💦 💦💦💦 💦
*LAIFIN WAYE??*
💦💦💦 💦💦💦
_Written by the Aplomb writer: *Hamagee*_
*In devotion to Maman Saif*
💦
Wattpad @ Hama_gee
Page 39 💦💦
Tare da Khadija suka fito har palourn,inda tayi introducing mata iyayenta suma tayi musu introducing Khadijan. Zama sukayi gaba d'ayansu bayan an gaisa suka soma hira.
*Abin mamaki wai har su Mommy sun yarda da batun Suhana abinka da lalatattun iyaye in ba haka ba ai yaci suyi bincike su tabbatar da abinda ta fad'a gaskiya ceh sannan koda sun gano gaskiyar ceh bai kamata ace sun barta wai tana zama gidan qawa ba tunda makaranta aka kawota ba qawance,sannan basu damu da jin dalilin daya hanata sanar dasu ba kafin ta tare da qawar.Allah ya kyauta*
Hankalin su kwance suka cigaba da hira kamar wasu sa'o'in juna. Can dai suka ce bari su je su nemi masauqi,Khadija ceh tace "why not stay here,I think it will be good". Daddy yace mata "no,don't worry we'll look for a place thank you",murmushi tayi mishi.
Suhana kuwa haushin Khadija taji sai dai kuma da taji response d'in Daddy sai taji dad'i dan bata qaunar a samu wata matsalar. Raka su sukayi bayan Mommy ta bata tsaraban da suka zo mata dasu itakuma tayi godiya. Har wani makeken hotel Minal ta kaisu kafinnan ta juyo da dawo wajen su Suhana itama.
Bata ji dad'in yadda Suhana tayi wasa da hankalin iyayenta ba shiyasa ta dawo akan tayi mata magana kuma ta sanar da ita cewa ba a son ranta ta bada gudumawa ba wajen raina wa iyaye hankali dan duk da barikancin Minal tasan darajan iyayen ta dama na wasu dan ta taso taga ana yin hakan a gidansu.
Tana isa ta cire gyalenta tareda ajiye jakarta da keyn mota sannan ta shiga har d'akin ta samu Suhana kwance tana latsa waya,sai famar smiling takeyi ita kad'ai. Daga gani hira takeyi wacce tayi mata dad'i sosai. Minal ta tab'e baki dan ganin halinda Suhana me ciki dan ta tabbatar ko jin shigowarta bata yi ba.
Sai da ta qarasa har inda take ta d'an make ta kafin nan Suhana ta d'ago Kant's tareda fad'in "haba,ai saiki tsorata ni kamar wata ghost". Minal tace "gaki da shegen tsoro kuma ba,wai ma wa kika samune like da wannan smiling haka? Dan dai nasan bada Farhan (sunan saurayinda take gidan shi kenan) kike chatting ba".
Wata 'yar dariya Suhana tayi kafin tace "kamar kin sani qawata,wannan yaci uban Farhan a kyau da kud'i ai. Yaushe ma zan zauna da namiji guda tak ni ba aure nayi ba,shiyasa ma bana son yin aure nikam" ta wani tab'e bakinta. Ita dai Minal taga wacce ta fi ta iskanci yau dan ita bata tab'a tunanin cin amanar saurayinta ba duk da suma d'in ba soyayyar mutunci sukeyi ba tunda tare suke zama,suke kwana kuma su biyu.
Minal dai tace "take it easy girl. Bama wannan ba tukun na,ko kin matsayin abinda kikayi wasu Mommy yau? Kin san da cewa kin raina musu hanali da wayo? Iyayenki ne fa komai zakiyi bai kamata su ki wulaqanta su ba". Suhana tace "me nayi na wulaqanci anan? Ke yanzu idan iyayenki neh a matsayin nawa,yadda suka zo miki a hakan nan kina nufin bazayi yadda nayi ba?".
Minal tace "ba wai b'oye musu da kikayi bane nufina,abinda ya kamata shine ki b'ulla musu ta wata hanya ba ta wannan ba,kinga yanzu sun zaci gidan friend d'inki ne har ga Allah alhali gidan saurayin kine. Da ta wata hanyar aka b'ulla musu". Suhana tace "koma miye dai qaryar za ayi musu so let it be".
Minal tace "anyhow,yanzu waye kika samu da yake neman yi mana qwace kin san a partyn Farhan nake",Suhana tace "kyayi ai,kina cikin wahala kuwa". Dariya sukayi gaba d'ayan su.
www.hghausanovelseries.blogspot.com
No comments:
Post a Comment