ta wani yi miqa tareda yin hamma irinta malalatan nan.
Mommy dae ido ta zuba mata kafin tace "am sorry toh,yanzu ki tashi kije ki gaida baqi a palour".
Kamar an mitsine ta tace "wasu irin baqi Mommy da safennan?",Mommy tace "idan kinje kya gansu,yanzu tashi ki wanke fuskarki saeki sa kaya sannan kije ku gaisa".
Mommy nah kaiwa nan ta miqe tayi hanyar fita dan sarai tasan halin Suhana,yanzu inba hakan tayi ba toh saeta bi wata hanyar kuma.
Kafin ta fita ta juyo tace mata "ki fito yanzun nan fa",tana kaiwa nan bata jira taji answern ta ba tayi ficewarta daga d'akin.
Palourn ta koma inda suka cigaba da tattaunawan su.
Suhana kuwa tashi tayi tanata faman ququni wae Mommy na son takura mata da yawa,ita bacci take jii kuma.
Bayan ta fito daga toilet d'in saeta sa kaya,riga da skirt ta atamfa saeta d'an yafa gyalenta colourn da yyi matching da kayan ta yafa sannan ta fito.
Da sallamarta ta shiga bayan sun answer.Ammee ta fara kallo wanda ganin nata yah fad'ar mata gaba,da qyar ta iya qarasawa wajen ta gaisheta.
Bayan sun gaisa saita je ta gaida Abbaa dake ta faman yin murmushi nah jin dad'in,a ranta tace 'dama ka daina wage bakin nan naka neh dan kuwa d'anka bazae tab'a samun karb'uwa a wajena ba!'.
Bayan sun gama gaisawar saeta miqe ta bar palourn inda ta koma d'akinta ta cire kaya,wanka ta shiga tayo tazo tana tsara kwalliya kamar meh zuwa biki.
Bayan fitar Suhana daga palourn sae Abba yah dubi Ammee yace "gaskiya yarinyar nan tabarkalla,ashe kykkyawa ceh ta qarshe shiyasa d'ana duk yabi yah birkice akan ta".
Dukkansu saeda sukayi dariya kafin Ammee tace "ae ni banma tab'a ganin meh kyaunta ba,gaskiya saedae kwae muyi fatan Allah yah daedaeta tsakaninsu,dan shine babban abu yanzu".
Abbaa yace "ameen,shine kam",Mommy da keta godema Allah da yasa har Suhana ta shigo ta fice batayi wani abun ba tace "insha Allahu it will come to an end soon!".
Duk sukace "ameen",bayan sunsha hirarsu sae su Abbaa da Ammee suka tafi.
***************************
Bayan ta gama kwalliyarta saita sanya kaya,less neh red colour saeda toch d'in yellow a jiki,kayan sun matuqar yi mata kyau.
Ta d'au gyale yellow meh adon red a ajiki,haka takalmin qafarta da hand back,ta mugun yin kyau.
Ta canza case na wayarta zuwa yellow d'in case.Dama kala-kala take dasu.Bayan ta gama shirinta tsaf sae wayarta tayi qara kamar an san cewa she's ready.
Chocolate keh kiranta dan haka without any hesitation tayi answering.
"My one na iso pha" Inji prof.Sadeeq kenan, Suhana tace "I'll be right there then!"tayi hanging tareda d'auko wani designer turarenta ta fesa ta ko'ina a jikinta.
Suhana kenan,ga kyau ga qanshi,koda wanne prof zeji?? Lolxx..
Saeda ta duba kanta a mirror ta tabbatar da komai yyi kafin nan ta fito.D'akin Mommy ta nufa inda tace mata zata fita.
Mommy ta qarema Suhana kallo kafin tace "irin wannan kyau beauty!! Sae ina kuma?".
Suhana tayi murmushi wanda yake qara fidda kyaunta waje tace "Mommy kenan! Zani bikin wata friend d'ina neh,yau wuni kuma,I think acan zan wuni ma".
Mommy tace "toh,ayi dai a hankali wannan kyaun kar kisa maza gwaruwa a kan hanya".
Dariya Suhana tayi tana fad'in "bye Mom",dan tasan halinta yanzu sae tayi ta wasting mata time tana zugata.
Tana fita Mommy tayi smiling tana fad'in "tabarkalla".
Suhana kuwa tana fita ta nufa d'akin Daddynta,inda ta same shi kwance a kan gado,ta shiga tana fad'in "dad na fita!".
Daddy yace "toh daughter,saekin dawo,ga wannan koh zaki buqata"kud'i yah miqa mata wanda shima kanshi besan adadinsu ba.
Ta karb'a tareda yin godiya.Tafiya tayi bayan ta mishi sallama...
*HAMAGEE*
[7:27pm, 3/30/2017] Hamagee: [10:14pm, 3/27/2017] Hamagee: Hamagee: garbahama69@gmail.com
💦 💦💦💦 💦
*LAIFIN WAYE??*
💦💦💦 💦💦💦
_Written by the Aplomb writer: *Hamagee*_
*In devotion to Maman Saif*
💦
*Sometimes you think you've gotten over a person, but when you see him smile you suddenly realize you're just pretending you're over him to ease the pain of knowing that he will never be yours....*
http://www.hamageenovelsseries.com/facebookpage
Page 18 💦💦
Yana zaune a motarshi yana jiran fitowarta,zuciyarshi fari tas abunshi.A tunanin shi koh ta tsaya yin qaryar inda zata jeh neh dan yaji shirun yyi yawa.
Besan cewa ita d'in ta daban ceh ba,tana iya fita a duk lokacinda taga dama kuma taje duk inda take so batareda ta sanarda kowa bama.
Dan sau tari in zata fita ma bata fad'a ma kowa saedae in maman ta shiga d'akin saeta ga bata nan kuma inta dawo ma saeta shige d'akinta ba tareda wani yasan dawowarta ba.
Kuma su hakan basu d'auke shi as wani abun ba. A ganinsu ba laifi bane yin hakan.
Suhana ceh ta bud'e qaramar qofar dake jikin gate d'in sannan tasako kai ta fito.
Ranta fari tass,tana d'okin ganin chocolate d'inta,dama tayi missing nashi gashi yau zasuyi spending much time tare.
Kafin ta qarasa yah fito da rawar jiki yah bud'e mata motar tana qarasowa ta shige dan akwae rana lokacin,wani shu'umin kallo yah bita dashi ita koh dad'i takeji a dole ta samu meh nuna mata tsantsan soyayya da kulawa.
Bayan ta shiga saeya zaga yah shiga side d'inshi.Wani irin kallo yake ta binta dashi kamar mayunwacin zaki yaga nama.
Tace "yah dae? Irin wannan kallon!",Sadeeq yace "baki ga yadda kkayi kyau bane!",mirmushu kawae tayi batace mishi komai ba.
Yace "shall we??",tace "sure!!",tada motar yyi sannan yajaa suka tafi..
Haka suka shaa yawonsu mara galihu sae can yamma yah dawo da ita gida.
***************************
Washegari a makarantarsu Suhana wasu y'anma na zaune suna ta zancen ta da prof.Sadeeq dan yanzu har maganar ta fara bazuwa.
Dama burin Suhana kenan tayi suna a makarantar,bama makaranta kad'ae ba a ko'ina,inda ko'ina tazo wucewa za'a ringa nunata ana cewa wancen fa wance ceh.
Toh yanzu abun nema yah samu,dan a d'an kwanakin nan kusan rabin y'an makarantar sun san zancen,Suby kala ma yanzu ta sanda zancen,Suhana ta dad'a qaurin suna a school.
Hakan ba qaramin dad'i yake mata ba.Tana isowa ta parker motarta tareda sanya space a idonta kafin ta bud'e qofar motar ta sanyo qafarta d'aya waje.
Ta d'an bata lokaci tana kallon wayarta qirar iphone 7 kafin ta d'au jakarta ta fito,kowa yah kalli Suhana yasan y'ar hutu ceh,dan kyaun nata harda hutu a cikinshi.
Zuwa tayi ta wuce ta gaban y'an matan nan tana takunta cikin isah da taqama kamar yadda takeyi,saedae ta yanzu tafi ta daa.
Office d'in prof.Sadeeq tah wuce kai tsaye bbu jin d'ari,tana shiga kuwa ta sameshi zaune yana jiranta,wani murmushi yah sakar mata itama ta maida mishi martani.
Yah tashi tsaye yana fad'in "have a seat my queen",neman guri tayi ta zauna kafin shima yah zauna,gaisawa sukayi cikeda so da nuna kulawa abunsu.
Wani irin on top Suhana keh jin kanta.
Students nah d'azunnan neh gulma be ishesu ba dan haka suka yanke shawarar zuwa office d'in sugane ma idonsu komai,dan d'aya daga cikinsu musu takeyi akan badae soyayya sukeyi ba.
Sukace mata soyayya neh mata,tace ita bata yarda ba.
Tashi sukayi suka nufa offishin da niyyar submitting assignment d'inda yah basu.
While yace zai qarb'a karb'a a class.Suna isowa meh qarfin halin cikinsu neh tayi knocking.Daedae lokacin Sadeeq yah taso yah nufo inda Suhana keh zaune,koh meh zaiyi mata?? Ohoo!!
Ranshi neh yah b'aci jin ana knocking qofar,bbu yadda yah iya saeya koma seat nashi yah zauna,bayan yah zauna saeya ceh "come in!",ba don ranshi yaso ba.
Su uku haka suka shigo office d'in kowaccensu riqeda papers a hannunta,gaishe shi sukayi yah answer.
Bayan nan yake tambayar su meh ya kawo su? Sukace sunzo submitting assignment neh.
Suhana da tun shigowarsu idonta yake kan wayarta ta d'ago ta qare musu kallo,ta ganesu dan d'azu ta wuce su a hanyar zuwa office d'in,saedae bata ceh qala ba ta mayarda kanta inda yake ta cigaba da abunda takeyi.
Sadeeq yace "amma dae nace muku a class zan karb'a koh!!".Kallon junansu sukeyi bayan sun qarema Suhana kallo,lallae inda bbu soyayya a tsakaninsu da bata isa ta sake dashi harta zauna haka ba.
Sukace "we're sorry sir,mun manta neh",shiru yyi musu,da kansu suka wuce suka bar office d'in ba tareda yah ceh su barin ba.
Suhana taceh "magulmata kwae,qarya suke ni suka zo gani sukayi qaryar kawo assignment dan na had'u dasu on my way here".
Sadeeq yace "lallae yarannan! Yanzu muje class toh time d'in fara lecture yyi".
Suhana tace "ka jira tukun,akwae wata qawata da bata zo ba,mu jira tazo sae muje koh!"yace "toh bbu komai".
Wayarta ta duba inda ta shiga neman layin Suby kala,tana zuwa kai tayi dailing.
Ringing nah farko ta d'aga,tana fad'in "hello,Suhana an shiga koh?",Suhana tayi murmushi da muryarta meh sanyi tace "aa,keh ake jira,kiyi sauri kizo kafin a fara".
Suby tace "kina sha'aninki,yanzu har nima sae an jirani! Toh gani nan kan hanya Habeeb neh yah tsaya b'ata mun lokaci wllh amma yanzu mun rabu ni ina hanyar zuwa".
