💦 💦💦💦 💦
*LAIFIN WAYE??*
💦💦💦 💦💦💦
_Written by the Aplomb writer: *Hamagee*_
*In devotion to Maman Saif*
💦
Wattpad @ Hama_gee
A last chap nace zan qarasa book d'in cikin wancen week din but abun be yiwu ba, am sorry for that.Ina neman addu'o'in ku zan fara test this week insha Allah, tnks for all the love u have for me, I love u even more....
Page 38 💦💦
From last chap,nasan readers zakuyi zaton Suhana ceh suka gani,nima I thought Itan ce daga farko amma daga baya dana ganta da kyau sai nace ashe sab'anin tunanina neh.Sunan budurwar Minal,itama daga 9ja take karatu neh ya kawota Uganda.Recently, ta had'u da Suhana a school dan a yanzu ma har sun saba sosai,a taqaice dai Suhana da ita are friends now.
Abinda yasa Minal ta tsaya kallon su Mommy saboda tasansu neh dan Suhana tasha nuna mata su a waya,sannan sau d'aya sun tab'a gaisawa saidai su bazasu ganeta ba dan ba hotonta suka gani ba balle. Gasuwa tayi musu na mutunci tareda basu wajen zama kafin ta shirya ta fito dan ta fad'a musu cewa tasan Suhana sannan tasan inda yanzu take da zama.
Su dai abin ya basu mamaki ace Suhana ta canza wajen zama amma bata sanar dasu ba. Komawan da tayi kuwa kiran Suhana ta shiga yi,nan ta sanar da ita cewa iyayenta sunzo nemanta kuma yanzu tana kawosu. Koda jin hakan bai wani dameta ba saima cewa da tayi babu damuwa sai sunzo.
Bayan sun gama wayanne ta shirya tsaf cikin doguwar riga tareda yafo gyalenta kamar mutuniyar arzik'i ta fito,harta fito sai ta tuno bata fito da key d'in motarta ba sai ta koma taje ta d'auko sa'annan tazo suka tafi. Hira tayi ta musu a hanya,nan ne ta sanar dasu cewa itace wacce suka tab'a gaisawa ,take suka tuno ta kuwa.
Suhana kuwa suna gama waya ta kira saurayinta da suke zaune tare ta sanar mishi cewa karya dawo dan iyayenta sunzo kuma at any moment zasu iso inda take. Yace babu damuwa sai sunyi waya kawai,tace toh sannan ta kashe wayar.
Tashi tayi ta gyara gidan tsaf ta tattare kayan shi wanda zai sa a gane gidan namiji ne duk ta b'oye su. Bayan ta gama saita kira wata k'awarta akan tazo su zauna samun in iyayentan suka zo saita ce musu gidan k'awar neh da Babanta ya sai mata shine tace tazo su zauna,dan makarantar su ma d'aya da yarinyar data kira d'in sai dai ita ba bahaushiya bace 'yar can ne.
Bayan ta gama shirya komai saita shiga tayi wanka tazo palour ta zauna zaman jiran isowarsu,gefenta kuma wannan frnd d'in nata ce suna d'an hirarsu. Bada jimawa ba kuwa sai akayi horn me gadi ya bud'e gate aka shigo,leqawa tayi ta window ganin iyayen nata ne yasa ta koma ta zauna suna kallo.
Wayarta ce tayi ringing sai dai bata amsa a karo na farko ba sai ana biyu tukun na ta amsa. Su Mommy basu san dawar garin ba dan a zaton su ma bata san sunzo ba akan zasuyi surprising d'inta neh. Bayan ta amsa neh Minal take tambayar ta tana gida neh,tace tana nan zata zo mata neh,tace ai tama zo amma ta d'an fito waje ta sameta.
Ba tareda wasting time ba Suhana ta tashi ta fita,ganin iyayenta yasa tayi tsalle cikin murna,da nuna suprise da taji kamar bata san da zuwan sun ba. Suma sunyi murna sosai da ganinta,nan taja su suka cikin gidan ta sauqe su a palour kafin ta koma ta d'auko musu drinks sannan ta shiga d'aki kiran qawarta Khadija.
www.hghausanovelseries.blogspot.com
No comments:
Post a Comment