💦 💦💦💦 💦
*LAIFIN WAYE??*
💦💦💦 💦💦💦
_Written by the Aplomb writer: *Hamagee*_
*In devotion to Maman Saif*
💦
Wattpad @ Hama_gee
Page 60 💦💦
Bayan tafiyar Suhana da 'yan mintuna Farheen ta shigo d'akin akan zata cema Farhana zasu fita. Ganin babu Farhana babu yaran yasa ta tsaya tana me tunanin inda suka shiga. Ana cikin haka saiga su sun dawo,Farheen ce tayi ma Farhana kashedin kada ta sake fita ta bar Farhan shi kad'ai,kafin ta tafi kuma saida tayi mata al'qawarin anjima idan su Mamansu sun dawo zasu fita tareda ita tunda yanzun bazata fita ba,Farheen ta amsa mata cikin jin dad'in ance itama za a fita da ita.
Daga nan kuma Farheen ta juya ta fita dan already yaran har sun fita sunbi Babansu,koda tace su koma su taya auntyn su zama qi sukayi. Ganin za suyi kuka yasa tace su tafi kawai dan koda an barsu a nan d'in ma qarama Farhana wahala kawai za ayi. Farhana kuwa ganin ita kad'ai ce bai mata dad'i ba,saidai sanin dalilin zaman nata yasa bata wani d'aga hankalinta ba,itama kamar Mamansu ce Farhan tafi so a kaf cikin 'yan gidansu.
Tausayin shine ya kamata ganin ko magana baya iya yi inba jiya da jikin ya d'an yi sauqi,a ranta kuma fatan samun lafiyar shi take yi samun su koma gida dashi dan Mamansu tace idan ya samu sauqi aka sallame shi to tare zasu koma gida dan bata san irin sakacin da Suhana zata sake yi da rayuwar shi ba,gara yana kusa da ita a fad'in ta kenan.
Wajen qarfe biyu da rabi na rana Farhan ya farka,da qyar yake iya fad'in "where is my mom? Where is my sisters and my wife?",Farhana bata ji abinda yake qoqarin fad'i ba dan haka ta tashi da sauri ganin ya tashi taje kusa da shi dan jin abinda yake buqata. Tana zama ya riqe hannunta saidai baya iya cewa komai a yanzun sai kallonta kawai da yake yi. Kuka Farhana ta shiga yi tana fad'in "what's it brother? What is it that you're saying earlier, please talk again or should I call a doctor?". Farhan ya girgiza mata kai alamar a'a,a haka suka tsaya har lokacin da taji yana fad'in "la'ilaha illallahu muhammadur rasulullillah sallallahu alaihi wassallam...lailaha illah muhammadur rasulullah sallallahu alaihi wasallam...lailaha illallah Muhamm...." Bai qarasa ba taji yayi shiru,idanun shi sun kafe sannan yana kallon sama fuskar shi kuma da d'an murmushi.
Wani ihun data qwala yasa su Maman dake hanyar shigowa suka kwasa da gudu suka shigo cikin ganin,dama sun dawo suna kan hanyar su ta shigowa kenan. Da sauri Farhana ta miqe ta nufa wajen iyayen cikin kuka tana fad'in "don't tell me what I saw is true,please mom tell me that I was just dreaming and try your possible best to wake me up because I can't bear to see more of the dream".
Maman ta riqeta tareda tambayar ta "what's the matter Farhana? Try and tell me something, did anything happen to your brother? Stop crying and tell me now!". Nan Farhana ta ja hannunta zuwa kan gadon Farhan dan ta gane ma idonta koma miye because right now batada strength d'in yin magana,Baban ma qarasowa wajen yayi.
Ba qaramin tashin hankalin suka shiga ba ganin gawar d'ansu,saidai ganin yadda yake murmushi da kuma yadda suka ji yayi kalmar shahada yasa suka d'anji dad'i kad'an a ransu. Mommy tafi kowa nuna damuwar ta,bata qaunar abinda zai tab'a mata Farhan,saidai kuma tayi believing da cewa kowane mai rai saiya d'and'ana mutuwa,hakan neh yasa take d'an rarrashin kanta.
www.hghausanovelseries.blogspot.com
No comments:
Post a Comment