Habeeb d'in saurayinta neh kullum suna tare kuma basuda maraba da ma'aurata dan duk sanda yake da buqatarta yana samu,yanzun ma kamar koda yaushe,cewa yyi yana needing nata shine yaje har gidansu yah d'auketa.
Suka wuce wani gidan abokin shi sukayi fasiqancinsu tukunna ta fito zatayi makaranta dan bata soh ana ganinta dashi.Dan Habeeb yyi qaurin suna wajen iskanci,kusan kowa yah sanshi.
Bayan Suhana tayi hanging call d'in suka cigaba da tad'insu.Can wayarta tayi ringing ta d'aga.
"kin iso neh?",Suby tace "eh kina ina neh?".Suhana tace "ina tareda my chocolate kije class kawae gamu nan zuwa".
Suby tace "ah lallae abun nayineh,toh sae kun shigo!",tace "yauwa"sannan tayi hanging call d'in.
Juyowa tayi ta gefe dan tanan yake facing nata tace "muje toh",wani munafikin kallo yyi mata tareda kashe mata ido d'aya.
Yace "muje",tashi yyi yah qaraso inda take yasa mata hannu ya riqota ta waist,wani iri taji saedae ta kasa ce mishi komai.
Haka suka fito yah rufe office d'in,saeda suka bar corridorn kusada office d'in kafinnan yah saketa dan akwae mutane a wajen.
Kowa kallonsu yah tsaya yanayi har suka nufa lecture room d'in,tunda yah fara lecturen Suhana bata fahimtar komai.
Daga qrshe ma maida kanta tayi kan desk a haka har bacci yyi gaba da ita.
*HAMAGEE*
[10:15pm, 3/27/2017] Hamagee: Hamagee: garbahama69@gmail.com
💦 💦💦💦 💦
*LAIFIN WAYE??*
💦💦💦 💦💦💦
_Written by the Aplomb writer: *Hamagee*_
*In devotion to Maman Saif*
💦
*No one is going to hand me success. I must go out and get it myself. Thats why Im here. To dominate. To conquer. Both the world, and myself....*
http://www.hamageenovelsseries.com/facebookpage
Page 19 💦💦
Har aka gama lecturen nan Suhana bata d'ago kanta ba even ones,bayan an gama sae kowa yah watse yah rage ita da Suby neh kad'ae.
Tasowa Suby tayi tazo inda Suhana keh kwance ta soma tashinta,"toh kaasa sarkin bacci,saeki samu daman tashi ae tunda yanzu kam an gama lecturen".
D'agowa Suhana tayi fuskarta da hannunta duk irin zanen baccin nan,ta danjaa guntun tsaki kafin tace "har an gama?".
Suby tayi dariya tace "gashi kina gani kuwa,yanzu dae tashi zakiyi nah kaiki offishin mallam Sadeeq dan yace dani na kai ki can".
Suhana tace "saeka ceh wata qaramar yarinya wae zaki kaini?",Suby tayi dariya tace "eh mana,keh dae dan Allah in kuna tare ki ringa yi mishi duk abunda yake so,kinga samun shi ba abune meh sauqi ba! Toh wallahi kada ki sake yah kub'uce miki".
Suhana ta dubeta confusely tace "name kenan,miye zanna mishi da zae qara mishi sonah?".
Suby tace "keh dad'ina dake baki fahimtar magana,gaki wayayya a haka amma bbu,kin gannin nan?"ta fad'a tana mata nuni da kanta.
Suhana dae d'aga kai kwae tayi lamun tana saurarenta,Suby ta cigaba "toh wallah I do everything to keep my man".
"Shawara d'aya zan baki nah kada ki bari sex yah shiga tsakaninki dashi tunda aure kuke sonyi amma wallahi ki sakar mishi jiki ku farantawa juna rai".
Suhana tace "amma baki ganin yin hakan zai iya janyo wata matsalar?".
Suby tace "ba wata matsala kinjii!!!! Kwae ki saki ranki bebe kisan meh duniya keh ciki yanzu".
Suhana tace "bakida kyau Suby,wallahi kuwa koda yaushe in muna tareda shi yakan nuna mun irin hakan,nidae kawae bana so wani abu haka yah shiga tsakanin mu dan ni yadda nake considering shine making romance zai iya janyowa ayi having sex kuma ni bana son rasa virginity nah for a boyfriend shiyasa kka ga banida shirgin samari".
Suby tace "ki saki ranki dalla,toh koda kunyi sex d'inma menene? Bashi zaki aura ba,toh bari kiji wallahi bbu abunda bama yi da da Habeeb d'ina dan yana sona ina sonshi kuma auren mu zamuyi soon insha Allah,yanzu haka an kusa kai kayan lefena".
Suhana tace "kuna sha'aninku Suby,nima zanyi qoqari in faranta ma choco nah rai @ any means kuwa".
Suby tace "yauwa y'ar gari!! Koh kefa! Kinga yanzu saboda keh nima yana d'aga mun qafa,mutumin da koh dariyarshi ba'a gani",suka tafe sannan suka tashi suka nufa office d'inna shi.
Koda suka isa Suby kala bata shiga ba sae kwae tace ma Suhana sae sunyi waya sannan ta wuce tayi tafiyarta.
Suhana kuma ta bud'e qofar ta shiga inda ta sameshi zaune a kujerarshi kamar yadda yake zama kullum.
Sallama tayi mishi yah answer sannan ta qarasa taje ta nemi kujera ta zauna tana facing nashi.
Sadeeq yace mata "sarkin bacci"cikin zolaya,tayi dariya kafin tace "kowa ma ai yana son baccin".
Yace "amma naki daban neh,duk lokacinda nah kiraki imma kin tashi kenan koh kuma zakiyi bacci".
Dariya kawae tayi batace komai ba.Yace "toh yanzu sae ina?",tace "kai zan tambaya ai".
Yace "toh ni koh nakeda wajenda zuwa,tashi mu fita!",tace "ohk".Nan suka kwashi shirgin kansu suka bar office d'in,saeda suka tsaya wani d'an shop suka sha ice-cream kafin nan suka wuce.
Wani gida yah kaita inda shi dae baza a kirashi gidan ba saboda mutanen dake ciki,kowa yana harqan gaban shine.
Wasu na shiga wasu kuma nah fita.In short qaramin hotel neh wajen,a mota yah barta yaje yah gama payment d'in komai kafin ya dawo yyi mata magana suka shiga.
Wani d'aki yah kaita inda yah shiga toilet yah fito.(Waiyazubillah,yau aji da jin kai yah qarema Suhana tunda take neman yada mutuncin ta),Muje zuwa...
**************************
Bayan yah fito daga toilet d'in wajenda take zaune yazo shima yah zauna.
Yace "kinga na kawoki nan koh! Wllh bana son hayaniyar mutane neh".
Tace "ba komai",jin ta fad'i hakan yah qara mishi qarfin gwiwa.Matsowa yah kuma yi dap da ita dan har numfashin juna suke ji.
Idonshi cikin nata yah d'aura hannun shi kan nata yana wasa dashi sannan yace "your hands are so soft my love!".
Qoqarin kawarda tsoron da take ji tayi saeta mishi murmushi dan ta tuno da maganar da Suby tayi mata d'azu na tayi mishi duk abunda yake so.
Kwanto da kanta tayi jikin shi tareda lumshe ido kamar meh jin bacci.
Dad'i neh yah kamashi a take yah kwantarda ita a kan gadon,romansing nata yah shiga yi ita kuma tana jin dad'in hakan shiyasa koh kad'an batayi attempting hanashi ba saema qara shigewa jikinshi da takeyi.
Sun jima suna sheqe ayarsu kafin yah rabuda ita ba don yaso ba saedan taqi amincewa yayi sex da ita.
Saedae yah d'auma kanshi alqawarin lalata da ita kota wane hali matuqar tana tareda shi.
Bayan sun shirya around 4:30pm yah maidata gida,a hotel d'in sukayi sallolin su sukaci abinci kuma.
Bayan yah kawota har qofar gidansu saeda suka d'au lokaci suna kissing juna kafin yah qyaleta ta shiga gida.
Bayan ta shiga saiya jaa motarshi yyi gaba ranshi farii tass dan daga dukkan alamu dae ta fara falling mishi kuma burinshi nah dab da cikawa.
Suhana nah shiga gidan tayi d'akin Daddy dan ta jiyo muryarsu daga palourn.
Sallama tayi sukayi answer kafin ta shiga.Mommy ceh tace "welcum back my princess".
Suhana tayi smiling tareda fad'in "tanks my Mom",daddy kuma yace "yah school d'in? Hope bbu wani problem!".
Suhana tace "bbu komai Dad,barinje in huta".Sukace "toh"sannan ta fita ta nufa d'akinta inda ta sameshi a gyare sae kanshi dake tashi.
Cire kayanta tayi ta shiga toilet yin wanka,tuno abunda yah faru yau tsakaninsu da Sadeeq da soma yi.
She just can't believe it,Sadeeq is soo sweet how she wish zata iya mallaka mishi kanta baki d'aya.
Saedae tana tsoron irin halin samarin yanzu karta yadda kuma yazo yah qi aurenta.
Amma she believe him,tasan bazae tab'a barinta ba because yana matuqar sonta.
Wasu irin imaginations tai tayi ita kad'anta,da qyar ta gama wankan ta fito,tana fitowa batan tayi draining ruwan jikinta saeta kwanta haka da towel a jikinta.
Bata jima ba bacci yah d'auketa.
*HAMAGEE*
[10:15pm, 3/27/2017] Hamagee: Hamagee: garbahama69@gmail.com
💦 💦💦💦 💦
*LAIFIN WAYE??*
💦💦💦 💦💦💦
_Written by the Aplomb writer: *Hamagee*_
*In devotion to Maman Saif*
💦
*Life is short, live it. Love is rare, grab it. Anger is bad, dump it. Fear is awful, face it. Memories are sweet, cherish it.....*
http://www.hamageenovelsseries.com/facebookpage
*You can now follow me on wattpad @Hama_gee*
Page 20 💦💦
Bayan sallahn isha'i around 8:15pm wayar Suhana tayi ringing,da kamar bazata d'auka ba dan number ceh bbu suna.
Sae kuma kawae ta d'aga dae,muryar Fahyim ta jiyo yana fad'in "ki fito dan Allah yanzu ina gidanku".
Be jira yaji answernta ba yah katse wayar,tashi Suhana tayi ta sanya kaya dan zuwa suyi duk wacce zasuyi dashi dan taga abun nashi yah wuce gona da iri yanzu.
Tana fita ta sameshi jingine a jikin Corolla_S d'inshi yana latsa waya,gashi dae d'an saurayi bbu laifi kuma yanada kyau,amma ita ba tsarin ta bane sh.
Gani take inta amince mishi ta qasqantar da kanta,dan mace meh kyau irinta kamata yyi ace ta auri wanda mutane zasu shaida cewa tayi aure,wanda duk inda ta wuce an san da zamansu.
Da wannan tunanin ta qarasa wajenshi.Babu koh sallama ta fara zazzaga mishi rashin mutunci.
"wae kai maye neh kam? Nace maka bana yi,banayi ka rabuda ni mana,koh so kkeyi sae nayi maka wulaqancin da harka mutu bazaka manta dani bane?".
Fahyim shiru yyi tunda ta fara maganar be mayar mata ba saida ta gama tukun yace "assalamu alaikum!!".
