This site offers you with different novels series from one writer, I hope this will educate and as well as entertain you..

LAIFIN WAYE? (Page 70)

💦 💦💦💦 💦
*LAIFIN WAYE??*
💦💦💦 💦💦💦

_Written by the Aplomb writer: *Hamagee*_

*In devotion to Maman Saif*
💦

Wattpad @ Hama_gee

Page 70 💦💦

Suna cikin hakan tace mishi zata shiga gida tana jin bacci,baiyi qoqarin hanata ba saima ce mata da yayi "it's ok my wife,have a lovely night",ba tareda tace wani abu ba ta wuce ta shiga gida abinta. Shi kuma cikin mota ya koma sannan ya tayar ya tafi gida kai tsaye,harya isa tunanin Suhana da irin maganganun da tayi mishi yake yi,saidai yasha alwashin wannan bazai sa shi ya rage sonda yake yi mata ba ko kad'an,itama kuwa yana addu'ar samun so daga gareta.


Ba qaramin rud'ani Suhana ta shiga ba kan lamarin Fadeel,gashi Baffa baida masaniya akan cewa she's HIV positive,shikenan ita kam asirin ta na neman tonuwa. Taso sanarda Baffa kan lamarin sau da dama dan ya dakatar da Fadeel daga neman ta karma abin yayi nisa amma ta kasa,ta rasa ta yadda zata b'ullo wa lamarin. Shima kan shi Fadeel d'in taso sanar dashi amma ta kasa,ta rasa yadda zata yi dai a yanzu,saidai a kullum addu'ar ta itace Allah ya kawo mata mafita cikin gaggawa.


Ana cikin haka har saura watanni biyu ayi auren su Suhana,gabad'aya fanni biyun sai shirye-shirye sukeyi. Saidai har yau Suhana bata yadda da cewa zata aure Fadeel ba,hasalima harta fito ta fad'a ma Baffa cewa bazata iya auren shi ba duk da bata iya sanar dashi dalilinta ba. Zaginta yayi tareda qara tabbatar mata da cewa ko taqi kota so saita aure shi in kuma ba haka ba to zai had'a ta da son ranshi kuma hakan ba zaiyi mata dad'i ba.



Gabad'aya Suhana ta rame ta rasa yadda zatayi da wannan maganar,kullum cikin tunanin ta inda zata b'ullo wa lamarin takeyi,saidai a koda yaushe tayi qoqarin samo mafita sai taga abin bai yiwu ba. Ana cikin haka watarana iyayen Fadeel suka matsa akan suje asibiti ayi test tunda biki ya kusa kada azo ayi wani abun d'an dana sani. Babu yadda Fadeel baiyi dasu ba kan su bari shi yasan babu wata matsala dan ya yadda da ita,kuma koma akwai shi baya son sani.


Amma ina iyayen shi suka qi da hakan,qarshe dai a dolen shi ya yarda suje ayi test d'in. Iyayen sun san zai iya baije ba yace musu yaje,hakan yasa aka had'a shi da babba,tare suka je gidansu Suhanan ma. Bayan sun nemi izinin Baffa ya amince sai suka tafi. Tunda Suhana taji hakan tasan cewa duk wata alaqar dake tsakanin su tazo qarshe dan babu makawa tasan in dai suka ji wannan magana to fasawa za suyi. Ta wani wajen taji dad'in hakan,ta wani wurin kuwa bata ji ba saboda tasan dole asirinta ya tonu a cikin 'yanuwanta,amma taji dad'i daya kasance Fadeel zai kub'uta daga wannan ciwon.


Suna isa asibitin ba tareda b'ata lokaci ba aka fara yin test d'in,bayan wani d'an lokaci kuwa result ya kammalu. Koda zo miqa ma Fadeel result d'in,yayan shi bai bari an bashi ba ya karb'a. Nan ya shiga karantawa kuwa,ganin bai fahimci abinda ke cikin dakardar ba yasa ya je gurin likitan daya rubuta musu test d'in tun farko ya bashi papern.


Bayan ya karb'a saiya shiga dubawa kafin daga qarshe ya rubuta musu result d'in in detail ya bashi a hannun shi,bayan nan yace mishi "akwai matsala a auren nan da ake shirin yi because macen tana da HIV". Godiya yayi mishi kafin ya fita,kallo d'aya yayi musu kafin ya wuce yayi tafiyar shi ya barsu a wajen suna tsaye.


www.hghausanovelseries.blogspot.com

Share:

No comments:

Post a Comment

Popular Posts

Translate

Archive

featured post

UNIVERSITY GIRL Final episode(Chapter thirty)

Powered by Blogger.

Contact Form

Name

Email *

Message *

Blog Archive