This site offers you with different novels series from one writer, I hope this will educate and as well as entertain you..

LAIFIN WAYE? (Page 49)

💦 💦💦💦 💦
*LAIFIN WAYE??*
💦💦💦 💦💦💦

_Written by the Aplomb writer: *Hamagee*_

*In devotion to Maman Saif*
💦

Wattpad @ Hama_gee

Page 49 💦💦

    Mommy tace "ina tafe dasu indai wa'yin nan neh babu matsala". Nan ta bud'e jakarta ta ciro dubu ashirin ta ajiye su a gaban shi. Dariya yayi kafin yace "an gama,buqatar ki ta biya amma baki gama ba. Sai kin kawo mana idon saniya da qashin dake tsakiyan haqarqarin zomo,sai kuma duk wani abu nashi ko kuma wanda aka san ya tab'a tab'awa koma miye shi saboda ganinshi yayi mana sauqi".

    Mommy tace "wai! A ina zan samo su kenan?",yace "dabara ta rage ga mai kayan kara,kamar idon saniya da haqarqarin zomo ki barni dashi kud'i kawai zaki qaro min,ni nasan yadda zan samu". Mommy tace "to babu damuwa,yanzun nan zan baka kud'in shi kuma abinda ya tab'a tab'awan zan nemo shi bani daga yau zuwa gobe in ya jima kenan". Yace "to babu damuwa".



    Jakarta ta bud'e ta ciro dubu goman da yake ciki sannan ta miqa mishi kafin ta tashi ta tafi. Komawa gida tayi tana tunanin inda zata samo abinda Farhan ya tab'a tab'ashi. Tayi tayi ta tuno wani abin amma ina ta kasa,sai can tana zaune ta tuno da wani abin,tashi tayi da sauri kamar an mintsine ta.

★★★
   Suhana na kwance amma abin duniya duk sun ishe ta,ga abinda ya faru tsakanin ta da Farhan,ga kuma halinda iyayen ta ke ciki a yanzu. Ta rasa wanne zatayi ma jimami. Can Suby kala ta fad'o mata a rai,ai kuwa babu shiri ta kira ta. Ringing na farko ta amsa.


    "Amarsu ta ango,wato duniya tayi miki dad'i kin mance da wata aminiyar ki Suby koh?". Suhana tayi tsaki "mtsww" sannan tace "ke dai bari da alla,inda kin san halinda nake ciki yanzu da duk wa'yannan kalaman naki kin adana ma kanki su". A zabure kamar an mintsina Suby tace "me kike nufi? Wani abin neh kuma ya faru?".



    Suhana tace "wani abun ko wasu abubuwan?". Suby ta gyara zama kafin tace "fad'a min,me ke faruwa ai ban san aminiyata na cikin damuwa ba da tuni an san yadda za ayi a magance miki ita". Suhana tace "kinga daga farko gidan mu sun koma abin tausayi,dan a halinda ake ciki Daddy na kwance rai a hannun Allah,daga farko an kasa gano matsalar da yake da ita amma daga baya an gano yana da cancer wacce ta cinye mai kidney gaba d'aya".


   Shiru ta d'anyi kafin ta cigaba "yanzu dai sun samu an canza kidney d'in sai dai kin san blood cancer, a gyaro can ne nan kuma ya b'aci,ga shi yanzu duk dukiyar shi ta tafi a jinyar Mommy kuma kin san bata aiki,kuma samu aiki da wuya a yanzu. Yanzu haka maganar da mukeyi sun canza gida kuma abinci ma neman gagarar su yakeyi",tana kaiwa nan ta fashe da kuka.

    Nan dai Suby ta shiga bata haquri,da qyar ta samu tayi shirun kafin tace "bama wannan kad'ai yake damuna ba,yanzu ace Farhan ya guje ni ko gidan ma ya bar kwana cikin sa". Cikin rashin fahimta Suby ta tambaya "kamar ya fa?". Take Suhana ta koro mata duk abubuwan da suka faru.


    Suby tace "to kina ganin da gaske shi d'inne ya saka miki cutar?",Suhana tace "inba shi ba to ni zan saka mishi?". Suby tace "abun neh da d'aure kai amma",kamar anyi wa Suhana wahayin wani abun tace "tsaya Suby,na tuna wani abun bari I'll call you in some minutes". Suby tace "it's ok sai kin kira". Hanging call d'in Suhana tayi sannan ta miqe tsaye tana wasu calculations..


    www.hghausanovelseries.blogspot.com

Share:

No comments:

Post a Comment

Popular Posts

Translate

Archive

featured post

UNIVERSITY GIRL Final episode(Chapter thirty)

Powered by Blogger.

Contact Form

Name

Email *

Message *

Blog Archive