Wani qarin haushin sa Suhana taji,wato ma yah raina mata hankali kenan?
Tace "banyi sallamar ba,kuma ban answer ba saboda you didn't deserve any from me!".
Yace "toh yyi kyau,amma ina so ki koyi maintaining tempern ki dan rashin yin hakan zae iya saka ki yin dana sani wata rana".
Bata ceh komai ba ta juya zata tafi,sae kuma ta juyoo tace mishi "am not interested in your preachings so kaga tafiya ta".
Dariya Fahyim yyi kafin yace "good,kinga na fara samun karb'uwa a wajenki tunda har kin juya zaki tafi,sai kika ga be dace ki tafi ki bar masoyinki tsaye a nan ba,shine kka juyo kkayi mun bayani,nagode da wannan".
Yah qarasa fad'i yana d'aga mata gira.Ita kuma haushi yah sake bata dan haka barin wajen tayi ba tareda tace komai ba.
Saeda Fahyim yaga ta shiga har gida kafin nan yah koma cikin motarshi me gadi yah bud'e gate yah fita.
*********************
Koda Suhana ta koma cikin gida straight d'akinta ta nufa.Ta sauya kayanta zuwa na bacci,bayan nan saeta kashe wutan d'akin ta hau gado.
Wayarta ta d'auka tana latsawa,call log nata ta shiga tana gani,saeta samu kanta da yin saving numbern Fahyim,ita kanta bata san dalilin yin hakan ba.
Ita dae kawae tayi saving neh,bayannan saeta kunna data ta hau whatsapp nata tana bin messages.Gaba d'aya bata jin dad'in chatting d'in,contact list nata ta shiga inda taga numbern Fahyim tayi appearing.
Profile pic nashi ta duba inda ta ga hoton shine da Ammensu akai,murmshi tayi tareda duba status nashi.
Ganin status d'in blank yasa ta fita a wajen ta shiga contact d'inshi,kamar zatayi mishi magana ta bashi haquri kan abunda yah faru sae kuma tayi saurin dan harta fara typing assalam.
A ranta ta fara tunanin wae meke damunta neh, duk tabi ta sauya,"poor me!!",ta fad'a a fili.
Sauqa tayi ta ajiye wayar a gefenta tana tunani,da haka har bacci yah d'auketa.Can around 9:50pm Chocolate yah kirata,ko kad'an Suhana bata ji ba dan wayar a silent take,saeda yah gaji da kira sannan yah share.
Shi dae a ranshi yasan lokacin baccinta beyi ba dan kullum yana kiranta at this time kuma sukan kai past 11 suna hira.
Yah kasa gane dalilin qin d'aukan wayarshi da tayi,da a tunaninshi koh bata kusa da wayar neh amma daga baya yace qila bata duba wayar baneh amma data kirashi.Shima dae a hakan yyi bacci.
*************************
Fahyim kuwa hankalinshi kwance yah bar gidansu Suhana,saeda yah tsaya ya sayi recharge card kafin yah wuce gida.
A palour yah samu Ammee da Abida suna kallon *Habeebi Da'eeman* a mbc_drama,sallama yyi suka answer sannn yah shigo.
Abida ceh tace "sannu da dawowa yaya!",Fahyim yah answer da "yauwa qanwata",sa'annan yah nemi guri yah zauna kusa da Ammee.
Ammee ta dubeshi cikeda kulawa irinta uwa tace "an dawo",yace "na dawo Ammee".
Tace "toh yah kukayi da ita?",yace "as usual tamun wulaqancin nata,but naga ta d'an rangwanta mun yau",dariya Ammee tayi kafin tace "Suhana y'ar gari!! Karka damu ina meh tabbatar maka da cewa she will totally fall for you soon,just wait and see".
Fahyim yace "da alamu kam,saedae ince Allah yasa hakan yah kuma zab'a mana mafi alkhairi",Ammee tace "ameen".
Abida tunda suka fara maganar take quluwa ta zumb'ura baki tareda tab'e shi kafin ta tashi ta bar wajen.
Kallo suka bita dashi harta shiga d'akin kafin suka juyo suka kalli juna tareda yin dariya dan sun san damuwarta be wuce akan maganar Suhana da sukeyi ba.
Fahyim neh yah tashi yace ma Ammee "barinje inyi lallami Ammee",Ammee tayi dariya tana fad'in "a fito lafiya".
************************
A zaune yah sameta ta wani b'ata rai kamar meh shirin yin kuka.Yah qarasa inda take zaune a gefen gadonta shima yah samu waje yah zauna.
Yah dubeta sannan yah fara mata magana cikin rarrashi "haba qanwata,meh yyi zafi haka?".
Tace "ni bada kai nake ba,abu nagani a tv",ta wani yi folding hannayenta biyu tareda gyara zama.
Dariya kwae Fahyim yyi dan sarai yasan akan maganar da sukeyi neh saedae be musa mata ba saima ce mata da yyi tayi haquri toh,yyi ta bata haquri kamar wacce akayi ma laifi.
Saeda suka shirya kafin yah bar d'akin,bayan yah koma palour yah fad'a ma Ammee yadda sukayi yana dariya.
Itama dariyar tayi tareda fad'in "Allah yah yaye ma Abida".Fahyim yah dau ma kanshi alqawarin tun daga ranar bazae qara yin wata magana da ta shafi Suhana a gaban Abida ba saedae in Allah yyi ita matarshi ceh.
Bayan sun gama hirarsu dukansu suka koma d'aki.Fahyim na shiga d'akin nashi yah canza kayan jikin shi zuwa na bacci.
Wayarshi yah d'auka inda yah kunna mobile data tareda hawa whatsapp.
Messages neh suka fara shigo mishi da yawa dan tun jiya rabonshi daya hau.
*HAMAGEE*
[10:16pm, 3/27/2017] Hamagee: Hamagee: garbahama69@gmail.com
💦 💦💦💦 💦
*LAIFIN WAYE??*
💦💦💦 💦💦💦
_Written by the Aplomb writer: *Hamagee*_
*In devotion to Maman Saif*
💦
*You Need A Plan To Build A House. To Build A Life, It Is Even More Important To Have A Plan Or Goal.....*
http://www.hamageenovelsseries.com/facebookpage
Wattpad @Hama_gee
Page 21
Contact na Suhana yah hau kamar kullum,inya hau saeya duba even though be tab'a yi mata magana anan ba.
To his supprise saeya ganta online,kuma tayi viewing profile nashi,daman version d'inda yake kan wayarshi na iya nuna maka mutanen da sukayi viewing profile naka.
Dariya yyi kawae sannan yah fita daga contact nata yah cigaba da chatting d'inshi,chan yah sake dubawa koh still tana online.
Dubawan shi keda wuya yaga last seen nata 10mins da suka wuce.Shima sauqa yyi yah rufe data sannan yyi addua yah kwanta ta hannun damanshi.
Da Suhana a ranshi yyi bacci ranan.
************************
Washegari da safe bayan Suhana tayi breakfast ta d'au wayarta tana dubawa.Kamar yadda tayi expecting haka ta gani.
Daman tana expecting ganin missed call na chocolate d'inta,hakan kuwa ta tarar.
Tayi murmushi kafin ta fara dailing numbern nashi.Kafin yah gama ringing yyi rejecting tareda sake kiranta.
Tayi picking tana fad'in "my one!",Sadeeq yace "naam beauty,shine jiya nayi ta kira bakiyi picking ba koh,kka sa na kasa yin bacci meh dad'i".
Suhana tace "am so sorry dia wllhi bacci nayi da wuri shiyasa,kasan bazan kasa picking call naka ba ae.But am so sorry,I apologize!".
Yah d'anyi dariya kafin yace "apology granted my queen!!",dukansu suka yi dariya.
Hirarsu suka cigaba dayi daga bisani sukayi sallama yyi hanging call d'in.
*************************
Washegari tunda hantsi Sadeeq yazo yah d'auki Suhana sukayi ta yawon holewarsu,basu suka dawo ba kuma sae can yamma liss dan har ana kiran sallahn magrib.
Alaramma nah tafe yana lazimi zashi masallaci,d'aga idon da zaiyi kwae yaga mota a pake qofar gidan su Suhana,ganin Suhana ta fito daga motar yah bashi mamaki saboda wannan lokacin be dace ace duk wata budurwa y'ar kirki kuma an ganta da saurayi ba.
"Allah shi kyauta",yah fad'a tareda qara hanzari dan lokacin sallah yah gabato.
Alaramma limamin unguwarsu Suhana neh,ainihin sunanshi kuma shine malam Hamisu,bawan Allah neh shi kuma meh gaskiya da son addinin Allah.
Bugu da qari shi malami neh dan yah kanyi tafsir a masallatai daban-daban a garin Kaduna.
A taqaice dai shi mutumin qwarai neh,suna mutunci qwarai da daddyn Suhana dan shima mutumin arziqi neh.
Sallah bata wuce shi gashi da son kyautatawa mutane,sau tari kuma yah kan bada gudumawa ta kud'i koma nah wani abun dan ganin cii gaban masallacin unguwar dama sauran wasu masallatan.
Wannan dalilin yasa Alaramma keh ganin martabar shi.
*************************
Bayan shigar Suhana gida Sadeeq yajaa motarshi yayi gaba,lokacin kuwa Alaramma harya isa masallaci,ladan kuma yah kira sallah.
Tana shiga sukayi karo da Daddyn ta zashi masallaci,"ah! An dawo? ",inji shi kenan.
Suhana kuwa ta wani marairaice irin ta gajin nan kafin tace "iy daddy nah dawo,wallah duk na gaji,yau tests hud'u mukayi".
Daddy yace "ayyarh sannu,yanzu ki shiga kije ki huta kafin nah dawo",tace "toh dad"tareda juyawa tayi cikin gidan cikeda jin dad'i.
Daddy kuwa girgiza kai yyi tareda juyawa shima yah fice.Massalaci yah nufa.
Suhana nah shiga ta tararda Mommy zaune a palour tana shirin tashi ta koma d'akinta.
Qarasowa tayi tazo ta zuba a jikin Mommyn tana fad'in "am so tired Mom!".
Mommy tah dubeta kafin tace "sorry daughter tun d'azu nake jiran dawowarki,hope ba wata matsala!" .
Suhana ta d'ago kanta tana kallon Mommy,tace "bbu komai sae gajiyar school,yau tests hud'u fa muka yi".
Mommy ta d'anyi jim alamun ta tausaya ma yarta tace "sannu,yanzu kije kiyi wanka kiyi sallah ni kuma zan d'aura miki pudding kafin ki fito".
Suhana tace "that's my mom!"tareda manna mata kiss a kumatu,tashi tayi ta nufa d'akinta,binta kawae da kallo Mommy tayi tana girgiza kai.
*HAMAGEE*
[10:16pm, 3/27/2017] Hamagee: Hamagee: garbahama69@gmail.com
💦 💦💦💦 💦
*LAIFIN WAYE??*
💦💦💦 💦💦💦
_Written by the Aplomb writer: *Hamagee*_
*This page is yours Fiyya galadanci,ina taya ki murnan kammala littafinki meh suna _Almajiri nah_,Allah yah qara basira da d'aukaka..waiting for your new page dia,stay blessed...*
💦
*Love the lovers and forget about the haters,the should die heartlessly....*
http://www.hamageenovelsseries.com/facebookpage
Wattpad @Hama_gee
Page 22
Tashi Mommy tayi ta shiga kitchen kasancewar bata sallah ranan,ta d'au tukunya ta zuba ruwan zafi ta d'aura.
