This site offers you with different novels series from one writer, I hope this will educate and as well as entertain you..

ALHAKI NEH! (Page 1)

🦋🌸🦋🌸🦋🌸🦋🌸🦋🌸

*ALHAKI NEH!*

🌸🦋🌸🦋🌸🦋🌸🦋🌸🦋

® *_PURE MOMENT OF LIFE WRITERS_*

_ɯɛ ɖơŋ'ŧ ơŋٳყ ɛŋŧɛřŧąıŋ ŋɖ ɛɖųĆąŧɛ, ცųŧ ɯɛ ąٳŞơ ŧơųĆɧ ŧɧɛ ɧɛąřŧ ơʄ řɛąɖɛřŞ_

By the applomb writer: *Hamagee*

Wattpad @Hama_gee

Page 01

°
Da k'arfi ta bankad'o k'yauren d'akin umma tsohuwa tana banbami "wannan ai iskanci neh,ance miki tsufa hauka neh da zan sa miki abinci ki cakud'a ki barmun? Waye zaici sauran ki?".

Ummaa tsohuwa dake kwance ta mik'e zaune da k'yar tana fad'in "haba zuwaira kiyi hak'uri mana,wannan ai be kai abun ki tada hankalinki ba,ba'a cikin kwanon naci ba d'iba nayi,kuma abunda yasa kika ga ban cinye ba bana jin dad'i neh shiyasa!!"

Zuwaira tace "dalla rufan baki tsohuwar banza,mara imani mara tausayi dan bake kike cefanen ba shiyasa zakice haka ai,ance miki koh d'annaki da yake sayowa zan yarda yana mun irin wannan neh?"

Umma tsohuwa dai hak'uri tayi ta bata kun san ance fad'an daya fi k'arfinka sai ka zuba mishi ido kawai.
Tsaki Zuwaira tayi tareda fad'in "tsohuwar k'azama!".

Tayi ficewarta daga d'akin inda tabar Ummaa tsohuwa tanata faman neman gurin kwanciya dan ita koh kad'an abun be dameta ba dan idan ana sabo da wulak'anci toh ita kam ta riga da ta saba dashi.

Dan wannan kad'an neh daga aikin Zuwaira.Kullum haka suke da surkuwar tata,tsangwama,kyara,masifa da rashin ganin girma.

Zuwaira nah barin d'akin ta koma d'akinta inda ta tararda Aminu zaune cikin kashi,sai faman wasa dashi yake yi.

Wani tsaki ta jaa kafin ta k'arasa inda yake zaune ta d'aga shi daga cikin kashin sannan ta wanke mishi jiki ta gyara wajen.

Bayannan ta sa mishi wando tareda d'ora shi kan cinyarta ta soma bashi kunun data dama mishi shi kuma yana sha.

Sallamar meh gidan neh yasa ta d'ago kanta tareda ansawa,Mal.Mahdi yah k'araso tareda fad'in "sannu da gida!",tace "yauwa sannu".

Harya nemi guri zai zauna sai kuma yah tashi,d'akin Umma tsohuwa yah nufa inda yah sameta kwance kamar tana bacci,har zai juya sai yaji ta kira sunanshi "Mahdi!".

"Naam",yah amsa tareda juyowa yah shiga d'an bukkarta.Bayan yah shiga saiya nemi guri yah zauna kafin yace "yah jikin?"

Tace "da sauk'i"yace "toh madalla! Daman jikin nazo dubawa barinje inci abinci".

Umma tsohuwa tace "toh babu laifi",yah tashi yah fita yana toshe hancin shi.

Yana fitowa yazo yah tambayi Zuwaira ina abincin shi,tace dashi ya duba zaure.Zauren yah nufa yah d'auko abincin shi yazo yana ci.

Zuwaira ta dubeshi kafin tace "Mahdi nifa na fara gajiya da halin tsohuwar kah".

Loma na biyun da Mahdi bai kai ba kenan,yace "lafiya? Meya faru Zuwaira!".

Zuwaira ta fara kukan k'arya tana fad'in,"komai nayi ban fita ba? Ace ni kenan saidai ina bauta mata ita kuma tana wulak'anta nii,d'azu nah kai mata abinci,ta rasa abunda zata ceh mun sae zagi,ta uwa ta uba? Ga can abincin ma yadda na kai mata bata ciba,saita cakud'a shi ta bari,da nayi magana kuma saita fara zagina wai ai bani nake siyen abincin ba,kuma gidan d'anta neh dole kuma tayi abunda take so".

Ta share hawayen ta na k'arya kafin ta cigaba "ace baza taji tausayin ka ba duk irin wahalan da kake sha kafin ka samo mana abinda zamu ci,kamar ba ita ta haifeka ba?,nikam ban san yadda take so inyi mata,duka irin biyayyar da nake yi mata bata gani,in ta tashi zagina harda iyayenaaa".

Wani sabon kuka Zuwaira ta soma rerawa.Shi kuma Mahdi duk hankalinshi yah bi ya tashi dan inda abunda yafi tsana toh shine ya ga Zuwaira cikin damuwa.

Tashinda Mahdi yyi be nufa ko ina ba sai d'akin Umma yana huci kamar wanda zai je ya daketa,babu koh sallama ya fad'a mata cikin d'aki,ganin yanayin Mahdi yasa Umma tace "lafiya kuwa Mahdi?".

       hghausanovelseries.blogspot.com

Share:

No comments:

Post a Comment

Popular Posts

Translate

Archive

featured post

UNIVERSITY GIRL Final episode(Chapter thirty)

Powered by Blogger.

Contact Form

Name

Email *

Message *

Blog Archive