This site offers you with different novels series from one writer, I hope this will educate and as well as entertain you..

LAIFIN WAYE? (Page 73)

💦 💦💦💦 💦
*LAIFIN WAYE??*
💦💦💦 💦💦💦

_Written by the Aplomb writer: *Hamagee*_

*Wannan page d'in naku neh masoya wannan littafi,ina godiya da yadda kuke bin littafin,ILY'LL*
💦

Wattpad @ Hama_gee

Page 73 💦💦

    Kowaccen su taji dad'in sannan rana da ta kasance ta aurensu amma banda Suhana,kasancewar ba wani sabon abu bane a wajenta kuma ma wanda ta auran ba sonshi takeyi ba,kawai dai biyayya tayi. Shi kuwa yana sonta har ranshi dan haka nema yake lallashinta. Washegari yayi introducing d'inta wa yaranshi gabad'ayan su kuma daga dukkanin alama bazata samu matsala daga garesu ba. Itama kuma tayi niyyar zama dasu tsakanin ta da Allah,babu ha'inci ko wani muzgunawa,shi kuma tasa ma ranta zatayi mishi biyayya irinta aure. Haka rayuwar Suhana ta cigaba kamar ba ita ba,iyayenta kuwa kullum cikin addu'a take yi musu.

★★★
Ko kun manta dasu Fahyim da Aasim da kuma matansu sannan qannensu? Ya kamata mu leqa su suma dan ganin yadda rayuwarsu ta kasance.

    Rayuwa mai cikeda jin dad'i da farin ciki sukeyi. A halin yanzu yaransu uku-uku dan a tare suke haihuwa wani ikon Allahn. Gidansu d'aya saidai kowa da side d'insu,koda yaushe suna tare kuma dan wajen aikin matayen d'aya haka ma mazajen. Yaransu ma makarantar su d'aya abinsu,kullum suna tare abin sha'awa.


    Watarana Aasim da Fahyim sun ziyarci wani abokin su wanda ya kusa yin aure a halinda ake ciki,shima tare suka taso saidai shi tun bayan gama secondary school d'insu suka rabu kasancewar ya koma Sokoto da zama,anan ya kammala karatun degree da masters d'inshi.


    Bayan sun kammala hiransu zasu tafi dan yamma yayi har magariba ya gabato. Fitowarsu keda wuya saiga wata mata na magana da almajiri,daga dukkan alamu abinci ta bashi. Basu kawo komai a ransu ba sukam,har sun saka kai zasu je wajen motarsu sai juyowarta ya hanasu,wa zasu gani banda Suhana. Kansu gabad'aya ya d'aure sai kallonta sukeyi. Abokin neh yace "wannan kallon fa? Kun Santa neh? Matar baba ceh fa",kowannensu ya kalli d'anuwan shi kafin suka maida kallon su ga Abokin.

   Suhana ceh tayi qarfin hali ta gaidasu,cikin yaqe suka amsa kafin ta wuce,bayan wucewar tane suke yima abokin nasu bayani,shine yace ai yanzu matar babanshi ce. Cikin mamaki suka koma gida,koda suka koma kowannen su saida yayi wa matarshi tad'in Suhanan. Suma matan sun yi mamaki matuqa dan basu tab'a kawowa  cewar Suhana zata nutsu haka ba harta iya auren tsoho kamar Alhj.Suhan,hakan ma ba wai wani kud'i yake dashi ba.


    A wajen Suhana kuwa kunya ce da nadamar abinda tayi wa Fahyim suka baibayeta,har dare tana cikin wannan tunanin har Alhj yaso ya fahimci damuwarta,koda ya tambayeta ce mishi tayi kanta na ciwo shiyasa. Washegari sun fita kasuwa suka had'u dasu Fahyim,a wannan karon harda su Abida da yaransu. Nanma Suhana bata ji dad'i ba ko kad'an,yaran kuwa ba qaramin sha'awa suka bata ba gashi yanzu ba iya haihuwa zatayi ba,ita dai ta cuce kanta kawai. Koda suka had'u gaisawa sukayi dake Alhj.Suhan yasan su daman suma kuma sun sanshi sosai. Haka rayuwar Suhana ta qare,babu iyenta,babu miji had'add'e mai kud'i,kuma babu haihuwa,what a pity life for her!

   Shin LAIFIN WANENE duk wa'yannan abubuwan da suka faru? Ina jiran feedback d'inku masu karatu. Anan na kawo qarshen wannan littafi me taken suna LAIFIN WAYE?, kuma ina roqon Allah yasa mu amfana dashi,mu cigaba da zuwa a littafaina na gaba wato 'ALHAKI NEH!, da kuma DA WATA QAWAR..'.

   Ina godiya ga Allah daya kawoni qarshen wannan littafi lafiya,kuma ina miqa godiya ta ga dukkanin masoya wannan littafi,taku har kullum Hama G Muh'd aka Hamagee.


      hghausanovelseries.blogspot.com

Share:

No comments:

Post a Comment

Popular Posts

Translate

Archive

featured post

UNIVERSITY GIRL Final episode(Chapter thirty)

Powered by Blogger.

Contact Form

Name

Email *

Message *

Blog Archive