Suhana kuwa tana shiga d'akin ta zube a kan gado koh cire takalmi batayi,saedae qafan nata ba'a kan gadon yake ba.
Smiling tayi tareda janyo wayarta ta shiga gallery inda ta hau kan hoton Sadeeq wanda ta d'auka d'azu bbu kaya a jikin shi,da wanda sukayi selfie su biyu.
Kallo tay tayi cikin jin dad'in,a ranta taita tuno irin abubuwan da suka faru tsakaninsu yau.
Daga qarshe ta tashi ta cire kayanta ta shiga wanka,bayan tayi wankan saeta had'o da alwala tazo tayi sallahn azahar,la'asar,magrib dan koh sallahn azahar bata samu daman yi ba yau.
Tana idarwa kuwa ta tashi tayi isha dan already anyi sallahn a masallaci.(Yah Allah ka hanemu da yin duk wani abun da zai hanamu bauta maka). ***********************
Daddy ko bai dawo ba saeda akayi sallahn isha'i,da sallama yah shigo,lokacin Mommy ta fito kenan daga kitchen riqeda bowl meh containing pudding d'in a ciki.
Ta answer sallaman tareda qarasowa palourn ta zauna. "an dawo?",inji Mommy,Daddy yace "wllh kuwa!".
Mommy tace "hope nima kamun addu'a",cikin shagwab'a tayi maganar.
Daddy yace "na miki mana",dariya sukayi dukansu.Daddy yace ta d'auko mishi fruits_salad d'inshi nah d'azu a fridge.
Mommy ta tashi ta d'auko ta kawo mishi.Komawa tayi ta d'auko glass d'in sugar a kitchen ta kawo palourn.
Ta zuba sugarn a sauran pudding d'inda tayi ma Suhana,ta miqa ma Daddy,daddy yace "kai!! Bazan sha ba dama na fad'a miki wannan fruits d'in are ohk for my dinner".
Mommy tace "it's alright then!",ta motsa kafin ta fara sha.Daddy neh yah d'au remote yah canza channel d'inda suke kallo zuwa AIT inda ake news.
Daedae lokacin Suhana ta fito,tana sanye da y'ar rigarta me qaramin hannu.
Qarasowa tayi ta zauna tana fad'in "tnks Momma!",Mommy tace "welcum my dearest".
Pudding d'in Suhana ta d'auka ta zuba sugar sannan ta soma sha.Saeda ta gama sha sannan ta kira Hadiza tazo ta d'aga bowl d'inda keh gabanta.
Wayarta ta kunna tareda bud'e data sannan ta soma chatting,daedae lokacin Sadeeq ma yah hau.
Ita ta fara mishi magana,saeya answer sannan suka cigaba da chatting d'insu.
**************************
Washegari thesame thing happens,Alaramma yah fito zashi masallaci saeya ga thesame mutumin jiyannan yah sauke Suhana a gida kuma dab magrib.
Abunda yah qara bashi mamaki ma shine ganin Sadeeq yyi kissing d'inta kafin ta fito,ita kuma tana mishi dariya.
Yyi niyyar yah tsaida shi yyi mishi magana amma sae wata zuciyar tace mishi aa ba haka yah kamata kayi ba,gwara ka samu mahaifinta tunda kuna mutunci dashi inyaso ka sanar mishi abunda yake faruwa.
Hakan kuwa akayi,Alaramma yayi tafiyar shi da niyyar in an idar da sallah zae sanarda Daddyn Suhana abunda ake ciki tunda yaga yana tsayawa har sallahn isha.
Sadeeq kuwa jaan motarshi yyi yah qara gaba.Ita kuma Suhana ta shiga gida kamar jiya jikinta a gajiye take jinshi.
Yau bata samu kowa a palour ba haka ta wuce d'akinta hankalinta kwance bbu wani d'ard'ar.
"Kaii! Suby kamar wata mayya ta isheni wallahi",ta fad'a a d'an fusace.Wayarta daketa faman ringing tun shigowarta ta ciro a jakarta tareda answering call d'in.
"Hello yane kam?",tayi tambayar a fusace.Suby tace "dalla zanma tambayeki ya kuka qare da don d'in naki".
Suhana tace "bari kawae Suby wllh duk a gajiye nake yanzu,Sadeeq bashida sauqii".
Suby tace "shegiyar kaya kice komai yah warware yau!",Suhana tace "ae bbu wani qullin daya rage yanzu".
Suka kwashe da dariya dukansu,Suby tace "to ki samu kiyi wanka ko zakiji daedae barin barki haka!".
Suhana tace "ohk sae munyi magana",Suby tayi hanging call d'in,Suhana ta ajiye wayar sannan ta tashi ta shiga toilet tayi wanka da alwala,kafin ta fito tayi salloli kamar jiya,azahar,la'asar da kuma magrib yau kam ba'ayi isha ba tukunna.
*HAMAGEE*
Hamagee: garbahama69@gmail.com
💦 💦💦💦 💦
*LAIFIN WAYE??*
💦💦💦 💦💦💦
_Written by the Aplomb writer: *Hamagee*_
*In devotion to Maman Saif*
💦
*Do your best and leave the rest to almighty Allah,because he's the one incharge of making everything to happen!!....*
http://www.hamageenovelsseries.com/facebookpage
Wattpad @Hama_gee
Page 23
Bayan ta idar da sallahn zama tayi bata tashiba,saeda tayi sallahn isha kafin ta tashi.
Bayan ta ninke himar d'inta saeta kwanta a nan bacci yyi gaba da ita..
★
Daddy da Mommy suna zaune a palourn daddy suna kallo aka fara kiran sallahn magrib,tashi yyi yah nufa d'akinshi yayo alwala sannan yah nufi masallaci.Sauri yyi tayi dan lokacin har an shiga sallahn dan yah d'an b'ata lokaci a toilet d'in kafin yah fito.Allah yaso ma sanda yah isa masallacin ba'a kai raka'a ba kasancewar masallacin bbu nisa da gidan dama.
Bayan an idar da sallah be wani jima ba yah koma gida saboda fitsarin da yake ji.So wannan yah hana Alaramma samun damar yi ma Daddy magana kenan.
Bayan yah dawo gida saeda yah sake alwala sannan yah koma masallacin da yaji ana kiran sallah.Bayan an idar saeya dawo gida.Bayan yah dawo sae yake tambayar Mommy Suhana,Mommy tace "maybe ta dawo barin dubata".Daddy yace
"ohk dubota kam".
Koda Momny ta shiga d'akin a kwance ta sameta,ganin bata juyo taga wayeba yasa Mommy juyawa ta fice dan a zatonta bacci Suhana takeyi.
Bayan ta fita saeta rufo mata qofar ta koma palourn Daddy ta fad'a mishi cewa Suhana na bacci,Daddy yace "it's alright ina ga ta gaji neh da yawa".
"I think so",inji Mommy.
Bayan sun d'an jima suna kallon sae sukaje suka kwanta bacci.
Suhana kuwa tashin da batayi ba kenan a ranan,koda Sadeeq yah kirata mah bata ji ba dan gajiyar da tayi.Haka yyi yah gaji yah rabuda ita yyi bacci shima.
Fahyim kuma fa??
Around qarfe biyu da rabi yau yah fito daga chamber zashi gida yah dawo dan bai kammala aikin shi nah yau d'inba,har yah wuce wurin sae kuma yah tuno yau sukayi da wani meh gyaran waya zai qarb'a wata wayar shi daya bayar shi gyara kwanaki uku da suka shige.
Har yyi kamar zae fasa tunda already yah wuce wajen sae kuma yah fasa.Dawowa yyi qofar shagon yyi parking sannan yah fito daga motar yah nufa shagon.
Koda yah shiga sae ya samu yaronda yah bashi gyaran baya nan,yaji haushi qwarai dan sauri yakeyi kuma da tsayuwannan da yyi yah kusa isa gida,gashi yanzu har to three kuma three thirty zasu koma.
"damn it",yah fita kwae zae koma cikin motarshi yah tafi,wani abun mamaki da takaicin daya gani yasa shi suman tsaye dan kasa tafiya yyi.Daga qarshe ma qafafun shi kasa d'aukanshi suka yi a wajen yah zube yan kallon ikon rabbi.
Kun san meh yah gani??
Suhana ceh da Sadeeq sun fito daga wani d'an qaramin hotel d'innan wanda ba'a cika samun customers masu kwana ba yawanci irin wanda maza keh hutawa a cikin nan neh,maybe ka fito daga office kuma baka son komawa gida @ that time.Koh kuma matafiya da basu gama tafiyar tasu ba kuma sunaso su d'an huta,maybe suci abinci suyi wanka kafin su cigaba da tafiyar,da dae sauransu.
Abunda yah fi bashi haushi ma shine ganin yadda Sadeeq yah rirriqeta kamar meh bacci a jikinshi suna tafiya zasu shiga mota.Har suka shiga motar suka tafi be iya motsawa daga inda yake ba.
Wani irin yanayi yah shiga a lokacin,ranshi yah mugun b'aci @ that very moment,idanuwanshi sunyi jaa kamar zaiyi kuka.Shi kad'ai yasan abunda yake ciki a wannan lokacin.Tunani iri_iri yyi tayi.
"first wannan yaron yah bata mun lokaci,and now Suhana! How can she do this to me? I can't believe my eyes of what I just saw,is that how really she is?,my god! Why? Why, meyasa na kamu da sonta while she isn't my type?,she's not meant for me because I can't marry someone like her,bazan iya auren mazinaciya ba".
Kuka yah soma yi kamar qaramin yaro.Da qyar yah iya tashi daga wurin yah koma cikin motarshi yaci gaba daga inda yah tsaya.
Yama rasa inda zaesa kanshi dan ba qaramin tashin hankali yah shigaba ganin Suhana da wani kuma daga hotel,sannan tana kwance a jikinshi.
Fahyim namiji neh meh matuqar kishi koh a wajen nema ballantana irin wannan,bashida neman mata wanda yasa shima baya son mace meh sauraron tarin maza.A rayuwarshi be tab'a zaton zae samu Suhana da aikata irin wannan sab'on ba.
He's disappointed in her,totally.Da qyar yah iya driving zuwa gida inda yayi ta tunanin yadda zae fahimtar da iyayenshi kan yah fasa neman Suhana,dan for sure yace yah fasa sae sun tambayeshi dalilin yin hakan saboda yadda yake son suhana.
HAMAGEE
Hamagee: garbahama69@gmail.com
💦 💦💦💦 💦
*LAIFIN WAYE??*
💦💦💦 💦💦💦
_Written by the Aplomb writer: *Hamagee*_
*In devotion to Maman Saif*
💦
*Hoping for da best!!....*
http://www.hamageenovelsseries.com/facebookpage
Wattpad @Hama_gee
Page 24
Bayan yah koma gida be iya yaci komai ba,wanka kwae yyi sannan yah koma,gaba d'aya baya jinshi adaedae.
Suna aiki kan wani case neh kuma shine lawyern wanda ake qara,gaba d'aya hankalinshi baya gurin,daga qarshe d'aga case din akayi zuwa wani lokacin.
