🌸🦋🌸🦋🌸🦋🌸🦋🌸
*ALHAKI NEH!*
🌸🦋🌸🦋🌸🦋🌸🦋🌸🦋
® *_PURE MOMENT OF LIFE WRITERS_*
_ɯɛ ɖơŋ'ŧ ơŋٳყ ɛŋŧɛřŧąıŋ ŋɖ ɛɖųĆąŧɛ, ცųŧ ɯɛ ąٳŞơ ŧơųĆɧ ŧɧɛ ɧɛąřŧ ơʄ řɛąɖɛřŞ_
By the applomb writer: *Hamagee*
*K'UNGIYA MAI SUNA A SAMA WATO P.M.L.W SUNYI SHIGE DA FICE WAJEN KAWO MUKU HANYOYI MAFIYA SAUK'I DA ZAKUNA BI DAN SAMUN LITTAFANSU KAI TSAYE,WAY'ANNAN SHAFUKAN KUWA SUNE WANDA ZAN JERO SU A K'ASA.BUK'ATARMU KAWAI ITACE KU CIGABA DA BINMU DAN MU NAKU NE,SANNAN KADA KU MANTA A KODA YAUSHE IN KUN KARANTA KU RINK'A LIKING,COMENTING DA KUMA SHARING..SAI KUNZO....Mune dai PML Writers* 👌🏼
# WWW.PMLWRITERS@GMAIL.COM
# IG PML WRITERS
# https://www.facebook.com/PML_-Writers-FANS-459256761123035
# http://maryamsbello.blogspot.com
Wattpad @Hama_gee
16th Sept,2017
Page 03
°
Jiki a sanyaye Zuwaira ta bar wajen da d'anta,ta koma d'aki ta soma kuka d'anta nata kallonta shima d'in ya fara kukan.
Kawu Bello kuwa ranshi yayi mugun b'aci,da ace yanada ikon da zai saka Mahdi ya saki Zuwaira toda ya jima da yin hakan dan babu abinda Zuwaira ta sanya a gaba sai muzguna ma Umma,kuma Mahdi na gani amma baya cewa komai.
Saida ya nemi gu ya zauna kafin ya dubi Umma ya kirata "Yaya",ta amsa da "na'am".Yace "a gaskiya na gaji da irin wannan zaman naki a gidannan,ace ke kenan kika rage mun a duniya amma ina ji ina gani ana k'untata miki?,toh gaskiya yau kam dole zaki bar gidannan inyaso Mahdin sai ya ringa zuwa koda kuwa kullum neh kina ganinshi tunda ba zai iya rabuwa da matarshi ba".
Umma tace "ka daina wannan maganan Bello,na riga da fad'a maka cewa anan gidan zan k'arasa rayuwata,me nake nema yanzu? Babu daman zaman jiran mutuwata kawai nakeyi to meyasa zan buk'aci wani jin dad'i na duniya,ka barni kawai dan babu inda zani".
Babu yadda Kawu Bello beyi da ita ba amma firr tak'i,haka yana ji yana gani ya barta a gidan.
****
Around 2:30pm Mahdi ya shigo gidan,kai tsaye d'akin Zuwaira ya shiga kamar yadda ya saba.Samunta yayi a kwance tasha kukanta harta gaji sannan tayi bacci,ga Aminu a gefenta shima yayi baccin.
Be tasheta ba ya nufi kitchen ya d'auko abincin shi dan yunwa yake ji a lokacin.Bayan ya d'auko saiya zauna yaci ya sha ruwa kafin ya tattare kwanukan ya mayar su zauren.
D'akin Umma ya nufa ya gaida ta sannan ya dawo d'akin Zuwaira shima ya kwanta,bai jima ba bacci ya d'auke shi.
Wajen k'arfe uku da rabi Zuwaira ta tashi,juyawan da zatayi sai taga Mahdi kwance yana bacci.Tashi tayi taje tayo alwala sannan ta dawo ta tashe shi kafin ta fara sallahn.
Bayan ta idar kuwa bata tashi a inda take ba har Mahdi ya shigo gidan.Zama yayi a gefen gadon yana jiranta dan a zatonshi ko addu'a takeyi.
Ga mamakinshi saiya ga har yanzu bata ko motsa a inda ya shigo ya sameta ba,kuma yasan in dai addu'a Zuwaira zatayi to bata wuce mintuna biyu gashi yanzu ta kusan mintuna goma tana zaune.Tasowa yayi yazo inda take zaune ya tsuguna a gabanta sannan ya dubeta.
Ya bud'i baki zaiyi magana saiya ga idonta cikeda k'walla tana k'ok'arin sharewa,yace "lafiya Zuwaira kike kuka?".Bata ce mishi komai ba hasalima kanta na kallon k'asa kamar yadda yazo ya sameta.Sake tambayarta yayi "lafiya Zuwaira,meya sameki?".
Cikin kuka ta fara fad'a mishi k'arya da gaskiyarta wai Kawu Bello neh yazo har cikin gidan ya zazzageta babu abunda ta mishi,saidata gama tsara mishi k'arerayinta sannan ta fashe da kukan gaske,shi kuma an tab'o mishi shalelenshi dan haka ranshi ya b'aci.
Nan ya shiga bata hak'uri yana lallashi har tayi shiru,tareda yi mata alk'awarin hakan bazai sake faruwa ba dan ya tabbatar mata da cewa zai je ya samu Kawu Bello suyi wacce za suyi yau d'innan,har cikin ranta kuwa taji dad'i.
Bayan nan ya tashi ya nufa gidan Kawu Bello kai tsaye.
hghausanovelseries.blogspot.com
No comments:
Post a Comment