Bayan yah koma gida around 5 nah yamma Ammee tasa shi wae yaje wajen Suhana d'azu sunyi waya da Mamanta tace bata nan amma zuwa yamma zata dawo.Bbu musu Fahyim yace toh amma ta kira ta sake tambayanta koh ta dawo tukunna.
Ammee ta kira Mommy inda mommyn ta sanar mata cewa bata dawo ba tukunna.Maybe saeda daddare yazo.Bayan sunyi sallama Ammee tayi hanging kafin ta fada ma Fahyim yadda sukayi.Yace shikenan saedae zuwa gobe da yamma yaje,Ammee tace "Allah yah kaimu".Yace "ameen".
Tashi yyi yah bar gidan inda yah nufi gidansu Aasim yah dan rage damuwar shi acan.
Aasim abokin Fahyim neh sosae dan tare suke tun yaranta.Halinsu yazo d'aya wanda hakan yasa abotar tasu yin qarfi da kuma jimawa.Daga ganin Fahyim Aasim yah fahimci cewa yana cikin damuwa dukda yaqi sanarda shi abunda keh damunshi.
Saeda Aasim yah matsa mishi tukunna yah sanarda shi komai.Aasim yah girgiza kai tareda dafa qafad'an Fahyim "you have to be strong my frnd,don't let this worry you at all wasu matan haka suke dama,kuma ina ganin wannan ba abun d'aga hankali bane dan Allah neh yah sanarda kai komai tun wuri tun kafin lokaci yah qure maka,so kayi haquri ka mance da ita kwae".
"Nifa bama abunda na gani bane damuwata Aasim,damuwata ita ce yadda zan fad'a ma su Ammee na fasa auren dan bazan iya fad'a musu abunda daya faru ba truely".
"You have to! Ka cire duk wani damuwa a ranka ka fuskanci iyayenka ka sanarda su duk abunda kke ciki without any worry kaji".
"I don't think I can,saboda hakan zae ba'ta musu rai matuqa dan yadda suke da iyayenta yah wuce yadda kke zato".
"But you must,because keeping silent will just hurts you more,amma don't you worry,zamu samesu,I will try and explain everything to them".
"It's ohk,as you said".Aasim yah jaashi da surutu har saeda sukayi sallahn magrib kafin yah tafi gida.
Washegari da yamma bayan sallahn la'asar bayan Fahyim yah dawo gida yah kira Aasim a waya.
"Assalamu alaikum"
"waalaikas salam ka dawo neh?"
"Wllh kuwa,yanzunnan shigowa ta,ina jiranka saeka zo".
"It's ohk am on my way",Fahyim yyi hanging call d'in.Bayan kamar 20mins da gama wayan saega Aasim yah iso,yah gaida Ammee dake zaune a palour tana kallo,Ammee ta anda cikeda fara'a a fuskarta.
Bayan sun gama gaisuwar saeya tashi yah nufa d'akin Fahyim,anan suka qarasa shirya yadda zasu b'ullowa lamarin.
Bayan sunyi sallahn magrib sae suka jee side d'in Abbaa inda suka tararda shi a palournshi yana kallon news.Aasim yah gaidashi cikeda girmamawa shima yah answer mai cikin fara'a.
Bayan nan sae Aasim yah shiga yima Abbaa bayanin duk abunda ake ciki cikin nutsuwa da fahimtarwa.Abbaa yah fahimce shi sosae kuma beji dad'in abunda yah faru ba.
Nan yace ma Fahyim duk hukuncin daya yanke yayi daedae bazae tilasta shi ba daga bisani yah sa mishi albarka,su kuma sukayi godiya kafin suka tashi suka bar palourn..
HAMAGEE
💦 💦💦💦 💦
*LAIFIN WAYE??*
💦💦💦 💦💦💦
_Written by the Aplomb writer: *Hamagee*_
*In devotion to Maman Saif*
💦
*Every soul must taste 'death',yah Allah,let our last word be the kalamatush shahada!!!....*
Page 25 💦💦
Bayan sallahn isha Aasim yyi ma su Ammee sallama kafin yah wuce gida.Fahyim kuwa sae godiya yake mishi dan ba qaramin temakon shi yyi ba yau.
Thesame ranar bayan sallahn isha,gaba d'ayansu suna zaune a palour suna kallon wani channel da ake animal show,they're all interested in the show.Abbaa yah dubi Ammee kafin ya gyara muryarshi,d'agowa itama tayi tana kallonshi don daga jii tasan wani abun yake son cewa.
Yace "nikam kunyi magana da d'anki kafin yah sameni neh?,dan naji baki mun wata maganar ba which u'r suppose to!".
Ammee ta qara dubanshi cikeda 'what did he mean look' kafin tace "wace magana kenan?".Abba yah dubi Fahyim kafin yace "baka fad'a mata abunda kuka sanarda ni d'azu ba?".
Da qarfi qirjin Fahyim yah buga tareda ware ido kamar beran da yaje sata aka kamashi.Sarai yasan halin Ammee,zata iya cewa bata san magana ba dan tana mugun son had'a aurenshi da Suhana da ake shirin yi.
Daurewa yyi yace "eh ban sanarda ita ba,dama zan fad'a mata",Ammee ta juya ,ta qare mishi kallo kafin ta dawo da kallon nata wurin Abba.
Abbaa yace "auren shi da yarinyar nan bazai yiwu ba saboda yawon banza takeyi,yace yau da idonshi ya ganta,ko ba haka kuka ce mun ba?",ya qarasa maganar yana nuna Fahyim da baki.
Fahyim yace "wllhi hakane Abba,d'azu da idona na gansu da wani suna fitowa daga hotel,I can't beer to see her as my wife,I can't",ya qarasa maganar yana sadda kai qasa.
"Will this mouth of urs be shut!!"Ammee ta fad'a cikin tsawa tareda da'gowa daga jinginon da tayi a kan kujera,tace "let my ears not hear this again Fahyim,dan wllh ranka zaeyi mugun b'aci,koda wasa don't u try me this evening",tana nunashi da yatsa.
Abbaa dai baice koh qala ba,Abida kuwa haushi taji sakamakon ganin yadda Ammee ke neman hana Fahyim qin auren Suhana,afterall rashin yiyuwar auren shine babban burinta a kullum,toh gashi Fahyim yah fahimta amma Ammee nah neman hanashi,ita bata san miye damuwan Ammensu da auren Suhana ba.
Fahyim kuwa sufa neh ya shigo keto mai,yama rasa ta inda zai fara fahimtar da Ammee,can bayan d'an wani lokaci yace "Amma dae Ammee kinsan bazan yi mata sharri ba koh? Kuma koma miye ba ni bane nace ina sonta,don miyasa yanzu zance banayi batareda wata hujja mai qarfi ba? Ammee ki duba dan Allah wllhi yarinyarnan isn't my type".
A fusace Ammee tace "da can baka san ba type dinka bace sae yanzu?,tambaynka nakeyi,nace baka sani ba tunda sae yanzu? Toh tashi ka bani waje taashii nace!!",haka Fahyim naji ya tashi ya bar palourn zuciyarshi a dagule.
Abeeda tace "haba Ammee,dan Allah ki bar yaya yyi abunda yaga yafi mishi mana,after all shiba yaro bane kuma Suhanan nan shi yah gani yace yana so bawae zab'an mishi ita akayi ba balle ace he's looking for a way out".
"Mun shiru,kema tashi kibani waje",Ammee ta fad'a cikin tsawa.Sad'af-sad'af ta tashi itama ta qara wuta,side d'in Fahyim ta wuce .
Abbaa ma yah tashi ya shiga side d'inshi,ya rage Ammee ceh kad'ae a palourn,itama bayan kaman 5mins haka ta tashi ta shiga ciki.
★★★
Da sallama Abeeda ta shiga d'akin ta sameshi kwance akan katifar d'akin,koda yah answer sallamar bae juyo ba bai kuma sake cewa komai ba.Itace ta nemi guri ta zauna tareda fad'in "kayi haquri yaya!Kaga abunda nake ta guje maka tun farko,Allah ma yasa ka ganota tun kafin ka aureta".
Fahyim bece mata komai ba,tayi ta surutunta harta gaji,daga qarshe yace ta tafi ta bashi guri ma,haka ta tashi tabar d'akin batareda taji dad'in yadda yyi mata ba,amma a ranta tasan tension neh ke damunshi shiyasa ta bashi uzuri.
Gaba da'yansu da qyar zukayi bacci ranan..
HAMAGEE
💦💦
*©QUEENS ONLINE WRITERS*👑✍
💦
_Written by the Aplomb writer: *Hamagee*_
*In devotion to Maman Saif*
💦
Page 26 💦💦
Washegari da yamma Daddyn Suhana nah kwance wayanshi tayi ringing,d'agawan da zaiyi sae yaga numbern meh gadi neh,bayan yah answer sae sallamar meh gadi yah biyo baya,Daddy yah answer tareda jiran yaji abunda zae fad'a,meh gadi yah sanar mishi cewa Alaramma neh yazo wajenshi.
Daddy yace yah shigo yah jirashi yana zuwa,meh gadi yace toh kafin yyi hanging call d'in.Yadda daddy yace yyi hakan yyi tareda fad'a ma Alaramma cewa me gidan yana zuwa wae yah jirashi,wata kujera yah bashi kusada wajen car park yah zauna.
Bada jimawa ba Daddy yah fito sanye da farar jallabiyar shi,yah miqa wa Alaramma hannu suka gaisa kafin nan yah zauna,bayan wasu y'an gaishe-gaishe sae Alamma yah fara sanarda shi abunda yake tafe dashi.
Maganar Suhana ceh ba wani abunba,nan yah kwashi duk abunda yah gani tun daga shekaranjiya har zuwa jiya da kuma yadda yaso sanar mishi jiya amma be samu dama ba,duk yah kwashe yah fad'a mishi.Bayannan saeya qara da cewa "Kuma ni a gani nah duk mun zamo da'ya,shiyasa bazan iya ganin abunda zae shafi gidanka mara kyau kuma in qyale ba,sannan ba wae na kawo maka qorafi bane koh wani abun,aa na sanarda kai neh saboda zaman tare,ya kamata kuma kasan meke faruwa a gidanka saboda tun wuri ka tareshi".
Tunda ya fara magar Daddy bece komai ba sae d'aga kai da yakeyi.Yah qare ma Alaramma duba kafin yace "Malam Hamisu!!",Alaramma ya answer "ranka yah dad'e".Daddy yace "ita yarinyar nan da kke magana akanta y'arka ceh koh tawa?".
Alaramma was so supprised with the statement,yace "y'arka ceh",Daddy yace "toh bbu ruwanka da sabgarta,bana son irin haka kaga muna mutunci da kai saboda haka kar kasa wani abu yah shiga tsakaninmu dan kana neman wuce gona da iri".
Baki sake Alaramma yah tsaya yana kallon Daddy,be iya fad'in komai ba dan tsaban mamaki,ace an kawo maka magana kan abunda y'arka takeyi mara kyau amma kabi bayanta,Allah yah sauwaqe,inji Alaramma a ranshi.
Daddy yah cigaba "dan haka ka rufe kunnenka da idonka akan ya'ta,in Allah yyi ma mutum arziqi saeya samu maqiya,haka nan in Allah yyi ka da kyau sae ka samu mahassada,inba kaiba yarinya kamar Suhana ace bazata yi samari ba,ai koh bata kulasu sae sun bita ko zasu samu shiga,saboda haka bana son sake jin wata magana makamancin wannan akan ya'ta".
Alaramma yace "shikenan Alhj.insha Allah wannan shine na qarshe",yyi mishi sallam kafin yah tafi,a ranshi yana mamakin abunda yah faru,koh a wasa aka ceh mishi Daddy zaiyi haka bazae yarda ba amma yanzu yah shaida wa kanshi,'lallae yana dab da fad'awa halaka indae komai yarinya tayi daedae neh',inji Alaramma a ranshi yake fad'in hakan.
Daddy kuwa tashi yyi yah shiga ciki abunshi yana meh jin haushin Alaramma,koda yah shiga saeda yyi wa Mommy tad'in,itama taji haushin Alaramma wae yana baqinciki neh dan yaga Suhana nada manema wa'inda suka fishi.
★★★
Suhana kuwa tana can suna ta sheqe ayarsu da Sadeeq da sunan ta tafi makaranta,dan yanzu ta daina attending class a cewar Sadeeq wae ta kwantar da hankalinta indae maganan class neh ba sae taje ba,shi yana da hanyar da zaesa ta samu flat-A a result d'inta ma,dan haka karta damu.Hakan yasa Suhana ta kwantar da hankalinta take kuma biyewa Sadeeq.
Kamar kullum saeda yamma liss Sadeeq yah sauketa a gida kafin yah wuce.
Bayan sallahn isha suna zaune a palour Mommy ta d'ago da tad'in,Suhana tace "lallae mutumin nan da gulma,toh wllh yah sake yah shiga harqata bazan barshi ba",Daddy yace "kina shirunki nima nan bazan barshi ba".Haka sukayi ta juya magana daga bisani suka sako wata chaptern.
★★★
*Fahyim......*
Washegari da safe Fahyim yaje gaida Ammee,ga mamakinshi sae yaji tayi shiru bata answer mishi ba,abun yah matuqar girgiza shi dan be tab'a ganin hakan ba tunda suke da ita.
Koda yah sake gaisheta a karo na biyu saeta answer ciki*2 ba dae yadda ta saba ansawa ba.Ba tareda b'ata lokaci ba fahyim ya tsinci kanshi yana mai bama Ammee haquri kan abunda ke faruwa dan yasan fushin nata nada nasaba da hakan.Ga mamakin shi Ammee ta d'aga mishi hannu kafin tace "ina kayi abunda kke so?to ka tashi ka je karka dameni,do whatever u think is right"..
Kamar Fahyim zae sake magana sae kuma yah fasa ganin yanayin da take ciki,dan haka yah tashi yah bar dakin.Dakin shi yah koma yah kwanta a ranshi yana tunanin next step daya kamata ya bi wajen shawo kan Ammeenshi.Daga qarshe dae ya rage mishi mafita guda wato ya nemi abokinshi wato Aasim dan neman shawarar shi kan lamarin,kamar wanda aka mintsina yah janyo wayarshi dake charge kan bed-side drawer yah shiga nemo numbern Aasim.
Dailing numbern nashi yah shiga yi,ringing na farko Aasim yah d'aga wayar,bayan sun gaisa sae Fahyim yah tambaye shi kan yana gida neh,Aasim yace yana nan..
HAMAGEE
💦 💦💦💦 💦
*LAIFIN WAYE??*
💦💦💦 💦💦💦
_Written by the Aplomb writer: *Hamagee*_
*In devotion to Maman Saif*
*This page is honoured to my three dearies:Jidda,Princess Aisha and Rabi'atu, _#Hamagee loves and cherish the both of u_* 😍😘
💦
Page 27 💦💦
Fahyim yace "ohk,gani nan zuwa yanzu akwae maganar da nake so muyi".Kamar Aasim zae tambaye shi lafiya kuwa,sae kuma yah fasa tareda fad'in "till you come",Fahyim yace "aha bye".Nan yyi hanging kiran tareda samun wani qwarin gwiwa yah miqe yah d'au keyn mota tareda ficewa koh wanka beyi ba balle aje ga maganar yin breakfast.
Fitowarsa tayi daedae da fitowar Abida zata je gaida Ammee,"ina kwana yaya Fahyim",ya answer "lfya lou Baby,an tashi lfya?",tace "lfya lou".Bayan sun gaisa sae taga alamar fita zaeyi,hakan yasa ta tambayeshi "yaya da wuri haka zaka office d'in yau?".Yace mata "eh" kwae dan baya son yawan magana.
Ta mishi adawo lfya kafin nan ta nufa dakin Ammee shi kuma yah nufa hanyar fita.A tsaye ta samu Ammee a gaban walldrop dinta tana gyara kaya,tayi sallama kafin ta shiga bayan Ammee ta answer.Har qasa ta tsuguna kafin ta gaidata,Ammee ta answer tareda tambayar lafiyarta,bayan sun gama gaisawa sae Abida ta tashi ta bar d'akin,kitchen ta nufa dan shirya musu breakfast..
********
Kai tsaye gidansu Aasim yah nufa,yana addu'ar neman mafita.Yana isa yyi parking motarshi a waje ba tareda ya shigarda ita ciki ba,yyi knocking baba me gadi yah bud'e mishi yah shiga.Saeda suka gaisa kafin yah wuce cikin gidan.A ta farko_farko dakin Aasim yake dan haka yana shiga palourn yah wuce ciki batareda bata lokaci ba.
Aasim na zaune yana aiki a labtop dinshi yaji sallamar Fahyim,yah answer tareda juyowa yana kallon qofar,Fahyim yah qaraso ya bashi hanu sukayi musabaha kafin yah zauna a gefen Aasim.Aasim yah kula da yanayin Fahyim sosae,yah fahimci irin damuwar dake tattareda shi dan haka ya ajiye system din a gefe kafin yah komo gareshi yace "meke damunka abokina?".
Ba tareda bata lokaci ba Fahyim yah sanarda shi dukkanin abunda yah faru,kama daga ranan daya ga Suhana da wani har zuwa yau da Ammee bata son kulashi.Yah qara da cewa "ni yanzu babban damuwa ta daya ceh,kuma shine fushin da Ammee keyi dani.Shi kadae yah damen".Aasim yace "hakane wannan,dan shine abun ji gaskiya,yanzu karka sama kanka wani much tension,everything will be resolved by d grace of Allah kaji,zamu samo mafita".Fahyim yah daga kai alamar eh tareda jin wani dan sanyi a ranshi dan yasan kamar yadda abokin nashi ya fadi to zae sama mishi mafita.
Sun jima suna tare kafin Aasim yah kaishi suka gaisa da maman shi sannan yasa qanwarshi wato Fa'iza ta kawo musu breakfast dan shima har zuwa time din be karya ba.Fahyim be wani ci chips din da aka kai musu ba yaji yah qoshi,bayan nan suka fita tare.
************
Can tsakar dare,kowa yyi bacci ga iska ta ko'ina yana bada yanayi me dadi.Da alama ma hadiri neh a garin dan har qanshi ruwa kke ji,kowa yana baccinshi cikin kwanciyar hankali da jin dadi amma banda Suhana da matsanancin ciwon mara yah isheta.Tayi kukanta harta gaji daga bisani ta daga wayarta ta kira numbern Mommy,saeda wayar tayi ringing kusan uku dan na ukun ma har zae yanke kafin Mommy ta dau wayar,ba tareda ta duba waye ba ta daga cikin muryar bacci take fadin "waye cikin daren nan haka?".
Da qyar Suhana ta iya fadin "Mmommmmy",a birkice Mommy ta tashi zaune dan yadda taji murya kamar na Suhana kuma kaman tana wani halin.Saeda ta duba kan screen din wayar da kyau dan tabbatar da shakkunta kan Suhana ceh ko ba itaba,taga 'My princess' rubuce a kan screen din kafin ta mayar kunnen ta."Hello! Helloo! Suhanaa",amma ina shiru kke ji.Mommy ta qara rudewa dan ji take kamar an sace Suhana ne.Tashin Daddyn ta shiga yi shima a firgice yah tashi dan jin yadda take tashin nashi,"lafiyarki kuwa?" Tambayar da yyi mata kenan,bata iya bashi answer ba sae sunan Suhana da ta iya kira,yace "meya sami Suhanan? Yi magana mana".
Ganin bata da niyyar fadin komai yasa yah tashi yah saka jallabiyar shi tareda sa slippers sannan yah fice daga dakin yah nufi na Suhana.Ae tuni Mommy ta taso tabi bayanshi.
HAMAGEE
💦 💦💦💦 💦
*LAIFIN WAYE??*
💦💦💦 💦💦💦
_Written by the Aplomb writer: *Hamagee*_
*In devotion to Maman Saif*
💦
Wattpad@ Hama_gee
Page 28 💦💦
Koda suka isa qofar dakin a bude suka jishi,hakan yah sake tayar musu da hankali dan a zatonsu ko b'arayine suka shigo musu.Mommy ta qara tsurewa qafarta ta hau rawa dama Mommy akwae tsoro😜.
A hankali yah bud'e qofar ya fara shiga kafin Mommy tabi bayanshi.Ganin Suhana kwance tana riqeda ciki sae shure_shure da takeyi yasa suka kau da wancen zargin,da sauri suka nufo ta.Daddy neh ya fara tambayarta "what's wrong with you my princess?"cikin damuwa yyi tambayar,bata iya answer mishi ba sae sake riqe cikinta da tayi wanda hakan yasa suka fahimci cewa tana cikin matsanancin ciwon ciki neh.
Daddy yah umarci Mommy ta nemo mata maganin ciwon cikin in akwae da ruwa saeta sha suga yadda Allah zaeyi kafin susan next step da zasu bi.Da rawar jiki ta tashi ta nufa d'akinta ta d'auko maganin ciwon mara had'e da pain releaver da ruwa,tana zuwa ta cira ta miqa mata had'e da ruwan,Suhana ta qarb'a da qyar ta iya sha suna yi mata sannu.
Tashi Mommy tayi tace da Daddy tana zuwa kafin ta fita.Wasu herbs naga ta had'a tasa ruwa ta zuba a tukunya sannan ta kunna gas ta d'aura.Bayan wasu y'an mintuna da basu wuce 10 ba ta sauqe tayi sieving a cup sannan ta koma d'akin Suhana ta kai mata.D'an kad'an ma ta iya sha sae amai,gaba daya ta amayar da maganin da ta sha.
Kansu duk yah d'aure suka rasa ma abunyi,Daddy neh yah tambayi Mommy kan dama ta kanyi irin haka neh in period zaezo mata,Mommy tace bata tab'a yiba.Hankalin Daddy yyi matuqar tashi,yana tunanin kiran Family doctornsu amma yana ganin dare yyi da yawa.Ciwo kuma yaqi ci yaqi cinyewa dan har yanzu maranta na ciwo,a haka suka kai har asuba.
Around 5:30am bayan sallahn immediately Daddy yah kira Dr.Raheem yah sanar mishi komai,Dr.Raheem yace yana zuwa yanzunnan dan asibiti ba'a bud'e ba yanzu,Daddy yyi hanging call d'in.Koh sallah Suhana bata iya tashi tayi ba kuma ciwon yaqi barinta,gashi bbu wani alamun period balle tasa ran inya fito zata huta.
Bayan kaman 35mins suka ji bud'e gate dan Daddy yah kira Meh gadi yah sanar mai zuwan Dr.Raheem,Daddy neh yah tashi yah nufa main entrance door na gidan dan ya bud'e ma Dr.Raheem.Mommy kuma ta da'n gyara ma Suhana kwanciyarta tana fad'in "be patient my princess Dr.Raheem is here" a hankali dan a kunne ma ta rad'a mata.
Da hanzari Daddy yayi ma Dr.Raheem jagora zuwa d'akin Suahana koh gaisawa basuyi ba,nan da nan Dr yah fara aikinshi bayan yyi mata wasu tambayoyi tana bashi answer,idan answern eh ne saeta d'aga kai,in kuma aa ne saeta girgiza kanta.Bayan wasu y'an binciken da yyi yah gano cewa ba period pain Suhana keh experiencing ba instead she's 2months and a week pregnant da kuma wasu issues d'in,yama rasa ta inda zae fara sanarma iyayen gashi duk sae kallonshi suke suna jiran jin answer daga bakin shi.
Yah dubi Suhana yah tambayeta "when last did u see ur period?",Suhana ta nuna mishi yatsunta biyu alamun 2months ko a jikinta kuwa dan bata tab'a kawo ma ranta she'll be pregnant ba saboda irin qwayoyin da Sadeeq ke bata tana sha anytime she spend time wit him.Dr.Raheem yyi gyaran murya kafin yah dubi Daddy yace dashi "am sorry Alhj but your daughter is 2months and a week pregnant",wani hajijiya neh yah d'ebi Mommy dake tsaye tun shigowar Dr.Raheem d'akin,da sauri suka yi kanta Dr.Raheem yah bata immediate treatment tareda bata shawarar ta kwantarda hankalinta saboda condition da take ciki right now.
Bayan Mommy ta dawo daedae sae Dr yah koma wajen Suhana,ya bada wasu magunguna a bata sannan yyi wa Daddy sallama akan zae tafi,Daddy yace "ae ka tsaya tukun,miye yah kamata yanzu muyi dan I can't see my daughter in this condition,ya zamo dole a zubar da cikinnan".
HAMAGEE
💦 💦💦💦 💦
*LAIFIN WAYE??*
💦💦💦 💦💦💦
_Written by the Aplomb writer: *Hamagee*_
*In devotion to Maman Saif*
💦
Wattpad@ Hama_gee
Page 29 💦💦
Dr. Raheem yaja numfashi "hmmmmm",Daddy yace "yah dai? ".Dr. Raheem yace "there's a huge problem Alhj.I think it's better to face the problem u just mentioned than to abort the child ",Daddy cikin rashin fahimta yace "what do u mean? ",Dr. Raheem yace "let's talk outside please ",Daddy yah tashi yah bishi har suka iso palour, nan Dr. Raheem ya ganar dashi illar zubar da cikin.Take Daddy yah hau goge zufa, a taqaice dae Daddy yah sallami Dr. Raheem sannan yah koma d'akinshi. Gaba d'aya ma zazzab'i yah kama shi,da qyar yah iya d'aga wayar shi ya kira Mommy dake zaune gefen Suhana da already tayi bacci,ringing na farko ta d'aga kasancewar wayar na hannunta at the time.
Tana d'agawa yace da ita taje d'aki ta sameshi, ba tareda b'ata lokaci ba ta sauqe hannun dake kuncinta (tagumin da tayi) ta tashi ta bar d'akin tareda rufo qofar.
A tsaye ta sameshi yana zagaye a harabar d'akin cikeda damuwa, ta qarasa wajen da yake a rikice tace "meke faruwa neh? What did he told u? Is there something worse? Talk to me pls", Daddy yace "just calm down, let sit zan fad'a miki koma miye".
Suka nemi gu suka zauna idon Mommy na kan Daddy tana sauraron abinda zaice, yace "as he said Suhana is pregnant right?", Mommy ta gad'a kai alamar eh, Daddy yace "good! To that's not the main problem, Suhana ta cuci kanta and also have deceived us,Dr. Raheem yace wasu qwayoyi take sha wanda a yanzu haka sunyi affecting mahaifarta, meaning that there isn't possibility that she could give birth again shiyasa yace kar a zubar da cikin".
Salati kwae Mommy takeyi tareda sa kuka, Daddy yace "ba kuka bane mafita, addu'a ceh ta kamace mu yanzu"cikin muryar kuka Mommy tace "that mean gaskiya Alaramma ya fad'a ranan? But I can't believe that she could stoop so low and can u imagine she didn't seem to be worried at all".
Daddy dai bece mata komai ba sae duniyar tunanin daya tsunduma,bbu me walwala a cikinsu har gari yyi haske.
Mommy na jingine da jikin gadonta tunda tayi sallah bata tashi daga wajen ba, Hadiza tayi sallama kafin ta shigo bayan Mommy ta answer mata.Ta gaida Mommy tareda fad'in "haj na gama abincin na shirya komai", Mommy tace "toh jeki ina fitowa".
Har Hadiza ta tashi zata fita sae Mommy tayi saurin kiran sunanta, Hadiza ta answer tareda dawowa kusa, Mommy ta tambayeta kan ta kira Suhana neh, Hadiza tace bata kirata ba dama yanzu take shirin kiran nata.Mommy tace "ki barta inna tashi zanje in mata magana dan batajin dad'i zaiyi wuya ma in zata ci",cikeda tausayi Hadiza tace "Allah sarki, Allah yah bata lfya", Mommy dae Ameen kwae tace tareda juyawa. Ita kuma Hadiza ta fice daga d'akin.
★★★
Tana cikin bacci wayanta ta fara ringing, da qyar ta iya tashi ta d'auka, cikin murya irinta bacci tace "hello", yah answer sannan suka cigaba da magana.Hiranta tayi ta sha kamar bbu abunda ya faru,sae can tace mishi "kasan meke faruwa kuwa?", yace "saekin fad'a", anan neh ta sanar dashi cewa tanada ciki.Ga mamakinta sae taji ya kashe wayar,ai kuwa nan da nan ta fara trying numbern shi, bayan ya d'aga sae ya ce mata airtime nashi neh yyi running down shiyasa taji yyi disconnecting.Tace mishi "it's alright, muna kan magana".
Yace "yeah, ina jinki, how did u let it happened?", cikeda jin mamakinshi tace "kaman yah fa? ", yace "eh mana, ain't u not consuming the pills I've been giving u?"tace "I did mana,why are u so tensed neh?", yace "it's nothing, but akwae matsala kin san!".
Suhana ta tambaye shi "matsalar me kenan?", yace "na abunda kke d'auke dashi,I don't even believe it",tace "are u for real Sadeeq?", "what else should I say, I'm lost wallahi, amma an tambayeki na waye cikin?".
Tace "aa, amma ana dab da hakan ai", yace "toh don't mention me pls, kisan yadda zakiyi amma dan Allah kar ki bada any detail a kaina kin gane?", Suhana ta zamo confused "but why? I mean what are u saying?".
Nan Sadeeq ya shiga lallaminta yana tsarata akan duk yadda zaa yi karta bada details akanshi dan yasan hakan yana iya sawa ya rasa aikinshi, tunda take neme nemenshi be tab'a had'uwa da wacce ta tona asirinshi ba dan haka he can't let Suhana did that.
HAMAGEE
💦 💦💦💦 💦
*LAIFIN WAYE??*
💦💦💦 💦💦💦
_Written by the Aplomb writer: *Hamagee*_
*In devotion to Maman Saif*
💦
Wattpad@ Hama_gee
Page 30 💦💦
*Fahyim*
Bayan fitarsu daga gidansu Aasim kai tsaye gidansu Fahyim d'in suka nufa,a cewar Aasim zasu je su sake bama Ammee haquri tareda fahimtar da ita kan lamarin.Sunci sa'ar samunta dan har lokacin bata bar gida ba although ranan Monday neh.
Koda suka isa gidan a palour suka sameta tana latsa waya,sukayi sallama ta answer sannan suka shiga.Aasim neh ya gaisheta ta answer tareda tambayarshi ya mamansu, yace mata lfyanta qlou, tace "toh madalla".
Bayan sun d'anyi shiru na y'an seconds sae Aasim yyi gyaran murya kafin yace "uhmm Ammee dama munzo neh dan mu qara bada haquri kan abunda yah faru, kumaa... ",Ammee bata bari ya qarasa ba ta katse shi da fad'in "aa Aasim,kace abokinka neh ya tiso a gaba dan kuzo kuyi mun dad'in baki koh?", Aasim ya dubi Fahyim, shima Fahyim d'in shi yake kallo.
Yace ma Ammee "aa wllhi Ammee,ba had'in baki bane,ganinshi da nayi cikin damuwa shi ya sanya na tambaye shi meke damunshi, shiyasa nace ya kamata muzo mu baki haquri dan Allah kiyi haquri Ammee wllhi shima ba a son shi zae rabuda ita". Ammee dae bata ce ta haqura ba kuma bata ce bata haqura ba, instead saeta ceh "Allah yah kyauta".
★★★
Sun fita kenan zasu bar gidan sae Abida ta fito, time d'in lectures zata dan harma tayi late.Koda ta iso su gaida Aasim tayi kafin ta jiya tayi ma Fahyim magana "yaya can you take me to school pls, nayi latti wllh!". Kafin Fahyim yah gama deciding harya furta abunda ke ranshi har Aasim yah answer "why not Baby"(shima Baby yake kiranta saboda yadda Fahyim ma ke kiranta kenan).
Fahyim dae bece komi ba illa nuna mata motar da yyi alamar ta shiga su kaita.Tayi murmushi tareda godiya kafin ta shiga motar, seat d'in baya ta shiga Aasim kuma shike driving, sae Fahyim a gefenshi.
Suna cikin tafiya wayar Aasim ta soma ringing, shi kuma a tsarinshi bbu answer call while driving so sae yah share be kula ba. Jin an sake kira ya sa ya baima Fahyim kan yah answer, ba tareda musu ba kuwa Fahyim ya d'aga bema kalla sunan dake jiki ba dan gaba d'aya he's lost.
"Hello, where r u bro?", Fa'iza ceh tayi maganar cikin shagwab'a kamar yadda ta saba yinta. Bata jira taji reply ba ta sake fad'in "ba barni inata jira while kai kace na jira zaka zo ka kaini koh?".
Sae a sannan Fahyim yace "toh sarkin sakalci yayan naki yana driving amma yanzu zamu zo muyi picking naki", wani sanyi Fa'iza taji dan a rayuwarta tana matuqar son jin muryar Fahyim duk da tsoronsa take amma a ranta tasan cewa tana mugun sonshi da son jin muryarshi, kuma already Aasim ya san tana sonshi saedae koda wasa be tab'a nuna mata ya sani ba, shima kuma be tab'a nuna mishi hakan ba.
Aasim dake gefe yana driving yah kalleshi ta gefen ido dan yasan da wacce yake maganar, kad'a kai kwae yyi ya cigaba da driving d'inshi.Bayan sun gama wayar sae Fahyim ke tambayar shi "dama kunyi akan zaka kaita school neh?", ba tareda Aasim yah juyo ko yyi magana ba ya d'aga kai alamar eh kwae.
"Lallae, shine da zamu je gallafirin mu koh dan nima yau bbu aikin da zanje because bbu abunda zanyi". Aasim yace "ka bari kwae, wllh na gama mantawa neh", Abida dake bayan motar tace "lallae, yau Fa'iza ma tayi latti kenan", Aasim ya answer "ae yau duk taku sae kunsha bulala gun uncle", gaba d'ayansu sukayi dariya. Haka suka cigaba da tafiya har suka iso gidansu Aasim d'in, Abida ta sauqa dan kiran Fa'izan daganan dama tana son gaida mamansu..
HAMAGEE
💦 💦💦💦 💦
*LAIFIN WAYE??*
💦💦💦 💦💦💦
_Written by the Aplomb writer: *Hamagee*_
*In devotion to Maman Saif*
💦
Wattpad@ Hama_gee
Page 31 💦💦
Abida na shiga saeta tararda Fa'iza a harabar gidan tana jiran isowarsu, waya ceh a hannunta tana latsalawa.Ganin Abida yasa ta tashi cikin murya, "qawa! Kice munyi biyu", Abida tace "ki bari kwae ban san yadda akayi nayi latti ba yau wllh, yanzu kanma bio ya jima da shiga".
Fa'iza tace "hmm ki bari kwae, dama tare kuke?", Abida tace "eh", Fa'iza tace "wllh tun d'azu nake jiran yaya yazo yah kaini amma shiru kuma shiya ceh na jirashi", Abida tayi murmushi kawae ba tareda tace komai ba.
Fa'iza tace "toh mu shiga koh gaida Mama saeki yi kafin mu wuce koh", Abida tace "gaskiya kam, amma mu hanzarta dan saeda suka mun warning cewa muyi sauri sunada gun zuwa", Fa'iza taja hannunta suka shiga suna hira suna dariya.
Bayan sun shiga kai tsaye d'akin maman suka shiga, Abida ta gaisheta ta answer tareda tambayar Ammee, Abida tace lafiyanta klou. Saeda sukayi mata sallama kafin suka fice,da sauri-sauri suka fita dan kar su tsaida yayun nasu dake jiransu.
Suna fitowa suka nufi motar suka bud'e kowa ta shiga sannan Aasim ya ja suka tafi, bayan sun sauqe su sae suka wuce damuwarsu suma.
★★★
*Suhana*
Koda su Mommy suka tambayeta wanda yyi mata cikin, bata fad'a musu ba kwae dae tace musu wani saurayinta neh,ta fad'i sunanshi amma bata sanar musu cewa lecturern su bane. Abun ban haushi kuma a cikin iyayen bbu wanda ya tsawatar mata as if ma batayi wani laifi, instead ma sae lallab'ata da suke.Daddy neh ya d'auki numbern Sadeeq a wayarta tana bacci dan already ta maida sunan da tayi mishi saving da 'Sadeeq' d'inshi.
Koda Daddy yah kira bai wani sha wahala ba Sadeeq yah answer wayan da "hello", Daddy yace "hope ina magana da Sadeeq?", saeda Sadeeq yah d'anyi shiru for some seconds kafin ya answer Daddy "eh, shine lafiya?", Daddy yace "Allah yasa, dan nima ban san koh lafiyar bace tukun, ba tareda b'ata lokaci miye alaqarka da y'ata Suhana?".
Dammmm, qirjin Sadeeq yah buga, yama rasa me zaice
,sae kuma ya d'an daure yace "ban gane ba,I mean I don't know who u r referring to", Daddy yah dubi Mommy dake sauraren yadda suke maganar dan a handsfree yasa wayar, kafin yace "don't pretend,nine mahaifin Suhana wacce kayi wa ciki kuma nasan kanada masaniya akan hakan saboda haka kazo gidana ina son yin magana da kai, in kuma ka qi wallahi hukuma ceh zata raba mu", Daddy na kaiwa nan yayi hanging call d'in, Mommy ta dube shi kafin tace "da baka kashe ba ai, daka jira kaji feedback nashi, maybe ma yaqi zuwa"Daddy yace "then we shall see,in yaqi zuwa nasan matakin da zan d'auka akan shi, kuma daga yau zuwa gobe na bashi in bai zo ba ni nasan sauran".A daddafe ranan sukayi bacci.
Washegari throughout su Mommy basu fita ba,Suhana kuwa tana d'aki tun randa abun yah faru basu barinta ta fita.
Qarfe 5 daedae na yamma suna zaune a palour me gadi yyi sallama yace ana magana da Daddy,Daddy yace yah bashi gun zama yana zuwa.Gudun kar Suhana taji zuwan Sadeeq yasa Daddy sauqan a waje, yah je yah sameshi,Sadeeq kamar mutumin kirki yah gaida Daddy, ba tareda yah wani answer mishi ba ya fara magana "kamar yadda jiya na fara tambayarka, miye had'inka da y'ata?", Sadeeq yace "ina nemanta amma banida masaniya kan abunda ka fad'i jiya, ta yiwu dae wani Sadeeq d'inne ba niba".
HAMAGEE
💦 💦💦💦 💦
*LAIFIN WAYE??*
💦💦💦 💦💦💦
_Written by the Aplomb writer: *Hamagee*_
*In devotion to Maman Saif*
💦
Wattpad @ Hama_gee
Page 32 💦💦
Daddy yace "what do you mean? I'm quite sure u r the same, so don't u try to fool urself", bud'an bakin Sadeeq yace "anyway, I don't have to convince u because u never see ur daughter's fault.Sannan ni a ganina wannan abunda ya samu y'ar taka ba wani abunda zai d'aga maka hankali bane tunda dama ka rigada ka b'atata,so komai tayi daedae neh".
Ba kad'an ba maganganun Sadeeq sun b'ata ran Daddy sosae,yama rasa ta inda zae fara because quite sure yasan cewa yanada babban *LAIFI* wajen faruwar wannan al'amarin.Gyaran murya yyi kafin yace "look young man,ba dan muyi arguing da kai na nemeka ba is to solve this problem,all I need is ur cooperation,abunda nake son fad'i a nan kuma shine,a d'aura muku aure kaida Suhana inyaso ta haihu a gidanka, I think that's the best solution for both of u.
Abun mamaki Sadeeq ya dubi Daddy yace shi ba zae iya auren mace kamar Suhana ba saboda ko kad'an batada tarbiyya,yana gama zubawa Daddy rashin kunya yah tashi ba tareda neman izini ba ya bar gidan.Daddy yah rasa yadda zaiyi, saedae ya yanke shawarar zae nemi iyayenshi inta kama ma saeya shigo da hukuma cikin maganar tunda Sadeeq yaqi suyi komai cikin mutunci.
Tashi yyi ya koma cikin gidan,nan ya sanarda Mommy abunda ake ciki da kuma irin hukuncin daya yanke.
★★★
Da yamma,Suhana na bacci kamar yadda ta saba,dan yanzu kullum cikin baccin take bbu dare ba rana.Qarar ringing na wayarta neh ya tasheta dan ta manta bata saka wayar a silent ba tayi bacci,da qyar ta iya tashi ta d'au wayar ta duba me kiranta,ga mamakinta sae taga 'Suby' akan screen d'in wayar dan sun d'an kwana biyu basuyi magana ba.
"Hello, Suby". Suby ta answer daga wajenta, bayan sun gaisa neh Subyn ke tambayarta lfya tajita shiru kwana biyu,nan Suhana ta fayyace mata komai harda yadda iyayenta suka matsa akan ta basu details akan Sadeeq dan neman iyayenshi koh wajen aikin shi amma firr taqi.
"Dirqashi!!", inji Suby kafin tace "da aiki gaskiya, toh idan sun sameshi me zasuyi mishi? Kuma ma inba suba menene dan kinyi ciki, bafa akanki aka fara ba kuma ba a kanki zaa qare ba", Suhana tace "oyoo, nima dae haka na gani,ai naqi basu wani details", Suby tace "su barki kwae kiyi rayuwarki,kin gannin nan wllh na zubarda ciki yafi a qirga amma meya canzani? Koh a yau kuma naga daman yin aure zanyi, dan na lura damuwar mutane kenan wae mutum ba zae auru ba.Shiyasa na bar zaman gidanmu nazo nan karatu in gaya miki,dan in kina gida bakida saqat wllh", Suhana ta d'an nisa kafin tace "ki barni kwae Suby, ni wllhi na fara gajiya da rayuwar gidannan, in dae naga zaa takurani da yawa to barin gidan zanyi, danma baa mun wani takuri gaskiya".
Suby tace "abunyi yanzu kwae ki san yadda zakiyi a zubar da shegen dan inya girma zae zame miki matsala,gwara na fad'a miki", Suhana tace "gaskiyarki, amma Daddy yace a zubar Dr.Raheem yace ba haka ba, wae there's a problem", Suby ta riqe hab'a tareda fad'in "shishshigiii", Suhana tace "keh ki gane mun hanya".
Suby tace "karki damu zamu samo mafita,gobe kice zaki zo scul duba result d'inki inya so sae mu samu Mal.Sadeeq d'in ayi arranging yadda zaa zubar miki dashi", Suhana tace "it's ok, I'll try to meet u insha Allah".
Suby tace "I almost forgot,kinga result kuwa?", Suhana tace "ina na gani,nace miki na jima ban fita ba", Suby ta d'anyi shiru kafin tace "gaskiya result baiyi kyau ba,wancen carry-overs d'inda na gyarannan sun sake dawo mun, naki kanma baa magana dan kora neh".
Suhana ta zaro ido kamar tana kallon Suby tareda fad'in "withdrawal?", Suby tace "iyi, kinga bakiyi exams koh d'aya ba kuma testes d'inma baki wani yi ba", Suhana tace "amma ai Sadeeq yyi mun alqawarin zae kula da wannan, that he'll not let me down, ashe haka yake?", Suby tace "ki kwantar da hankalinki goben in mun had'u duk zamu san yadda zaa yi,ni dan kar inzo gidannaku ne ayi suspecting wani abun amma dana zo".
Suhana tace "karki damu, u really care for me tnks", Suby tace "u don't have to tnk me ae mun zamo d'aya", Suhana tace "haka neh, we shall see to it tomorrow bye", Suby ma tace "bye" sannan tayi hanging call d'in.
Nima kuma nan nake ce muku sae Allah ya kaimu gobe ma ji yadda Suhana zata qare da iyayenta,ko zasu yadda ta fitan koh yaya?.... Am sorry for the late post pls,wllh I'm busy these days that's y, love u all😘
HAMAGEE
Hi am Isha here from mumbai , 23 year old staying bangalore we provide body to body massage services in bangalore , iam so friendly please click my blog and see myvideos
ReplyDeletemassage bangalore
massage in bangalore
body massage bangalore
body massage in bangalore
body to body massage in bangalore
body to body massage bangalore
massage parlour bangalore
massage parlour in bangalore
body massage parlour in bangalore
body massage centers in bangalore
body to body massage bangalore
body to body massage in bangalore
erotic body massage bangalore
female body massage bangalore
full body massage bangalore
female massage in bangalore
girls body massage in bangalore
b to b massage in bangalore
b to b massage bangalore
Allah ya kara basira HAUSA EBOOKS
ReplyDelete